Abubuwa hudu ba su da amfani a Najeriya
Ga dukkan alamu abubuwa hudu ba su da amfani a Najeriya. (1) Arzikin Kasa (2) Mutanen Kirki (3) Ilimi (4) hankali. Na fadi haka ne saboda da ana yin amfani da wadannan muhimman abubuwa hudu da na jero a sama yadda ya kamata da ba mu shiga mugun halin da muke ciki a kasar nan […]
Ga dukkan alamu abubuwa hudu ba su da amfani a Najeriya.
(1) Arzikin Kasa
(2) Mutanen Kirki
(3) Ilimi
(4) hankali.
Na fadi haka ne saboda da ana yin amfani da wadannan muhimman abubuwa hudu da na jero a sama yadda ya kamata da ba mu shiga mugun halin da muke ciki a kasar nan a yanzu ba.
Daga lokacin da aka fara fitar da danyen man fetur daga Najeriya zuwa wasu kasashe ana sayarwa zuwa ranar 1 ga Oktoban bara (2018) an sayar da man da ya kai na Dala tiriliyan (wato Dala biliyan 1000). Ban san yadda zan bayyana wannan adadi a Naira ba, sai dai mu yi ta yara wato Naira malala gashin tunkiya! Daga cikin wannan adadi na Dala biliyan dubu daya, barayin shugabanni sun sace Dala biliyan 500, wato rabin kudin sun boye su a kasashen waje yayin da kusan kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya suke fama da kazamin talauci da kuncin rayuwa da mayata da yunwa da cututtuka.
Wadannan barayin shugabanni sun kuma hana mutanen kirki zuwa kusa da mulki don kada a hana su ci gaba da sata da kisa ko a kwace abin da suka sata a hukunta su a tsawon shekara da shekaru.
Mafi saukin halin da ake ciki a yanzu an samu shugaba ne da ake yi masa shaidar ba barawo ba ne, sai dai abin tambaya na kewaye da shi da sauran mukarrabai a tarayya da jihohi da kananan hukumomi da ma’aikatu da hukumomin gwamnati haka suke? Sanin kowa ne shugaban nan an kewaye shi da barayi suna hana wadanda ba ire-irensu ba su isa kusa da shi, balle su taimake shi wajen aiwatar da abin da ya kamata wajen gina kasa da hana ci gaba da sata da kisa da sauran laifuffukan da ake fama da su a kasar nan.
Ina fata Allah Ya karkato da hankalin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kumaYa tunatar da shi tarihin Annabi Yusuf (AS) wanda ’yan uwansa suka jefa shi a rijiya da ransa bisa fatar ya mutu ko wadansu su tsince shi su tafi da shi wata kasa su sayar da shi, a karshe sayarwar ta zame sanadin samun mulki gare shi. Allah Ya ganar da Shugaba Buhari ya gane makiran da yake tsananin kauna ido-rufe suna amfani da kaunar da yake yi musu, suna jefa gwamnatinsa a hallaka suna jawo masa bakin jini a idon jama’a don bukatunsu na samun kazamar dukiya. Suna hada kai da makiyansa don aikata abubuwan da yake yaki da su.
Wannan ya sa hatta a wannan gwamnati da talakawa suka yi tsaye wajen kafuwarta an rika samun korafe-korafe cewa wadansu sun kanainaye Shugaban Kasa sun hana mutanen kirki da dama isa gare shi. Wannan ne kuma ya sa Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari ta rika kokawa a kafafen watsa labarai kan haka a shekarun baya. A wancan lokaci mutane da dama sun rika suka da zarginta kan korafin da ta yi, amma abin da mutane suka kasa ganewa shi ne ta fi kowa son mijinta ya samu nasara, ta fi kowa son mijinta ya yi abin kirki, ko ba komai ba, ta huta da gori da suka daga jama’a cewa mijinta ya gaza.
