Abubuwan al’ajabi da suka faru a ranar Kirsimeti a Legas

Ranar 25 ga watan Disemba rana ce da daukacin Kiristocin duniya ke gudanar da bukukuwa domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Yesu Almasihu, to amma kamar kowace shekara, wannan shekarar ma abubuwa na ban mamaki da al’ajabi sun  auku a sassa daban-daban na Jihar Legas.A ranar ne wani matashi mai suna Sodik Ojomo dan […]

Abubuwan al’ajabi da suka faru a ranar Kirsimeti a Legas
Abubuwan al’ajabi da suka faru a ranar Kirsimeti a Legas

Ranar 25 ga watan Disemba rana ce da daukacin Kiristocin duniya ke gudanar da bukukuwa domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Yesu Almasihu, to amma kamar kowace shekara, wannan shekarar ma abubuwa na ban mamaki da al’ajabi sun  auku a sassa daban-daban na Jihar Legas.
A ranar ne wani matashi mai suna Sodik Ojomo dan kimanin shekaru 23 a duniya ya mutu, yayin da yake ninkaya a cikin ruwan a yankin tsibirin bictoria Island.
Rahotannin sun nuna cewa Sodik wanda yake aiki da gidan abinci da ba a fadi sunansa ba saboda wasu dalilai ya shiga cikin ruwan ne bayan da aka gargade shi da kada ya shiga ciki.
Wadanda lamarin ya auku a kan idon su sun tabbatar da cewa jim kdan da shigar sa cikin ruwan sai ya nutse amma kafin a ceto shi ya riga ya mutu nan take.
Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Legas, Mista Rasak Fadipe ya tabbatar da mutuwar saurayin inda ya ce lamarin ya auku ne a gida mai lamba 3 zuwa 5 a kan titi Durosinmi Etti da ke bictoria Island.
A ranar ne matafiya da dama da suka je filin saukar jiragen saman Murtala Muhammed da ke Ikeja domin sayen tikitin tafiya garuruwan su suka samu tsaiko, saboda karancin jirage da kuma tsadar tikiti.
Binciken Aminiya ya gano cewa tikitin jirgin da ake  sayarwa Naira dubu 18 ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira dubu 30, wanda ake sayarwa dubu 30 ya tashi zuwa dubu 43.
Aminiya ta gano cewa tikitin jirgi daga Lagos zuwa Enugu da ake sayarwa dubu 20 ya tashi zuwa dubu 35. Tikitin Legas zuwa Abuja  da ake sayarwa dubu 24 ya tashi zuwa dubu 40 a ranar Kirsimeti.
Bincike ya nuna cewa matafiya da dama ba su samu damar tafiya ba a ranar.
Hakazalika fasinjojin da suke tashoshin mota a wuraren daban-daban na jihar su ma sun samu tsaiko, saboda karancin motoci da tsadar kudin mota a ranar Kirsimeti.
Tikitin motar bas daga Legas zuwa Kano da ake sayarwa dubu biyar ya tashi zuwa dubu shida ko bakwai.
Dadin-dadawa wata yarinya ’yar kimanin shekaru 17 da haihuwa mai suna Agnes ta mutu yayin da take wanka a tekun Legas, tare da wani saurayinta a ranar Kirsimeti.
Binciken Aminiya ya gano cewa Agnes ta bar gidansu da ke kan titin kirikiri a yankin Ajegunle zuwa tekun Legos, tare da saurayinta Emmanuel, amma ba ta dawo gida ba.
Saurayinta mai suna Emmanuel ya shaida wa manema labarai cewa, duk kokarin da suka yi na ceto Agnes ya ci tura, domin ruwan ya tafi da gawarta.
Daga bisani gobara ta kone gidaje a sassa da dama na jihar da suka hada da yankin Ejigbo da Ifako Ijaye.
Gobarar ta fara ne a wani gini mai hawa biyu da ke kan titin Modupeola da ke yankin Ejigbo da sanyin safiyar  Alhamis, amma ba a samu asarar rayuka ba.
Sai dai daraktan hukumar ’yan kwana-kwana na jihar, Rasak Fadipe ya ce daukin gaggawa da jami’an hukumar suka kai shi ne ya hana gobarar kai wa ga wasu gine-gine da ke makwabtaka da ginin da ya kama da wuta.
Shi kuwa jami’i a hukumar kai agaji ta NEMA na sashen Kudu maso Yamma, Mista Farinloye ya tabbatar da cewa iyalai 16 lamarin ya shafa.