Abubakar Haruna, Daga Legas A ci gaba da gasar cin kofin qalubale na kamfanin Glo da ake gudanarwa, kulob xin Sunshine Star yasamu nasara a kan na Kano Pillers da ci uku da xaya. Nasarar da Sunshine Star ta samu ya baiwa kulob xin damar samun maki 26 in

Abubakar Haruna, Daga Legas A ci gaba da gasar cin kofin kalubale na kamfanin Glo da ake gudanarwa, kulob din Sunshine Star yasamu nasara a kan na Kano Pillers da ci uku da daya.Nasarar da Sunshine Star ta samu ya baiwa kulob din damar samun maki 26 inda hakan ta sa yake sahun farko a […]

Abubakar Haruna, Daga Legas A ci gaba da gasar cin kofin qalubale na kamfanin Glo da ake gudanarwa, kulob xin Sunshine Star yasamu nasara a kan na Kano Pillers da ci uku da xaya. Nasarar da Sunshine Star ta samu ya baiwa kulob xin damar samun maki 26 in
Abubakar Haruna, Daga Legas A ci gaba da gasar cin kofin qalubale na kamfanin Glo da ake gudanarwa, kulob xin Sunshine Star yasamu nasara a kan na Kano Pillers da ci uku da xaya. Nasarar da Sunshine Star ta samu ya baiwa kulob xin damar samun maki 26 in

Abubakar Haruna, Daga Legas

A ci gaba da gasar cin kofin kalubale na kamfanin Glo da ake gudanarwa, kulob din Sunshine Star yasamu nasara a kan na Kano Pillers da ci uku da daya.
Nasarar da Sunshine Star ta samu ya baiwa kulob din damar samun maki 26 inda hakan ta sa yake sahun farko a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar.
Wasan wanda aka gudanar a filin wasa na garin Akure a karshen makon da ya gabata ya kayatar da jama’a.
kwallon farko da dan wasa Sunshine mai suna Paul Onobi ya zura a ragar Kano Pillers ya kara wa ’yan wasan kulob dinsa kaimi. Sai Seun Oludayo ya zura kwallo na biyu a ragar Kano Pillers wanda hakan ya sanya gwiwar ’yan wasan Kano Pillers ta yi sanyi.
Daga bisani ne kuma Dayo Ojo ya zura kwallo ta uku da hakan ya baiwa kulob din Sunshine Star nasarar lashe wasansu na takwas a gasar kawo yanzu.
Mai horar da ’yan wasan kulab din Sunshine Star Kannedy Boboye ya bayyana farin cikinsa dangane da nasarar da kungiyarsa ta samu. Kennedy ya bayyana cewa kulab din Kano Pillers ba kanwar –lasa ba ne saboda kwararrun ’yan wasa da suka tara.
Shi kuwa mai horar da ’yan wasan Kano Pillers, Okey Emordi ya ce ba shi da abin da zai ce dangane da sakamakon wasan.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram