Abubuwan da arewacin kasar nan ke bukata daga gwamnatin Buhari

Arewacin kasar nan yana tare da matsalloli masu yawa wadanda suka yi wa yankin katutu fiye da sauran yankunan Nijeriya. Kuma fatan samun kawar da wadanan matsaloli ne ma ya kara wa Janar Muhammadu Buhari farin jini. Domin kuwa shi ne kawai a yanzu zai iya kawar da matsalolin da Arewa ta samu kanta a […]

Abubuwan da arewacin kasar nan ke bukata daga gwamnatin Buhari
Abubuwan da arewacin kasar nan ke bukata daga gwamnatin Buhari

Arewacin kasar nan yana tare da matsalloli masu yawa wadanda suka yi wa yankin katutu fiye da sauran yankunan Nijeriya. Kuma fatan samun kawar da wadanan matsaloli ne ma ya kara wa Janar Muhammadu Buhari farin jini. Domin kuwa shi ne kawai a yanzu zai iya kawar da matsalolin da Arewa ta samu kanta a ciki. Ganin irin wannan kyakkyawan fata ya zama wajibi ga wannan gwamnati ta kawo wasu shirye- shiryen da za su sa wannan yanki na Arewa ya fita daga kangin da ya samu kansa a ciki. To, me ya kamata wannan Gwamnati ta yi domin ciyar da yankin nan na Arewa gaba?