Wani abin takaici kuma shi ne duk masu ilimin da muke da su na addini da na Bature (boko), sun kasa hada kai su ilimantar da mu kan yadda za mu ceto kasar nan daga hannun miyagu tare da dora ta a kan hanyar ci gaba da kuma tabbatar da cewa masu mulki suna yin mulki na adalci kamar yadda Allah Yake so. Maimakon haka, sai suke taya bera buruntu ta hanyar gwara kan mabiyansu, don a ba miyagun shugabannin damar ci gaba da aikata tu’annati da fasadi da barna da dukiyar jama’a. Wannan ya sa muka wayi gari yau kowace kabila ko kowane addini ko kowace jam’iyya ko kowace jiha, ba ta so a taba danta da ya aikata ba daidai ba. Da wannan sai ya zamo ana siyasantar da komai a kasar nan ta yadda duk barnar da wani ya yi, sai a nuna ai don dalilin kabilarsa ko addininsa ko jam’iyyarsa ko yankinsa ake yi masa terere.
Da wannan sai aka ci gaba da rasa kyakkyyawan shugabanci har ya zame jiki cewa duk lokacin da wani ya tafka barna to ya yi maza ya koma bangaren da ke mulki a jiha ko tarayya don samun mafakar da za a rufe wannan barna. Masu ilimin cikinmu duk suna ganin wannan hali, amma sun yi gum. Wadansu daga cikinsu ma sun zama ’yan a bi yarima a sha kida, da su ake shan lagwadar, wadansu kuma sun zama masu raunin imani, sun kasa hanawa da hannu sun kasa fada cewa abubuwan da ake yi ba daidai ba ne, yayin da wadansu ma suke ganin ba laifi ba ne wanda aka ba shi amana ya kwasa ya rika sammar da kalilan ga kalilan din jama’a.
Kuma masu hankali suna gani ’ya’yansu suna ta aikata ta’asa da barna suna sata da fashi da makami da fashi da mukami da shaye-shayen miyagun kwayoyi suna fita daga cikin hankulansu suna aikata masha’a da zinace-zinace da luwadi da madigo da fyade da kisan kai, amma sun yi gum ko sun kawar da kawunansu daga haka! Saboda yanzu sun koma bautar ’ya’yan suna gudun bacin ransu! Kai wadansu iyaye ma suna tafka sata ta fitar hankali ne saboda wai kada ’ya’yansu su shiga wahala a nan gaba, alhali su iyayensu sun haife su ne ba tare da sun tara masu dukiya ba.
Wani bangare da muka rasa mutanen kirki, shi ne yadda jami’an tsaro da alkalai da aka damka musu amanar kamawa da hukunta masu aikata barna, kuma wadanda su da shugabannin Allah Ya dora musu alhakin kare rayuka da dukiya da addini da hankali da nasabar mutane, amma sai ya zamo su ne suke lalata hankali da tsaro da shari’a domin su samu kazamar dukiya su ci karensu babu babbaka!
Don haka ina fata a yanzu da Shugaba Buhari ya kama zango na biyu na mulkinsa kuma zango na karshe zai kafa wani kwamiti mai karfin shari’a wanda zai kunshi mutane masu gaskiya da rikon amana irin su tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara, Mai shari’a Isa Ayo Salami da Malam Nuhu Ribadu, Shugaban Hukumar EFCC na farko da Janar Ishola Williams da sauransu su binciki kowa da kowa, daga kan masu yin dokoki zuwa masu zartarwa da masu shari’a da shugabanni da ma’aikatan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da su kansu hukumomin da suka hada da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da Fadar Shugaban Kasa da sauransu a zazzage kowannensu a tabbatar da abin da kowa ya mallaka a lokaci da kafin gwamnatin Shugaba Buhari, kudi da kadarori gida da waje. Duk wanda aka samu da dukiyar da ta fi karfin samunsa a kwace kuma a hukunta shi don ya zame darasi ga na baya.
Gyaran kasar nan na bukatar yin amfani da abubuwan nan hudu da na ambata a sama kuma babu wani daga waje da zai zo ya gyara mana, mu ne dai za mu tsaya mu yi aiki bilhakki da gaskiya mu gyara kasar nan.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA),
08060116666, 08023106666