Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan sabon Shugaban JAMB

Farfesa Aina shi ne ya kafa tarihin zamowa farfesan injiniyancin kwamfuta mafi ƙarancin shekaru a Najeriya.

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan sabon Shugaban JAMB

Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB), wanda zai maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede.

Mashawarcin Shugaban Ƙasa a ɓangaren yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan, bayan cikar wa’adin tsohon Farfesa Oloyede tun a ranar 31 ga watan Yuli.

Kan haka ne muka zaƙulo muku wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da sabon rajistaran:

  1. Farfesa ne a sashen Injiniyan Kwamfuta a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), da ke Ille-Ife.
    Ana kallonsa a matsayin ƙwararre da ke da ƙwarewa a fannin tsarin shirya jarabawa da kuma harkokin ilimi na yanar gizo.
  2. ⁠Ya yi digirinsa na farko a fannin Injiniyan Kwamfuta a Jami’ar Kent da ke Birtaniya, da digiri na biyu da na uku a Jami’ar Loughborough da ke ƙasar.
  3. Ya yi aikin yi wa ƙasa hidima a Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a (JAMB).
  4.  ⁠Yayi aiki a hukumomin shirya jarrabawar NECO, NABTEB, da kuma ma’aikatun ilimin jihohi daban-daban.
  5. Ya zamo rajistaran JAMB mafi ƙarancin shekaru a tarihi, inda zai cika shekaru 40 a watan Yuli. Haka zalika, shi ne ya kafa tarihin zamowa farfesan injiniyancin kwamfuta mafi ƙarancin shekaru a Najeriya.