Abincin N4bn muke ciyar da dalibai —Gwamnatin Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta yi ikirarin kashe Naira biliyan hudu wajen ciyar da daliban makarantun kwana a duk shekara.
Gwamnatin Kaduna ta yi ikirarin ciyar da daliban makarantun kwana abincin Naira biliyan hudu a duk shekara.
Mai ba wa gwamnan jihar shawara ta musamman kan shirin ciyar da dalibai, Dokta Fauziya Buhari Ado, ce ta sanar da hakan a ranar Lahadi.
Dokta Fauziya ta ce dalibai 25,000 da ke makarantun kwanan gwamnati 51 da ke fadin jihar ne suke cin gajiyar abincin gwamnatin.
A cewarta, shirin ciyarwan ya kara yawan shigan dalibai makarantu tare da amfanar da manoma da ake sayen kayan abincin daga hannunsu.
“Shirin ya kuma habaka tattalin arzikin masu sana’ar abinci da masu sayar da kayan masarufi da sauransu,” a cewar Fauziya.
Ta ci gaba da cewa gwamntin jihar za ta ci gaba da tabbatar da bin ka’idojin da ta gindaya wa shirin a bangaren ingancin abinci da yawansa da kuma raba wa a kan lokaci.