Da farko dai abu mafi mahimanci da wannan gwamnati za ta tunkara shi ne tabarbarewar ilimin Arewa. Kowa ya san cewar daga dukan yankunan da muke da su a kasar nan, yankin Arewa shi ne mafi koma baya ta fuskar ilimin zamani. Saboda haka ya zama wajibi wannan gwamnati ta bullo da shirye-shirye masu karfi da za su ciyar da ilimi gaba a Arewacin kasar nan. A nan gwamnatin tararya ya kamata ta hada kai da gwamnatocin jihohi don tabbatar da cewa ilimi ya zama dole ga dukkan wani yaro a Arewa. Koda yake dai abu ne mai kamar wuya ganin yadda al’adunmu suka ginu, to amma wajibi ne a kawar da tsarin nan na almajirci. Gwamnati mai hangen nesa tana yin abin da ta ga ya dace ne koda kuwa mutane suna dari-dari da shi. Za a iya yin tsari mai kyau ta yadda yara za su rika karatun allo ba tare da sun je birane suna bara ba. Ko a yanzu ma mun ga yadda gwamnatin jihar Kano ta fara aiwatar da wani tsari na hana yara kanana gararanba da sunan karatun allo. Domin kuwa a yanzu haka gwamnatin Kano tana gina makarntu na kwana a kowacce karamar hukuma wandanda za su kula da karatun allo na iri wadannan yara. Kuma kwanan nan ma har gwamnati ta yi musu hukuma mai cin gashin kanta. Ka ga ke nan idan shirin ya kammala wannan tsohon tsari na karatun allo zai zama tarihi. Idan gwamnatin Buhari ta karfafa irin wannan tsari, to lallai zai kawo ci gaba a jihohin arewa.
Kuma ganinn yadd yanzu Janar Buhari ya zama wanda ya fi kowa tasiri a Arewacin Nijeriya, yana da kyau ya yi amfani da tasirinsa wajen yadda za a ja hankalin ‘yan boko da masu kudin Arewa da su kawo gudunmawa wajen ci gaban ilimi a wannan yanki.Musamman ma ta abin da ya shafi ilimi mai zurfi. A gaskiya an yi wa Arewa fintinkau ta wannan fanni. Domin idan muka dubi misalin jami’o’i masu zaman kansu da muke da su a kasar nan wadanda sun kai fiye da hamsin, guda biyu ne kawai muke da su a jihohi goma sha ukun da muke da su a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Abin mamaki jihar Ogun ita kadai, tana da jami’o’i hudu masu zaman kansu. Ban da jam’i’o’in gwamnati guda biyu. Ka ga k enan akwai sauran aiki a gaban Arewa. Kuma a nan dole ne muga laifin kungiyoyinmu na addini, musamman ma na Muslunci da suke a Arewa. Don abin bakin ciki ne a ce wai har yanzu kungiyar Izala ko ta Fiyanu ba wacce ta ke kokarin kafa jami’a. Ba kamar sauran kungiyoyin Kiristocin dake Kudu ba da suke da jami’oi da yawa.
Abu na biyu da Arewa za ta so gwamnatin Buhari ta kalla, shi ne aikin gona. Ganin yadda Arewa take da filin noma mai fadi. Sannan kuma ga yadda darajar man fetur take ta faduwa ya zama wajibi a kalli wannan harka ta gona. Alal misali ga yadda muke da dam dam a Arewa masu yawa, yana da kyau idan a bai wa noman rani babban muhimmanci.Da yawa daga cikin dam dam din da muke da su ba a amfani da su yadda ya kamata, Saboda haka zai yi kyau ga wannan gwamnati mai zuwa ta bullo da wani kakkarfan shiri da zai bunkasa yadda za a yi amfani da wadanan dam dam wajen noman rani.Mu dau misali da dam din Tiga dake jihar Kano. Kowa ya san irin gajiyar da ake ci a garuruwan da suka hadu suka kewaye Kadawa. Tsare- tsare irin na Kadawa ko ma wadanda suka fi Kadawa girma a jihohin Arewa ba shakka zai bunkasa wadannan jihohi. Bugu da kari gwamnati ta samar da wani yanayi ta yadda su manoman za su iya sayar da kayan noman nasu cikin daraja a cikin gida ko a kasashen waje. A nan za mu iya daukar wani tsari da Brazil ta yi amfani da shi wajen tabbatar da cewar manoma sun sayar da kayan nomansu cikin daraja ba tare da sun sha wahala ba ko kuma sun rasa masu saya ba.
Na tabbata, idan da tsari mai kyau, aikin gona kawai zai daukaka mutanen Arewa. Domin akwai kayan gona da yawa wadanda ma ba a ba su mahimmanci ba a Arewa.Amma kuma muna kashe kudi da yawa wajen shigo da su. Alal misali ana kashe kudi da yawa wajen shigo da dabino daga Nijar da Masar da Cadi da Murtaniya. Bayan kuma muna da kasar noma da yanayin da za mu rika yin dabino a jihohin Arewa, musamman a Jigawa da Kano da Borno da Yobe da Bauchi da Katsina da Sokoto da Zamfara.Wannan zai rage iri zaman kashe wando da matasan Arewa suke yi. Kuma wannan fa bayan sauran kayan gonar da za mu iya yi ne wato irin su auduga da gyada da dawa da masara da rogo da shinkafa da alkama da dai sauransu. Mu dauki alkama; kowa ya san alkama ce amfanin gona mafi mahimmanci wajen yin fulawa don yin biredi. To amma saboda wani dalili na gwamnatocin da suka wuce sai suka kawo wani shiri na amfani da rogo wai don yin biredi.Tunda an san dai alkama ita ce ake amfani da ita wajen yin fulawa to me zai sa ba za a bunkasa nomanta ba a jihoshin da suke da yanayi mai kyau da shuka alkama? Soboda haka irin wadannan shirye-shirye na noma da za su taimaka wa manoman Arewa ya kamata wannan gwamnati ta bai wa muhimmanci.
Sannan kuma ya zama wajibi ga wananna gwamnati mai zuwa ta duba matsalar rashin aikin yi. Wannan kuwa za a iya kau da shi ne ko rage shi ta hanyar farfado da masana’antun da suka durkushe a Arewa, ko kuma kakkafa wadansu sababbi. Wannan zai rage zaman kashe wando da matasan Arewa suke yi.Kuma tun da yake a halin da ake ciki yanzu mafi yawa da tattalin arzikin duniya ya ginu ne akan gudanarwar dai-daiku ko kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba, a nan gwamnati za ta iya shawo kan wadannan bangarori don su zo su kakkafa masana’antu a Arewacin kasar nan. Ga misali maimakon shigo da kaya da ake daga China, ina ganin gwamnati za ta iya shawo kan ‘yan China don su zo su kakkafa masanntun a Nijeriya kamar yadda suke yi a wasu lokuta a wasu kasashen Afirka. Koda a Kano ma ai muna da wata masana’anta ta yin leda mallaki’yan China wadda kuma ta samar da daruruwan guraben aikin yi ga mutanen Kano da ma wadanda ba ‘yan Kano ba. To, irin wannan tsari zai kawo ci gaba ta fannin masana’antu a Arewacin kasar nan.
Bugu da kari yana da kyau wannan gwamnati ta tabbatar da shirin nan na kafa tashar kawo kaya a Kano, wato wadda ba a bakin teku take ba, kuma a kira ta da ‘Dry port’. Wannan idan aka yi zai taimaka wajen samar da daruruwan aikin yi a Arewacin kasar nan. Wani abun kuma da yake da muhimmanci a yi masa kyakkyawan tsari shi ne na samar da muhalli. A gaskiya mafi yawa da manyan biranen da muke da su a Arewa kamar Kano da Kaduna ana fama da karancin muhalli. Mun san yadda wadannan birane a koda yaushe suke ta karuwa cikin sauri. To , ashe zai yi kyau a samar da wani yanayi da zai saukaka samun gidaje a wadannan birane. Mutane suna da yakinin cewar da shirin nan da gwamnatin Shagari ta bullo da shi na samar da gidaje ya ci gaba, to da yanzu matsalar gidaje a Nijeriya sai dai labari. Rashin gidaje ga mafi yawa na mutanen da suke a birane shi ne yake kara girman talaucin da suka samu kansu a ciki.
Abu na karshe da wannan gwamnati ya kamata ta yi shi ne fito da wani tsari da zai saukaka radadin da mutanen Arewa maso Gabas suke fama da shi na rikicin Boko Haram. A gaskiya mutanen wannan yanki sun galabaita, kuma gwamnatocinsu,musamman ma jihar Barno sun tagayyara. To ashe ya kamata wannan gwamnati mai zuwa ta kafa wata gidauniya da za ta farfado da wannan yanki.Wannan gidauniya za ta zama ba ta gwamnati ba. Amma gwamnati za ta sa hannu ta hanyar shawo kan daidaikun mutane da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na waje don su zo su zuba gudunmowarsu a wannan gidaunya. Wannan zai sa a sake gina wannan yanki ta hanyar samar da gidaje, makarantu, asibitoci da kuma kasuwanni. Wanan zai taimaka wajen rage wahalhalun da wannan rikici ya janyo a wannan yanki .
In dai har gwamnatin Janar Buhari ta yi wadannan shirye -shirye a Arewacin kasar nan, to na tabbata mafi yawan matsalolin da Arewar take fama da su za su ragu in ma ba su kau ba. Kuma wannan ba shakka zai share wa talakawan Arewa hawayen da suka dade suna zubarwa. Wanda kuma dalilin hakan ne ya ba su kwarin gwiwar jajircewa don ganin cewar Janar Buhari ya karbi mulkin wannan kasar.
Yunus Ahmed Kabo, Kabo Ward,Kano State.
+2348022180636