Abokai hudu sun kashe budurwa da fyade
A ranar Asabar da ta gabata (28/12/13) ne wadansu matasa su hudu suka kashe wata budurwa ta hanyar yi mata fyade.Aminiya ta gano cewa ita dai wannan matashiya mai suna Maryam Ummi Muhammed ‘yar kimanin shekara goma sha shida wanda take zaune a bayan Albarka sinima da ke Tudun Wada Zariya, ta rasa ranta ne […]

A ranar Asabar da ta gabata (28/12/13) ne wadansu matasa su hudu suka kashe wata budurwa ta hanyar yi mata fyade.
Aminiya ta gano cewa ita dai wannan matashiya mai suna Maryam Ummi Muhammed ‘yar kimanin shekara goma sha shida wanda take zaune a bayan Albarka sinima da ke Tudun Wada Zariya, ta rasa ranta ne ta hanyar yi mata fyade da ake zargin wadansu matasa hudu sun yi mata.
Majiyarmu ta ce, Maryam Ummi ta je gidan wasan kwaikwayo ne wanda ake kira gidan Baba Cikaji da ke tashar jirgin kasa, inda suka gudanar da wasan kwaikwayo, sai su wadannan matasan suka gayyace ta domin su gana da ita, a inda aka ce sun sanya mata wani magani da ake ce wa ‘’TRAMOL’ mai karfin giram 200 guda goma suka sanya mata a cikin abin sha suka ba ta ta sha, ba tare da ta sani ba, a inda daga nan suka dauke ta suka kai ta dakin daya daga cikinsu mai suna Habu a layin Yarabawa da ke Sabon Gari Zariya.
Majiyar tamu ta sheda mana cewa, su dai wadannan matasa abokan juna ne kuma dama sun saba aikata irin wannan mummunan aikin.
Kamar yadda Aminiya ta gano daga wata majiya ta jami’an tsaro, ta ce daya daga ciki matasan mai suna Habu, wanda aka yi wa Ummi fyade a dakinsa da shi da wani mai suna Shamsu duk sun gudu ba a gansu ba. Sai dai an kama biyu daga cikinsu, Murtala Muhammad wanda yake zaune a layin Warri da ke Sabon Gari da kuma Musa Abdullahi da ke zaune a Unguwar Alkali a cikin birnin Zariya.
Aminiya ta tuntubi mahaifiyar Ummi domin jin ta bakinta inda ta bayyana cewa, “sunana Rukayya Salisu, kuma ni ce mahaifiyar Ummi, ina zaune da misalin karfe tara na safe sai ga wata daga cikin kawayen Ummi ta shigo tana kuka ta ce Ummi tana asibiti ba ta da lafiya, sai na ce wane asibiti kuma meye na kuka? sai ta ce ai ta mutu ne. To daga nan sai na ji jiri ya kwashe ni, kafin a rike ni na zauna, daga nan sai muka nufi asibitin, inda na tarar da kawayenta suna kuka.’’
Mahaifiyar Ummi ta ci gaba da cewa, “jiya da rana muna tare da ‘yata Ummi, sai ta ce mun zata ta tafi domin ta karbo dinkinta na anko, domin ranar Asabar mai zuwan nan za a a yi bikinta, iyakar rabuwa ta da ita ke nan, sai dai gawarta na gani.’’
Ta kara da cewa, “ofishin rundunar ‘yansanda da ke kasuwar mata Sabon Gari Zariya da maganar take hannunsu sun kira mu sun tura mu Kaduna tare da yara biyu da aka kama daga cikin yara hudu da ake zargi sun aikata wannan kisa na ‘yata.’’
Malama Rukayya ta kuma bayyana wa wakilinmu cewa, “ni ba abin da ya fi damuna daga cikin wannan lamari gaba daya sai kasancewa ya rage sauran mako guda a daura mata aure.’’
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansanda jahar Kaduna amma abin ya ci tura. Sai dai wata majiya daga ofishin ‘yansanda da ke kasuwan mata Sabon Gari Zariya ta tabbatar mana da aukuwar lamarin, inda ta ce sun kama mutum biyu, kuma suna neman mutane biyu, amma wadanda aka kama sun tura su Kaduna domin cigaba da bincike.
…An yi wa wata budurwar yankan rago
Muhammad danladi Ibrahim,Daga Minna
Wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa wata budurwa mai suna Malama Aminah Abdul-kadiri ‘yar shekara 16 yankan rago a ranar Asabar ta makon jiya da dare, suka yasar da gawarta a wata Unguwar da ake kira ‘New Market’ da ke karamar hukumar mulki ta Chanchanga a Jihar Neja.
Da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne yara suka ga gawar da aka yasar a wani gidan da ba a kammala ba yayin da suka je biyan wata bukatarsu. Ba su bata lokaci ba suka sanar da manyan da ke kusa cewa sun ga gawar wata budurwar da aka yi wa yankan rago.
Wannan ne ya sanya mutane suka dunguma zuwa gidan kuma ba su bata lokaci ba wurin shaida wa ‘Yan sanda wadanda suka dauke gawar marigayiyar zuwa asibitin kwararru na IBB da ke Unguwar Chanchaga saboda likitoci su gudanar da gwaje-gwaje domin gano musababbin rasuwar budurwar.
Marigayiyar wadda take aji uku a karamar Sakandaren ‘Yan matan da ke hanyar Bosso kusa da shahararriyar Makarantar fada, suna zaune ne rukunin gidajen gwamnati na Airport kuarters tare da kawunta mai suna Malam Muhammad Abdul-kadir, wanda ma’aikaci ne a Kotun daukaka kara ta Addinin Islama da ke Minna.
