Abokansa sun kashe shi saboda zargin ya satar musu kaji

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas na neman wani matashi mai suna Yahaya kan zargin hada baki da wasu mutum biyu suka kashe abokin kasuwancinsu mai suna Gbadamosi Tarba, sakamakon jayayyar da ta shiga tsakaninsu kan mallakar wasu kaji guda biyu.Binciken Aminiya ya gano cewa wadanda ake zargi Yahaya da Musa Sama’ila da kuma Usman Garba […]

Abokansa sun kashe shi saboda zargin ya satar musu kaji
Abokansa sun kashe shi saboda zargin ya satar musu kaji

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas na neman wani matashi mai suna Yahaya kan zargin hada baki da wasu mutum biyu suka kashe abokin kasuwancinsu mai suna Gbadamosi Tarba, sakamakon jayayyar da ta shiga tsakaninsu kan mallakar wasu kaji guda biyu.
Binciken Aminiya ya gano cewa wadanda ake zargi Yahaya da Musa Sama’ila da kuma Usman Garba suna  sana’ar sayar da kaji ne a unguwar Epe da ke Lagas.
Aminiya ta gano cewa fada ya kaure tsakanin Gbadamosi da abokan sana’arsa lokacin da suka zarge shi da satar musu zakaru biyu, inda suka yi masa dukan kawo wuka har sai da ya fita daga hayyacinsa.
Bincike ya nuna cewa Gbadamosi ya rasu a lokacin da aka kai shi asibitin unguwar Epe don yi masa magani.
Daga bisani ’yan sanda sun kama Musa da Usman da ake zargi da raunata Gabadamosi, amma daya daga cikinsu mai suna Yahaya ya gudu.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin shugabannin masu sayar da kaji na unguwar Epe, inda Gbadamosi yake sana’a, ya ci tura, sai dai wani wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce shugabanninsu sun hana kowa ya yi magana da manema labarai.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce rundunar ta kame mutum biyu da ake zargin sun yi sanadin mutuwar Gbadamosi.
Sai dai ta ce daya daga cikinsu mai suna Yahaya ya gudu kuma ’yan sanda na nemansa ruwa a jallo.
Ta ce da zarar ’yan sanda sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kuliya, don a yi musu shari’a ba tare da wani bata lokaci ba.
Ta bayyana cewa hankali ya kwanta kuma mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba a yankin.