Abubuwa 10 da ke cikin Dakin Ka’aba
An kera kofar Ka’aba ne da tattaccen zinare da dauyinsa ya kai kilogram 280
Ka’aba shi ne daki mafi falala a duniya, kuma yana nan ne a Masallacin da babu kamarsa wajen falala da muhimmanci a ban kasa.
A duk shekara, miliyoyin Musulmi daga sassan duniya kan je kasar Saudiyya domin yin aikin Hajji da Umra a wannan Masallaci inda suke Dawafi ta hanyar zagaye wannan daki.
- Hajarul Aswad: Muhimman abubuwan game da dutse mai daraja
- Buhari da Gwamnoni sun halarci daurin auren dan Sarkin Kano a Sakkwato
Kowane Musulumi na burin samun damar ya taba Ka’aba, musamman ma dutsen Hajarul Aswad da ke jikinsa — Uwa uba shi ne samun shiga cikin dakin, wanda a tsawon zamani, sai mai tsananin rabo.
Shin kun san abubuwan da ke cikin wannan daki mai Alfarma, wanda aka gina tun zamanin Annabi Ibrahim?
Ga wasu daga ciki da kuma bayanansu, har da hotuna da muka samo muku:
Kofar Ka’aba
An kera kofar Ka’aba ne da narkakken zinare kuma nauyinsa ya kai kilogram 280; An yi wannan aiki ne a zamanin Sarki Khalid na kasar Saudiyya, inda aka kawata kyamare biyu na kofar da zayannar rubutun ayoyin Alkur’ani da wasu zikirori.
Makullin Ka’aba
Ana rufe Ka’abah ne da kwado da makulli na musamman, wanda a halin yanzu makullin na musamman ke karkashin klawar Mataimakin Mai Kula da Ka’aba, Sheikh Abdul Malki bin Taha Al Shaibi. Babban Mai Kula da Ka’aba shi ne Sheikh Salih Al Shaibi.
Bab Al Tawbah
Bab Al Tawbah (kofar zuwa rufin Ka’aba) an yi ta ne da tataccen zinare da aka kawata da zayyanar rubutun Larabci.
Kofar ma da makullinta na musamman kuma a gefenta a kwai wani allon farin dutse dauke da bayanan ginin kofar da aka yi da zayyanar rubutun Larabci a zamanin.
Jauharin ciki
Wadannan jauhari da aka rataye daga sama kyaututtuka ne da sarakuna da ’ya’ya sarakuna suka kawo wa Ka’aba a tsawon daruruwan shekaru.
Wadannan kyaututtuka mallakin Ka’aba ne kuma daga cikinsu akwai kwanuka da tasoshi na zallar zinare da azurfa; akwai kuma wadanda aka yi wa ado da ruwan zinare da azurfa da lu’ulu’u da zabarjadu da sauran tuwatsu masu daraja.
Bangon Ka’aba
An shafe bangon Ka’aba ne gaba daya da farin dutsen ‘marble’ da kuma ratsin kore, wanda aka yi a zamanin Sarki Fahd na Saudiyya a shekarar 1996.
A lokacin ne aka shafe rufin dakin ta ciki da farin ‘marbe’, sannan aka toge shi da al’amudai uku da aka yi daga icen ‘teak’ na yankin Burma.
Silin din Ka’aba
Daga saman bangon Kaba’a har zuwa silin dinsa kuma an lullube shi da wani koren kyalle wanda aka kawaya shi da zayyanan rubutan Larabci.
Wurin da Annabi (SAW) ya yi Sallah
A daben dakin Ka’aba akwai alama da aka sanya a wurin da ake kyautata zaton a dai-dai nan ne Manzon Allah (SAW) ya yi Sallah bayan ya shiga dakin a ranar da ya ci Makka da yaki (Fathu Makkah).
Idan mutum yana cikin dakin Ka’aba, zai iya fuskantar kowace kusurwa ya yi Sallah; Shi ma daben dakin shafe shi da farin ‘marble’ da rashin kore.
Al Multazam
Al-Multazama shi ne tsakanin kusurwar dutsen Hajarul Aswad da kofa ta cikin dakin Ka’aba — fadinsa kimanin mita biyu ne.
Sahabin Manzon Allah (SAW), Abdullahi bin Abbas, ya ruwaito Hadisi cewa addu’ar da aka yi a Multazam karbabbiya ce.
Farin allon dutsen can da ake gani na dauke ne da bayanan aikin garambawul da aka yi wa Ka’aba ne a 2019.
Kabet din cikin Ka’aba
A tsakanin al’amudai biyu da ke cikin Ka’aba akwai wani karamin kabet, wanda a cikinsa aka adana turaren Oud da sauran kayan da ake amfani da su a bikin wanke dakin.
Saman bangon Kaba’a da silin dinsa kuma lullube yake da wani koren kyalle da aka kawaya da zayyanan rubutan Larabci.
Allunan rubutu
Kamar yadda aka bayyana, fararen allunan dutse da ke cikin Ka’aba suna dauke ne da bayanin ayyukan gyaran dakin da aka yi daga lokaci zuwa lokaci.