Kawun marigayiyar mai shekaru 51 da haihuwa, ya shaida wa wakilinmu cewa, a ranar da lamarin ya auku da misalin karfe biyu da rabi na rana ne suka fita da yayanta mai suna Hassan suka je sabuwar kasuwar Minna, wadda ba ta da nisa daga Unguwar, domin sayo doya. ‘’Wannan ne ya sa suka taka zuwa kasuwar tare. Yayin da suke kan hanyar zuwa kasuwar, sai yayanta Hassan ya lura da cewa an yi ta buga mata waya akai-akai, kuma bisa ga dukkan alamu ana da bukatarta ne, ita kuwa tana ta amsa wa wadanda suka yi ta buga mata wayar cewa tana zuwa. Bayan da suka sayo doyar ta hawo babur domin komawa gida, saukarta daga kan babur ke da wuya, sai aka sake buga mata waya,ta nanata musu cewar ga ta nan zuwa, ba tare da bata lokaci ba,a gaban wani makwabcinsu da misalin karfe uku na rana.Tana ajiye doyar, shi ne ta shirya ta je amsa kiran da aka yi ta yi mata a waya. Rabonmu da ita ke nan.’’
Hankalin mutanen gidan ya koma wurinta ne yayin da aka ga gari ya fara duhu kuma ba a ganta ba, sai aka buga lambar wayarta, ba a yi nasarar samunta ba, don wayar tana a kashe. Duk da ba a same ta a wannan lokacin ba, ba a daga hankali ba, don wasu lokuta ta kan je Unguwar Kwangila ta kwana a gidan Kakaninta. Sai dai akasari ta kan buga waya ta sanar da gida cewa za ta kwana a can. Ganin ba ta bugo ba don shaida wa mutanen gida,ya sa aka yi ta jiranta har karfe sha biyu da rabi zuwa daya na dare, da ba a ji duriyarta ba, aka hakura aka kwana haka.
Kashe gari ranar Lahadi aka sa ran duk in da ta shiga za ta dawo gida,shiru ba labari.Can sai mutanen gidan suka samu labarin cewa an kashe wata budurwa kuma an yasar da gawarta a Unguwar ‘New Market’,mutane na zuwa kallo. Kawunta ya ce, ko kusa ba su kawo a ransu cewa marigayiyar ce ba.Daga bisani wani Yaron da suke Islamiyya daya da marigayiyar ya zo nan gidan domin shaida wa mutanen cewa an ga ‘Yan sanda sun dauki gawar Malama Amina a cikin mota kuma an yi hanyar Unguwar Dutsen Kura da ita.
Yaron da ya kawo labarin kuwa shi ma wani ne ya sanar da shi,wanda ya yi masa kwatancenta da irin kayan da ta yi nacin sa wa, wato jan wando jeans da karamar riga,da hijabi har ya zuwa lokacin da aka yi mata kisan gillar.
Samun wannan labarin ke da wuya,sai Kawunta ya jagoranci mutane zuwa hedkwatar rundunar ‘Yan sandan da ke Dutsen-Kuran Hausa domin bincken ko an kai gawar,sai aka ce musu ba a kawo ba. A ofshin shiyya da ke GRA ne aka tabbatar musu cewar lallai an kawo gawar wata budurwar da aka yanka. An shaida musu cewa ba a ajiye gawar a nan ba, an kai ta asibitin kwararru na IBB domin likitoci su binciko sanadiyyar mutuwarta.
Zuwansu asibitin ke da wuya,suna arba da kafarta dan uwanta ya tabbatar da ita ce, inda ya yi musu bayanin cewa idan an cire safar kafarta za a ga wata alamar raunin da ta samu sanadiyyar hadarin da ta samu. Ana cire safar sai aka ga alamar,sannan aka bude fuskarta aka tabbatar da ita ce, kuma yanka ta aka yi.
Kawun ya ce ya samu labarin cewa a ranar Asabar da dare da misalin karfe tara an ga marigayiyar da wadansu kawayenta su uku wurin wani mai balangu da ke bayan kantin Bomas sun sayi nama.Bayan da suka saya sai suka tsallake titi suka shiga Unguwar Oduoye kuarters. Shi kuwa bai yi wata-wata ba,ya je ya sanar da ‘Yan sanda labarin da suka samu. ‘Yan sanda sun bukaci hotonta da lambar wayarta domin gudanar da bincike.
‘Yan sandan sun gayyato kawayen marigayiyar domin yi musu tambayoyi, watau Hadiza da Rukayya, sai ta ukun da shi kawun bai san sunanta ba.Duk da cewa marigayiyar ba ta taba shaida wa kawunta cewa tana da matsala da kawayenta ba yayin da take da rai.
Marigayiyar ta tashi a hannun kawunta ne, domin tun ba ta kai shekara biyu ba Allah Ya yi wa iyayenta rasuwa.
Wakilinmu ya je wurin mai balangun da su marigayiyar suka sayi nama a wurinsa da ke bayan kantin Bomas domin samun karin bayani game da yaran da suka sayi nama a wurinsa, sai dai ya tarar ya yi tafiya zuwa Sakkwato.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, ASP Oguche Richard Adamu.ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar lamarin, inda ya nuna cewa jami’ansu na gudanar da bincike.
Ya yaba wa mutanen Unguwar ‘New Market’ wadanda ba su bata lokaci ba wurin sanar da ‘Yan sanda halin da suka samu kansu a ciki ranar Lahadin. Ya nemi jama’a da su cigaba da taimaka musu da bayanan da za su iya sa a dakile aikata aukuwar miyagun ayyuka a tsakanin al’umma.