Abubuwa 10 da mata za su yi don faranta wa mijinsu (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon da ya gabata. Allah Ya sa wannan rubutu ya amfanar da masu bukatarsa, amin.6 Addu’a: A duk lokacin da mijinku zai fita idan ya ji kun yi masa addu’a sai […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon da ya gabata. Allah Ya sa wannan rubutu ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
6 Addu’a: A duk lokacin da mijinku zai fita idan ya ji kun yi masa addu’a sai ya ji farin ciki ya kama shi, hakan kuma zai sa ya dage wajen nemo abin da za a ci a gidan, domin ya san kun san fitar da zai yi tana da muhimmanci a wurinku. Ku rika cewa: “Allah Ya kiyaye, “Allah Ya dawo da kai lafiya,” ko “Allah Ya sa a fita a sa’a,” ko kuma “Allah Ya sa a samo abin da aka je nema,” da sauransu
7. Godiya: Babu abin da namiji yake so face idan ya fita ya nemo wani abu ya kawo gida, walau ya sha wahala ko cikin sauki har idan ya kawo gida, ya ji matarsa ta yaba, sannan ta yi godiya. Yana da kyau mata su rika gode wa mijinsu, hakan zai rika sanya shi farin ciki. Wani lokaci ma matan za su iya kambama abin da ya samo, ta hanyar bayanin yadda al’amura suka yi tsanani, su rika nuna ba karamin kokari mijinsu ya yi ba. Su nuna sun yi sa’ar miji. Yin godiya ga miji zai sa ya ji farin ciki, sannan ya zage damtse wajen neman abinci don ya kawo gida. Kada mata su manta Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk matar da ba ta gode wa kyautar mijinta ba, to Allah (SWT) ba Ya kallonta (da rahama).”
8. Tausasa lafazi: Miji kan yi farin ciki a duk lokacin da matarsa take yi masa magana cikin tausassan lafazi. Domin ya fahimci akwai girmamawa daga matarsa. Ko da miji ya yi muku abin da ba ku so, to kada ku manta da yin bayani cikin lafazi mai taushi, kada ku ce kullum mijinku na maimaita abin bakin cikin da yake muku, su fahimci daga murya ba zai sanya ya daina ba, amma ta hanyar amfani da lafazi mai taushi sai ta sa zuciyar miji ta yi sanyi har ya yi nadamar abin da ya aikata, ya bada hakuri, sannan farin ciki ya wanzu a tsakanin ma’auratan.
9. Tausayi: Idan mata suka rika tausaya wa mijinsu musamman mijin da yake shan wahala wajen nemo cefane, to zai rika jin farin ciki. Kada ya fita ya samo abin da za a ci da kyar amma ku rika kushewa ko korafi a kai, ku rika cewa gidansu wance abinci sai an ture, ko kuma kowane wata sai ya yi mata dinki. Mata su fahimci kowa da karfinsa. Tausaya wa miji wani sinadari ne da zai sanya miji cikin farin ciki.
10 Girki: Wata hanya mai matukar muhimmanci da mata za su faranta wa mijinsu ita ce, wajen iya girki. Akwai wani abokina ya ce dalilin da ya yake kara son matarsa shi ne, yadda ta kware wajen iya girki iri-iri. Idan mata suka iya girki za su samu wata daraja ta musamman a wurin mijinsu, zai kuma rika jin farin ciki, domin duk wahalar da ya sha wajen yin cafane ya san kwalliya za ta biya kudin sabulu. Idan mata ba su iya girki ba ya kamata su koya, kada su tsaya a salon girki iri daya kawai, hakan zai gunduri mijinsu, har ya rika korafi, inda maimakon samun farin ciki sai ya rika jin haushi.
A karshe ina fata mata za su bi wadannan hanyoyin don faranta wa mijinsu. Allah Ya taimake mu, amin.
Bashir Liman ya rubuto daga Jos.
Za a iya samunsa a wannan lambar 07036925654.