Abubuwan da ba a sani ba game da Maina

Tsohon shugaban kwamiti yi wa fansho garambawul (PRTT), Alhaji Abdulrasheed Maina, wanda kwana nan  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki bayan an dawo da shi kuma an masa karin girma zuwa matsayin darakta a ma’aikatar harkokin cikin gida, ya kasance cikin komar EFCC da dadewa duk da cewa ya taba cewa an wankeshi. […]

Abubuwan da ba a sani ba game da Maina

Tsohon shugaban kwamiti yi wa fansho garambawul (PRTT), Alhaji Abdulrasheed Maina, wanda kwana nan  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki bayan an dawo da shi kuma an masa karin girma zuwa matsayin darakta a ma’aikatar harkokin cikin gida, ya kasance cikin komar EFCC da dadewa duk da cewa ya taba cewa an wankeshi.

Tun bayan da aka samu labarin cewa an dawo da shi bakin aiki ake ta cece-kuce, wanda hakan ya sa wadansu ke tambaya wai waye Maina.

Hakan ya sa Aminiya ta rairayo takaitaccen bayani game da shi, musamman ga wadanda ba so sani ba.

1.   1. A shekarar 2011, an nada Maina ya zama shugaban kwamitin yi wa fansho garambawul, domin ya gyara yadd ake tafiyar da fanshon kasar.

2.   2. A ‘yan watanni da fara aikin Maina, sai ‘yan fansho karkashin kungiyar ‘yan fanshon ma’aikatun Gwamnatin Tarayya suka fara zanga-zangar lumana, inda suka bukaci a dakatar da ayyukan kwamitin fanshon karkashin shugabancin Maina.

3.   3. A watan Fabrailun 2013, tsohon shugana kasa Goodluck Jonathan ya ba shugaban ma’aikata na wancan lokaci, Alhaji Isa Sali umarni da ya bincika yadda Maina ya daina aiki. Wannan ya sa Maina ya bace bat, har rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar cewa tana nemansa ruwa-a-jalli saboda zargin almundahanan kudin fansho na Naira biliyan 195.

4.   4. A watan Maris, sai Maina ya kai kara kotu, inda ya bukaci a ba shi kudi Naira biliyan 1.5 saboda an bata masa suna.

5.   5. Sai kuma a shekarar 2016, Maina ya kai kara kutu, inda ya bukaci ta dakatar da hukumar EFFC a kan nemansa da hukumar ke yi ruwa-a-jallo, wanda kotun ta yi.

6.   6. Sai kuma ya sake komawa kotu, inda ya bukaci a mayar da shi aiki domin an koreshi ne ba bisa ka’ida ba, inda ya lissafa shugaban ma’aikata, ministan shara’a da ministan harkokin cikin gida a matsayin wadanda yake kara.

7.   7. A watan Yuni, sai Maina ya bada sanarwar cewa Majalisar Dattijai ta wankeshi a kan zargin da ake masa. Sannan y ace majalisar ta gano cewa kudin da ake zarginsa das hi yana aljahun gwamnati. Sai ya bukaci gwamnatin da majalisar das u nemi afuwarsa.

8.   8. A ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba, kwatsam sai aka samun labarin cewa an dawo da Maina bakin aiki, kuma an masa karin girma zuwa matsayin darakta. An yi wanna lamarin ne cikin sirri, amma sai kafar yada labarai na Premium Times suka bankado lamarin.

9.   9. Bayan kwana uku, sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa ya salami Maina, sannan kuma ya bukaci a bincika masa yadda aka yi har Maina ya dawo bakin aiki.

10.10. Lamarin dai har yanzu na ci gaba da jan hankalin al’umma. Musamman ganin yadda lamarin ke daukan sabon salo, ta yadda ake ta zarge-zarge da neman asalin mai laifi.