Abnur Entertainament ya sa gasar ‘Manyan Mata’
Kamfanin Abnur Entertainment ya shirya wani kayataccen gasar rubuta sunayen jaruman da ake zaton za su fito a sabon fim dinsa mai suna Manyan Mata. Ita dai wannan gasar mai taken ‘#ManyanMataChallenge” za ta taimaka wajen jawo hankalin mutane game da kayataccen fim din mai dogon zango da za a fara dauka nan ba da […]
Kamfanin Abnur Entertainment ya shirya wani kayataccen gasar rubuta sunayen jaruman da ake zaton za su fito a sabon fim dinsa mai suna Manyan Mata.
Ita dai wannan gasar mai taken ‘#ManyanMataChallenge” za ta taimaka wajen jawo hankalin mutane game da kayataccen fim din mai dogon zango da za a fara dauka nan ba da jimawa ba, tare da ba mutane dama su bayyana ra’ayinsu kan jaruman da suke tunanin za su taka rawa a ciki.
Shugaban kamfanin, Abdul Amart Maikwashewa, wanda ake wa lakabi da Dujiman Kannywood ne ya sanar da gasar.
Sharudan shiga gasar su ne, a “lissafa sunan jarumai mata goma 11 na jikin posta da za mu saki, wadanda za su fito a fim din na Manyan Mata. Lissafa sunan jarumai guda biyar maza wadanda za su fito cikin fim din.
“Na uku a bayyana darakta guda nawa za su ba da umarni kuma a lissafo su. Sai a bayyana marubuta nawa ne suka rubuta fim din a lissafo su. Sannan a karshe a bayyana wane ne forudusan fim din”, inji shi.
Ka’idojin bayyana amsoshin tambayoyin su ne, “wanda zai shiga gasar zai bi shafin abnur_entertainment a shafukan sada zumunta na Instagram da Twitter da Facebook.
“Sannan mutum ya wallafa tallar gasar a shafinsa, tare da ambaton shafukan abnur-entertainment da kannywoodexclusive da kannywoodcelebrities da manyanmatachalleneg”.
Tuni aka fara aikawa da amsoshin tambayoyin gasar, wadda za a kammala a cikin mako biyu.
Su dai wadannan tambayoyin duk akwai amsoshinsu amma a boye, inda ake bukatar masu kallo su yi kokarin hararo amsoshin.
Wanda ya samu nasarar zuwa na daya zai samu kyautar karamar kwanfuta. Na biyu zai samu wayar hannu kirar Spark 4. Na uku zai samu shadda gezna. Na hudu atamfa Super Wax, sai na biyar zai samu yadi gyale.