Abubuwan da ke kassara fina-finan Hausa — Babba Sanda
Masu tace finafinan su lura da addini da al’adun da muke da su.
Alhaji Auwalu Babba Sanda, tsohon ɗan wasan kwaikwayo ne tun lokacin ana wasan daɓe, kafin ya zama ɗaya daga cikin masu harkar fim.
A tattaunawarsa da Aminiya, ya yi tsokaci a kan finafinan Hausa a yanzu da masu shirya su da jarumansu, musamman yadda suke sa baƙin al’adu a finafinan da sanya suturun Turawa, maimakon su riƙa sa tufafi na Hausawa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Wane tsokaci za ka yi a kan Masana’antar Kannywood da masu shiryawa da yin finafinan da ake suka da yin amfani da baƙin al’adun da suka saɓa da na Hausawa ko al’ummar Arewa?
Gaba ɗaya ba zai iya yiwuwa a ce harkar fim ta tafi a haka ba.
Ko me ya sa?
Saboda addini ya daɗe yana tasiri a kan al’amuran rayuwar Bahaushe.
Kamar yaya, ba mu misali?
Misali, a al’adar Bahaushe idan maigida yana barci, idan za a tashe shi, sashen jikinsa matarsa za ta taɓa, kamar ƙafa ta ce maigida.
Sai maigida ya tashi ko kuma idan ya dawo daga tafiya, ba yadda za a yi matarsa ta rungume shi a gaban wasu don ta yi masa barka da zuwa.
Bahaushe ba zai iya yin wannan ba kamar yadda ake nunawa a fim ɗin Hausa.
Domin haka za a ce wannan ya ci karo da addini ko al’ada, duk da cewa al’ada ce ta hana hakan.
Wannan ya sa ake kushe irin wannan yanayi a fim da Hausawa suke yi, ake ganin baƙuwar al’ada ce.
Kana nufin raye-raye da waƙenwaƙen da ake yi ba irin al’adar Bahaushe ba ne?
Haka ne. Mutane da dama suna ganin raye-raye da waƙe-waƙen da ake yi a cikin fim a matsayin baƙuwar al’ada ce, domin Bahaushe ba ya yin haka.
Idan na fahimce ka, wato hakan ya saɓa wa ɗabi’a da al’adar Bahaushe ko mutumin Arewa?
Ƙwarai kuwa, domin wannan wata baƙuwar al’ada ce aka shigo da ita.
Hatta irin suturun da masu fim suke sanyawa akasari ba na al’adar Bahaushe ba ne.
Ya dace ma a ce su sanya hula haɓar kada, kamar yadda iyaye da kakanninsu suka sanya a baya.
To amma sun zubar da al’adarsu, sun ɗauko ta aro, sai ka ga jarumin fim ya sanya hular kaboyi irin ta Amurkawa, ko Hana-Sallah ko ya tsuke da zanzaro yana tiƙar rawa da budurwa.
Wato dai a ganinka akwai buƙatar gyara ke nan?
Eh, idan da so samu ne, Hukumar Tace Finafinai ta gane cewa, idan aka yi wani abu wanda ya dace da al’adar
Bahaushe, to ta bar shi a fim, tunda ai al’adarsu suka nuna ta gaskiya.
Ba a riƙa nuna mutane wancan ya zo ya rungume matarsa, a nuna wa jama’a ba. Wannan ba al’adar Bahaushe ba ne.
Akwai buƙatar a riƙa finafinan da ’ya’yanmu za su taso da tsantsar harshensu da al’adunsu.
Amma yanzu idan aka fassara fim ɗin Indiya da Hausa, sai ka ji ana cewa suburbuɗa.
Wannan baƙuwar kalma ce wacce aka samar da ita, kuma tana watsuwa, mu kuma akwai kalmomin da muke rasawa waɗanda ’ya’yanmu ba za su san su ba.
Misali na taɓa ce wa ɗana je ka, ka zaro min zabori, amma ya kasa gane me ake nufi.
Sai da na gaya masa tsintsiya, idan an ɗaure ta tsintsiya ce, amma idan an zaro ɗaya daga ciki ta zama zabori.
Duka irin waɗannan tsofaffin kalmomin ya kamata masu rubuta finafinan Hausa su karanta littattafai, su riƙa shigar da su a finafinan Hausa.
Amma yanzu an zo an daina, maimakon shigar da kalmomin sai a riƙa ƙirƙiro na ruɗani, ana zamanantar da su.
Takamaimai ina shawararka ta dosa ga masu shirya finafinan Hausa?
Ni shawarata ba su ne kaɗai suke da laifi ba, waɗanda suka fi laifi su ne waɗanda suke tace finafinan.
Ba su tace fim a kan al’adar Bahaushe, ba suna tace fim ne a kan addinin da Bahauahe yake kai ba.
Su kuma masu yin fim kamar Ibo, kamar Turawa kamar mutanen China wato Sin da Indiya ai suna finafinansu ne a kan al’adaunsu da suka taso da su.
Don haka su masu tace finafinai su samo wata doka da idan an yi fim kada ya saɓa addininsu, ya zama a al’adance.
Su kuma masu yin fim su tsarkake zukatansu cewa idan sun yi wannan abin ba suna nufin fasiƙanci ba ne ko neman kuɗi kawai, a’a za su kiyaye addini da al’adar mutanen da suke wakilta.
Wato gyaran ya zama fuskoki biyu ke nan, wato farko masu tace finafinan da kuma masu yin sa?
A tsarkake zuciya, ya zamana yin waɗannan abubuwa ba yana nufin yin wani abu na son zuciya ba.
Su kuma masu tace finafinan su lura da addini da al’adun da muke da su.
Sannan su canja yanayin shigar su masu fitowa a finafinan don su dace da addini da al’adunmu.