Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa
Ya kamata mai azumi ya lazumci wadannan abubuwa domin samun dacewa.
Shahararren malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta.
A yayin da al’ummar Musulmi suka dauki azumin Ramadan, Sheikh Daurawa ya ce akwai tarin lada ga duk wanda yake yin wadannan abubuwan, kamar yadda ya bayyana wa Sashen Hausa na BBC:
- Ramadana: Tsohon Gwamna ya raba abincin biliyan N1.4 a Zamfara
- Kar a manta da talakawa a lokacin Azumi — Buhari
- Azumin: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncen azumi, ya kuma kiyaye su.
- Sallah: Musamman Sallar Taraweeh da Tahajjud da yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin farilla.
- Ciyarwa: Tana da muhimmanci ko da dabino ko ruwan sanyi ne. “Domin Annabi (SAW) ya ce, duk wanda ya ciyar da mai azumi, za a kara masa [lada] kamar ya yi wani azumin ne” inji Sheikh Daurawa.
- Umrah: Ya kara da cewa idan mutum yana da hali ana so ya yi Umrah a watan Ramadan, idan kuma babu hali, sai ya ciyar.
- I’tikafi: Ya kara da cewa, “Ana so mutum ya mayar da hankali wajen shiga I’tikafi idan yana da hali.”
- Daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan alheri.
- Yafiya: Ya shawarci Musulmi da su yafe wa juna, saboda gabarar Allah ake nema a cikin watan.
- Karatun Al-Kur’ani: A dage tare da yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi.
- Addu’a: Mutum ya himmatu wajen yin addu’o’i, “Domin lokacin Sahur da lokacin bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin, ana amsa addu’a.”
- Zumunci: Domin sada zumunta a watan azumi tana kara arziki da zaman lafiya, kamar yadda ya bayyana.
- Tausayi: Azumi zai koya wa mai yin sa tausayi da taimako idan ya ga masu bukata, saboda ya riga ya koya a watan Azumi.