Abu dankure ya samu kansa daga masu garkuwa da mutane
Shahararren dan kasuwar nan kuma dan siyasa a Jihar Sakkwato Alhaji Abu dankure da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Larabar makon jiya ya samu kansa a ranar Litinin da ta gabata bayan da aka ce an biya fansar Naira miliyan 51 kansa. Lokacin da Aminiya ta ziyarci gidansa da ke Dandi ko […]
Shahararren dan kasuwar nan kuma dan siyasa a Jihar Sakkwato Alhaji Abu dankure da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Larabar makon jiya ya samu kansa a ranar Litinin da ta gabata bayan da aka ce an biya fansar Naira miliyan 51 kansa.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci gidansa da ke Dandi ko Gangare ta iske dimbin masoya da abokan arziki na ta yin tururuwa don yi masa barka kan waki’ar da ta fada masa. Cikin wadanda suka je yi masa barka da arziki har da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa.
Alhaji Abu dankure ya shaida wa manema labarai ya cewa “Mutanen da suka sace ni bayan sun sa ni a mota sun rufemin fuska ban sake sanin inda nake ba, tsawon kwanakin da na yi a wurinsu, sai dai ina zargin suna yawo da ni ne a kauyakan wannan gari a tsawon lokacin da na dauka a wuinsu, amma ba su
takurar mini ba, ina yin Sallah da cin abinci, shi ne ma dalilin da kuka gan ni cikin koshin lafiya ba wata damuwa a tare da ni.”
Alhaji Abu dankure ya ce bai san yawan mutanen ba, kuma harshen Ingilishi da Hausa ne abin da suke magana da shi.
Da aka tambaye shi ko sun amshi wani abu ga hannun iylansa kafin sako shi? Sai ya ce “ A bar wannan magana, ni dai na san ba su taba lafiyata ba, amma sun canja min tufafi daga babbar riga da ’yar cikinta da zuwa karamar riga ta yara (t-shirt) da wando jins da hula hana Sallah, kuma da wadannan kaya
suka ajiye ni a inda iyalina suka dauko ni.”
Ya gode wa duk wadanda suka taimaka masa da duk wani abu da suke iyawa, kamar Gwamnan Jihar
Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko da ’yan jarida da sarakuna da al’umma baki daya.
Murtala S.T., ya shaida wa Aminiya cewa mutanen sun kira iyalan dankure da misalin karfe 8:30 na dare ne suka gaya musu su tafi bakin masallacin Juma’a na Abubakar na Uku da yake gefen gari su tafi
da mahaifinsu, kuma suna zuwa wurin.
Wata majiya da ba a tabbatar ba ta ce an karbi Naira miliyan 51 kafin a sako shi inda manya ’ya’yansa uku suka kasa kudin a tsakaninsu, Alhaji Sirajo Kure ya ba da Naira miliyan 25, sai Nura Kure Naira miliyan 11, sai Aminu Kure Naira miliyan 14 kuma a Abuja aka biya kudin. Wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da aka yi garkuwa da wani mutum a jihar.