Abubuwa 10 game da mawaki Dauda Rarara

Ya yi wa ’yan takarar shugaban kasa hudu wakar neman zabe kuma duk sun yi nasara.

Abubuwa 10 game da mawaki Dauda Rarara

Mawaki Dauda Kahutu Rarara. (Hoto: Rabiu Garba Gaya)

Dauda Adamu Kahutu Rarara shahararren mawakin siyasa ne a Najeriya da ma kasashen ketare.

Ya yi wa ’yan takarar shugaban kasa hudu wakar neman zabe kuma sun yi nasara.

Ga wasu abubuwa 10 da za ku so sani a game da shi:

1. Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara dan asalin kauyen Kahutu ne da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.

2. An haife shi a watan Satumbar shekaran 1986, kuma a mahaifarsa ya yi karatun firamare da sakandare. Sanann ya yi karatun allo a Jihar Kano.

3. Mahaifansa Alhaji Adamu da Hajiya Halima sun ba shi goyon baya a harkar waka, inda suka sa shi ya koyo kuma suke mara masa baya idan yana yi a bainar jama’a.

4. Gabanin babban zaben shekarar 2015 Rarara ya wayi gari a matsayin fitaccen mawakin siyaya a Nigeriya.

5. Wakokinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar jam’iyyar  adawa ta APC da dan takararta na shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

6. Rarara ya kuma yi wakokin yakin neman zabe ga Mohammed Bazoum  na Nijar wanda shi ma a karshe ya lashe zaben shugaban kasar.

7. A gabanin zaben Najeriya na 2023 ya yi wa Bola Ahmed  tinubu na APC wakar kuma shi ma ya lashe zaben.

8. Haka kuma ya yi wakar neman zaben dan takarar shugaban kasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Itno Deby, wanda shi ma ya lashe zaben.

9. Daga cikin fitattun wakokinsa akwai: Masu Gudu Su Gudu, Baba Buhari Dodar, Aisha, da kuma wakar Fatima Mai Zogale, wadda a sanadiyyarta wata mai sana’ar sayar da zogale a Abuja ta samu daukaka.

10. Rarara ne shugaban kungiyar matasan Kannywood ta 13×13, wadda ke da mambobi  13, kuma kowanne daga cikinsu na da mutum 13 a karkashinsa.

11. A shekarar 2020 ya bukaci magoya bayan Shugaba Buhari su ba da gudummawar Naira 1,000 kowannensu domin ya yi wakar bayyanna ayyukan Buhari, inda aka hasa masa Naira miliyan 57 a cikin awa 48.