Abubuwan da ke kawo tsinkewar gashi da yadda za a magancesu
Akwai abubuwa da dama da ke janyo karyewa ko tsinkewar gashi wadanda da yawa daga cikinmu ba su sansu ba. Gashi yana daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mace kyau. Kun ga ko dole ne mu lura da gashin kanmu sosai. Yau mun kawo muku abubuwan da suke janyo tsinkewar gashi domin a […]
Akwai abubuwa da dama da ke janyo karyewa ko tsinkewar gashi wadanda da yawa daga cikinmu ba su sansu ba. Gashi yana daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mace kyau. Kun ga ko dole ne mu lura da gashin kanmu sosai. Yau mun kawo muku abubuwan da suke janyo tsinkewar gashi domin a kiyaye da kuma yadda za a magance wannan matsala.
• Rashin sanya dankwali na janyo karyewar gashi saboda idan rana ta haska gashin da yawa, hakan na sanya fatar kai ta zama mara karfi sai ta fara zubar da gashi.
• Yawan amfani da na’uran ‘dryer’ domin busar da gashi na bata gashi.
• Damuwa da yawan tunani na janyo tsinkewar gashi.
• Rashin cin abinci mai dauke da sinadaran bitamin da protein da rashin cin mai, mai inganci kamar zaitun na janyo tsinkewar gashi.
• Masu dauke da juna biyu na yawan samun tsinkewar gashi saboda canji da jikinsu ya yi.
• Amfani da magunguna masu karfi saboda kyankyami da sauransu na janyo tsinkewar gashi, haka ma yawan sanya man gashi a kai-a kai kamar ‘relader’ na janyo tsinkewar gashi. Ana so ana amfani da man ‘relader’ bayan wata uku-uku.
• Barin gashi ya yi datti sosai na janyo amosanin ka da kuma karyewar gashi.
Yadda za a magance wannan matsala
• Domin samun gashi mai lafiya da fatar kai mai karfi, a dage da shafa man gashi a kai kamar man kwakwa da na zaitun da sauransu.
• Domin rage furfurar gashi, yana da kyau a rika shafa lalle a gashi bayan awa daya sai a wanke.
• Idan ana so a rabu da amosanin ka, sai a samu kwallon mangoro bayan an busar da shi sai a rika hadawa da man gashi, kafin a shafa a fatar kai.
• Yana da kyau ana wanke gashi da ruwan dumi, a wankewar karshe a yi amfani da ruwan sanyi. Ruwan sanyi na kara karfin jijiyoyin da ke rike da gashi.
• A dage da cin abinci mai dauke da sinadaran ‘iron’ da ‘zinc’ da B ‘compled’ da ‘bitamin C’ domin samun gashi mai santsi, mai lafiya.
• Amfani da kwaiduwar kwai da nono a gashi na sanya laushin gashi.
• A hada lalle da bakin ‘coffee’ a shafa a kai a wanke bayan awa daya na rage furfurar gashi.