Maganganu 5 da shugabannin Afirka suka gaya wa taron MDD

Ghana ta nemi Turawa su biya diyyar bautar da ’yan Afirka, Guinea ta ce su daina neman juya shugabannin nahiyar

Maganganu 5 da shugabannin Afirka suka gaya wa taron MDD

Shugaban gwamnatin mulkin sojar kasar Guinea, Mamady Doumbouya,

A yayin da ake wa shugabannin Afirka kallon ’yan amshin shatan manyan kasashen duniya, wasu daga cikinsu sun yi wasu maganganu a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, wanda za a iya cewa kan mage ya waye.

Daga cikinsu akwai wadanda ake iya cewa sun nuna wa manyan kasashen yatsa, duk da cewa ba a yi tunanin za su hakan ba, saboda yadda suke neman gindin zama ko tallafi daga wurin iyayen gidan nasu.

Alal misali, Ghana ta nemi Turawa su biya diyyar bautar da ’yan Afirka; Guinea ta nuna musu yatsa kan neman juya shugabannin Afirka; DR Congo ta ce sojojin MDD ba su da amfani; Najeriya ta caccake su kan sace albarkatun Afirka; da dai sauransu

Ga biyar daga cikin magannganun:

1- DR Congo: Sojojin MDD ba su da amfani

Shugaban kasar Dimokuradiyyar Cong, Felix Tshisekedi, ya umarci dakarun dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD su fice daga kasarsa saboda bai ga amfaninsu, kuma ya ba su wa’adin wata uku su fara barin kasar.

Tshisekedi ya shaida wa taron MDD cewa ya soke shekara guda a wa’adin zaman dakarunta na MUNOSCO a kasarsa, saboda sun kasa aikin da aka kai su na kare fararen hula da yakar kungiyoyi masu dauke da makamai suke addabar yankin gabashin kasar.

Ya ce “Abin kunya ne a tsawon shekaru 25 rundunar… ta kasa magance tarzoma da rikicin masu dauke da makamai.

“Na sa a fara tattaunawa da MDD su gaggauta kwashe dakarun MONUSCO… a watan Disamban 2023 maimakon Disamban 2024.”

Ya ce, al’ummar kasarsa sun gaji da su, inda aka sha yin boren kin jininsu.

Akalla mutum 40 ne aka kashe, aka jikkata wasu da dama a rikicin kin jinin MDD a birnin Goma da ke gabashin kasar a watan Agusta.

2- Ghana: A biya mu diyyar bautar da kakanninmu

Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana ya bukaci kasashen da suka yi mulkin mallaka a Afirka su biya kasashen nahiyar diyyar bautar da iyaye da kakanninsu.

Ya ce, “Yawancin kasashen Turai da Amurka an gina su ne da arzikin da aka samu daga gumi da hawaye har ma da jinin kakanninmu da suka bautar da kuma irin tashin hankalin da zamanin bauta ya jefa al’ummar Afirka.”

Akufo-Addo ya jaddada muhimmancin biyan diyyar a yanzu, inda ya fadar hakan ya zama dole, saboda kasashen da ake magana ba sa son biyan diyyar bautar da ’yan Afirka da suka yi, duk kuwa da irin ta’adin da suka yi wa nahiyar.

3- Guinea: Mu ba yaran Turawa ba ne

Shugaban gwamnatin mulkin sojar kasar Guinea, Mamady Doumbouya, ya shaida wa kasashen Turawa a taron cewa su daina neman zaba wa Afirka irin salon mulkin da suke tunanin ya dace da nahiyar.

Kanar Doumbouya, wanda ya yi juyi nulki a 2021 ya ce, tsarin mulkin da kasashen Yamma ke so a Afirka su kawai yake amfana, amma yana cutar da al’ummar nahiyar.

“Afirka na wahala a sakamakon irin salon mulkin da aka dora ta a kai… wanda kasashen Yamma yake amfana, don haka suke ganin dacewarsa.

“Amma da wuyan gaske a cewa tsarin ya dace da yanayin al’ummarmu da al’adunmu; Lokaci ya yi a ku daina gaya cewa za ku ne za ku gaya mana abin da ya dace da mu, kuna son ku rika juya mu kamar kananan yara.”

4- Najeriya: A daina sace albarkatun kasa

A nasa bangaren, shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) kuma Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, cewa ya yi manyan kasashen da suke sace arzikin kasashen Afirka su ne musabbabin talauci da tashe-tashen hankula a nahiyar.

Ya gaya wa Sakatare-Janar na MDD, Antonio Guterres cewa Afirka ba za ta lamunci yadda manyan kasashen ke fasa-kwaurin makamai da sauran miyagun abubuwa zuwa cikinta ba, suna sace mata albarkatun kasa da ma’adinai.

Ya ce ba za mu lamunci, “’yan bola-jari da ke lalata mana kasashe su danne al’ummarmu, suna hakar ma’adinanmu ta bayan fage su kwashe arzikin kasarsu zuwa kasashensu, a sirrance ko ta hanyar rikici ba.”

Don haka ya ce, “Za mu taka musu burki, babu wanda za mu raga wa; duk wanda ke son hulda da mu, sai mun yi masa tambayoyi mu san manufarsa.”

Ya yi wannan maganar ne a zantawarsu da Guterres kan raunin MDD wajen daukar matakan magance matsalar tsaro da talauci a Afirka, kuma Sakatare-Janar din ya amince da bukatar kara wa kasashen karfin iko a zauren.

5- Zimbabwe: Zaben kasarmu sahihi ne

Duk da sukan da kasarsa ke sha da tabarbarewar tattalin arziki, Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe ya shida wa MDD cewa zaben da ya lashe ya samu tazarce sahihi ne, kuma an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.

Mnangawa wanda shekara 43 jam’iyyarsa ta Zanu-PF ke mulkin kasar tun bayan samun ’yancin kai a 1980, ya bayyana wa taron na MDD ne, duk da cewa al’ummar kasar na ganin tazarcensa za ta kara jefa su cikin matsin rayuwa.

Mnangawa, wanda shi ne shugaban kasar na biyu, bayan hambararren tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, yana jagorantar kasar ne a daidai lokacin da talauci ya yi wa kasar katutu.

A baya Zimbabwe ta kasance babbar cibiyar samar da abinci da kamfanoni a Kudancin Afirka, inda turawa da masana’antu ke rububin zuwa.

Gwamnatinsa da Mugabe ta sha suka, musamman daga kasashen turawa, kan matsa wa ’yan kasashensu da kwace gonakinsu da gwamnatin kasar ta yi, da kuma batun fatara a kasar.