Abokaina sun guje ni bayan faduwa a zabe – Jonathan

Shugaban kasa mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan ya ce wasu daga cikin abokansa sun guje masa jim kadan da amincewa da kayen da Janar Muhammadu Buhari ya yi masa a zaben watan Maris. Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da yake bayani wajen addu’ar musamman da aka […]

Abokaina sun guje ni bayan faduwa a zabe – Jonathan
Abokaina sun guje ni bayan faduwa a zabe – Jonathan

Shugaban kasa mai barin gado Dokta Goodluck Jonathan ya ce wasu daga cikin abokansa sun guje masa jim kadan da amincewa da kayen da Janar Muhammadu Buhari ya yi masa a zaben watan Maris.

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da yake bayani wajen addu’ar musamman da aka shirya masa don ban kwana a Abuja.
Jonathan wanda ya amince da shan kayen a ranar 31 ga Maris, ya samu yabo a ciki da wajen kasar nan, saboda ya kwantar da kurar tashin hankalin siyasa. Ya ce, “Matakai masu wahala suna da nasu sakamakon, babu shakka a kan haka. Kuma wannan ne mataki mai matukar wahala da na dauka, don haka wajibi ne in hadu da wannan sakamako.” Ya kara da cewa: “Idan ka dauki wasu matakai, za ka ga hatta wasu mutanen da suke kusa da kai za su guje maka a wani lokacin. Na fada wa mutane cewa da dama daga cikin masu kiran kansu abokaina za su bace.”
’Yan Jam’iyyar PDP ta Shugaba Jonathan kodai sun koma Jam’iyyar APC ta Janar Buhari ko kuma sun fadi kalamai masu zafi kan jam’iyyar Jonathan ko shugabanninta.
Shugaba Jonathan ya ce bai ji mamakin guje masa ba, ko kuma kalaman da tsofaffin magoya bayansa suka rika yi ba, inda ya ce tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Frederik de Klerk ya fuskanci irin wannan hali lokacin da ya yanke shawarar ya soke mulkin wariya na fararen fata marasa rinjaye a kasarsa.
“Amma wannan ne kawai matakin da ya mayar da Afirka ta Kudu daya daga cikin masu fadi a ji a duniya. Da har zuwa yanzu ana mulkin marasa rinjaye a Afirka ta Kudu, babu wanda zai yi maganar Afirka ta Kudu a wannan lokaci,” inji Jonathan.
Sai ya ce ministocin da suka yi aiki da shi su zauna da shirin fuskantar “takurawa” saboda faduwarsa a zabe da kuma amincewa da shan kayen da ya yi daga gwamnati mai shigowa.
Sai dai a martanin Jam’iyyar APC ta ce babu wanda za a musguna masa daga mukarraban Jonathan din, amma wanda bukatar a binciki abin da ya gudanar za a nemi ya yi bayani.