Abubuwa 7 da suka fifita Ranar Arafa ta 2022

A ranar Arafa da ta kasance ranar Juma’a ce Allah Ya cika addinin Musulunci, a Hajjin Bankwana na Manzon Allah (SAW).

Abubuwa 7 da suka fifita Ranar Arafa ta 2022

Cikin ikon Allah a 2022, tsayuwar Arafa ta kasance a ranar Juma’a.

Juma’a ita ce ranar Idin Musulimi a kowane mako, Arafa kuma ita ce ranar kololuwar aikin Hajji kuma yini mafi alheri a shekara.

Ga wasu abubuwa da suka sa haduwar wadannan abubuwa a rana guda zama na musamman:

  • Ninkin alherai

Juma’a ranar farin ciki ce, haka ma ranar Arafa — Allah Na amsa addu’o’i da kuma yafe wa bayinSa — don haka a bana Musulmi sun samu wannan falala.

  • Lada na musamman

Manzon Allah (SAW) ya ce aikin Hajji daya da aka yi tsayuwar Arafa a ranar Juma’a daidai yake da aikin Hajji 72 da ba a yi tsayuwar Arafa ranar Juma’a ba.

  • Garabasa biyu

Annabi Muhammad (SAW) ya ce a duk ranar Juma’a akwai wani lokaci da Allah Ke amsa duk addu’ar da aka yi.

Ita ranar Arafa ana amsa addu’a, don haka a wannan shekara biyun sun hadu a rana guda.

  • Hudubobi biyu

Kamar yadda Musulmi ke taruwa domin sauraron hudubar Juma’a haka ma alhazai ke taruwa su saurari hudubar Arafa.

  • Babbar ranar tarihi

A ranar Arafa da ta kasance ranar Juma’a ce Allah Ya cika addinin Musulunci, a Hajjin Bankwana na Manzon Allah (SAW).

  • Ranar yafiya

A ranar Arafa Allah Ya yi wa yawancin bayinSa gafara da kuma ’yanta su daga wuta zuwa Aljanna.

  • Kamar ranar Alkiyama

Ranar Alkiyama za ta kasance a ranar Juma’a, ranar da duk halittu za su taro a filin Alkiyama.

A ranar Arafa kuma alhazai daga sassan duniya za su taru a fili daya, wanda hakan ke tunatarwa game da ranar hisabi.