Abokin mutum biyu munafikin daya
Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya zame duwawu, tilas a zauna da shi a harkokin mulki da kuma na siyasar kasar nan. Babu wata sabga, musamman ma ta sharri, wacce aka kulla tun zamanin su Sardauna don cutar da kasar nan da babu hannu Obasanjo a ciki. Yanzu kuma bayan ya gama kitsa kutungwilar […]
Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya zame duwawu, tilas a zauna da shi a harkokin mulki da kuma na siyasar kasar nan. Babu wata sabga, musamman ma ta sharri, wacce aka kulla tun zamanin su Sardauna don cutar da kasar nan da babu hannu Obasanjo a ciki. Yanzu kuma bayan ya gama kitsa kutungwilar yadda za a kai kasar kasa, ya koma gefe guda, yana ta zuga-zugin ruruta fitina, kuma wanda duk ke son galba sai ya neme shi, idan ba haka ba kuwa tuwonsa ya yi ruwa. Wannan ne ya sa a makon jiya wasu Gwamnonin Arewa, har ma da shugaban kasa suka ziyarce a fadarsa ta Abeokuta daban-daban, a rana guda, don su taba alli ta yadda za su ji dadin bin tafarkin da kowannensu ya shirya don galba a zaben 2011.
Daga cikin gwamnonin da suka niki gari daga Arewa don ziyartar Cif Obasanjo akwai: Malam Sule Lamido na jihar Jigawa da Rabi’u Musa Kwankwaso na jihar Kano da Murtala Nyako na jihar Adamawa da kuma Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako na jihae Sakkwato. Wadanan su ne gwamnonin da suka kai ziyarar yaukaka zumunci ga Gwamnan Jihar Ribas, Cif Rotimi Amaechi, aka kuma nuna masu iyakarsu, domin wasu miyagu, ‘yan asalin jihar sun yi masu marhaban da harsashan Annabi Nuhu, ba tare da tunanin cewa hakan zai iya sa mutanensu na Arewa su yi ramuwar gayyar da za ta tayar da gagarumar fitina ba.
Shi kuwa Shugaba Jonathan ya kai wannan ziyarar ce kwanaki biyu bayan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi wani taro na musamman da Cif Obasanjo, tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, kuma bayan wani na hannun daman Shugaba Jonathan, Chie Godswill Akpabio, Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya yi takakka zuwa Abuja don ganawa da Cif Obasanjo a asirce. Akwai kuma batun kafar wando guda da Obasanjo ya sanya tare da Cif Tony Anenih sakamakon bambancin ra’ayi kan tsarin gudanar da jam’iyya da kuma yadda za a sarrafa akalarta. Ba a fayyace sigar zancen da ya wakana tsakanin Shugaba Jonathan da ubandakinsa Obasanjo ba, amma sai dai Shugaba Jonathan ya ce ai Obasanjo tamkar mahaifinsa ne, kuma wannan ziyarar ta dinke duk wata barakar da ta wanzu tsakaninsu a baya.
To idan Shugaba Jonathan na ganin ziyarar da ya kai wa Obasanjo ta kawo karshen tashin-tashinar da ke tsakaninsu wacce ta kai shi Obasanjon kwancewa Jonathan zani a kasuwa a kwanakin baya, sai a ce bai ji da kyau ba, domin idan ya dinke waccan barakar wata sabuwa kuma ta wakana a tsohon gyauton jam’iyyarsu, wacce kuma bisa ga dukkan alamu ba shi da azancin yi mata dajiya don kar ta ci gaba da darewa. Wasu kuma na ganin cewa da gangan ne Jonathan ke hasassala wutar rigimar da ke ruruwa a jam’iyarsu don ta haka ne zai samu sukunin biyan bukatarsa ta zarcewa bisa mulki a 2015. An dai rigaya an tabbatar da cewa Shugaba Jonathan na da ruwa har da tsaki cikin rikicin da ya dabaibaye jihar Ribas, wanda ake gani ya samo asali ne daga kafircewar da Gwamnan jihar ya yi masa, da kuma yadda ya dage wajen watsa masa kasa a gari. Haka nan ma Uwargidan Jonathan ta yi uwa, ta yi makarbiya cikin wannan al’amari har ma ta kasance magajiyar masu iza wutar fitinar da ke ci a Jihar Ribas. Shugaba Jonathan dai ya bar jaki ne yana dukan taiki, domin kuwa maganin rikice-rikicen jam’iyyar PDP da suka jawo katankatana a Jihar Ribas na hannunsa, ba wajen Cif Obasanjo ba, wanda tun can farko shi ne ummul-haba’isin dukkan fitintinun da ke addabar kasar nan a yanzu, ba ma jam’iyar PDP ba kadai. Idan kuwa haka ne ashe ya ba kura ne ajiyar nama.
Su kuma gwamnonin Arewa da suke ta wadari a halin yanzu tsakanin Abeokuta da Minna don neman maganin annobar rikicin PDP don kada ta karade ko ina a kasar, sun daura yaki ne za su ci gadonsu, domin kuwa Obasanjon da suke yi kallon kitse ashe ganjin rogo ne, wanda bai ciwuwa, ba kuma zai taimake su da komai ba illa ma ya kara tura su cikin ramin kura, ta kuma fito ta ciccije su. Wane ne ya fara tozarta Gwamna Rotimi Chibuike Amechi, wanda gwamnonin Arewar ke dada kansu da kasa a kansa, ba Cif Obasanjo ba? Sun mance ne da halinsa na yankan baya? Ai ba wani hamshakin dan siyasa a fadin tarayyar kasar nan da bai da tabon Obasanjo, kuma idan a yanzu ya ce zai taimaka masu karya yake, domin kuwa har yanzu yana nan tare da Jonathan, kuma abokin mutum biyu munafikin daya ne.
Obasanjo dai shu’umin mutum ne, wanda ke hada baki da Yahudu da Nasara don ganin bayan kasar haihuwarsa, an kuma tabbatar da haka ba sau daya ba, ba sau biyu ba. A yanzu ya samu shugaba Jonathan inda yake so, gwamnonin jam’iyarsa kuma sun rungumi dagutocin da ba su iya ceton kawunansu ba daga tarkon da ya rigaya ya kafa masu tun can farko, balle su agaji gwamnonin da ya makanta, ya bar su da ja masu gora.
Wato ke nan ana iya cewa an ja daga don dambacewa tsakanin wasu tsirarun Gwamnonin Arewa da ladifan iyayen gidansu, wadanda su ma bakinsu daya ne da Obasanjo a daya bangaren; ga kuma Shugaba Jonathan da Yahudu ke goyon baya a daya gefen; Cif Obasanjo, a matsayinsa na kanwa uwar gami, na tsakiya, yana kada kurya gangar mutuwa don a taru duka a lalace, kasar kuma ta rugurguje. Babu wani abin da tsoffin janarorin kasar nan, da ke cikin jam’iyar PDP, za su iya yi don ceto dimokuradiyya daga rugujewa kaman yadda Gwamnonin Arewa suka bukace su da yi, domin kuwa wadanda ke dagula ruwar siyasar Najeriya iyayen gidansu ne, ba kuma wanda zai taba bijirewa ubangidansa. Wannan matsala dai ta PDP ce amma alakullihalin ana so sai ta gauraye Najeriya.