Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa
Ya kamata mai azumi ya lazumci wadannan abubuwa domin samun dacewa.
Shahararren malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta.
A yayin da al’ummar Musulmi suka dauki azumin Ramadan, Sheikh Daurawa ya ce akwai tarin lada ga duk wanda yake yin wadannan abubuwan:
Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncen azumi, ya kuma kiyaye su.
Sallah: Musamman Sallar Taraweeh da Tahajjud da yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin farilla.
Ciyarwa: Tana da muhimmanci ko da dabino ko ruwan sanyi ne. “Domin Annabi (SAW) ya ce, duk wanda ya ciyar da mai azumi, za a kara masa [lada] kamar ya yi wani azumin ne” inji Sheikh Daurawa.
Umrah: Ya kara da cewa idan mutum yana da hali ana so ya yi Umrah a watan Ramadan, idan kuma babu hali, sai ya ciyar.
I’tikafi: Ya kara da cewa, “Ana so mutum ya mayar da hankali wajen shiga I’tikafi idan yana da hali.”
Daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan alheri.
Yafiya: Ya shawarci Musulmi da su yafe wa juna, saboda gabarar Allah ake nema a cikin watan.
Karatun Al-Kur’ani: A dage tare da yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi.
Addu’a: Mutum ya himmatu wajen yin addu’o’i, “Domin lokacin Sahur da lokacin bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin, ana amsa addu’a.”
Zumunci: Domin sada zumunta a watan azumi tana kara arziki da zaman lafiya, kamar yadda ya bayyana.
Tausayi: Azumi zai koya wa mai yin sa tausayi da taimako idan ya ga masu bukata, saboda ya riga ya koya a watan Azumi.