Abubuwa 5 da za ki sanya a jakar kwalliyarki

Ina fatan ‘yan mata na da jakar kwalliya. Ko mece ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka ce da za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar su; jambaki, gazal, hoda da sauransu. Akwai abubuwa da dama wadanda suka cancanta ki sanya a jakar kwalliyarki don inganta adonki. A yau mun kawo miki kadan daga ciki; […]

Abubuwa 5 da za ki sanya a jakar kwalliyarki
Abubuwa 5 da za ki sanya a jakar kwalliyarki

Ina fatan ‘yan mata na da jakar kwalliya. Ko mece ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka ce da za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar su; jambaki, gazal, hoda da sauransu. Akwai abubuwa da dama wadanda suka cancanta ki sanya a jakar kwalliyarki don inganta adonki. A yau mun kawo miki kadan daga ciki;

·         Hodar fandeshi: Hoda ce da za ki fara shafa ta a fuskarki kafin ki fara kwalliya. Wannan hodar takan sanya fuska ta yi haske. Ana so ki shafa hodar fandeshi da yatsun hannayenki.
·     Hodar  ‘Concealer’: Wannan hodar na taimakawa wajen boye bakaken tabon ko dabbare-dabbaren da ke fuska. Akan shafa ta ne bayan an sanya hodar fandeshi.
·         Maskara : Akan yi amfani da Maskara don taje gashin ido da kuma sanya wa gashin ido launi. Akwai sababbin kaloli na maskara a kasuwa wadanda za ki iya saya don kara wa gashin idonki kyau.
·         Gazal: Gazal na kara wa idanu haske. Idan kina son idanunki su yi haske sai ki rika sanya gazal.
·         Jan-baki/man baki: Jan-baki ko man baki suna sanya leba laushi. Ki zabi jan bakin da ya dace da launin fatarki don inganta kwalliyarki.