Abubuwan da suka faru bayan kwana 750 da soma yaƙin Rasha da Ukraine

Wasu alkaluma sun tabbatar da cewa yakin ya shafi wani bangare na tattalin arzikin duniya.

Abubuwan da suka faru bayan kwana 750 da soma yaƙin Rasha da Ukraine

Yayin da yaƙin Rasha da Ukraine ya shiga rana ta 750, Aminiya ta rairayo waɗansu manyan abubuwan da suka faru.

Ga halin da ake ciki dangane da yakin da wasu alkaluma suka tabbatar da cewa ya shafi wani bangare na tattalin arzikin duniya.

Faɗa

  • Aƙalla mutane 3 ne suka mutu, 38 kuma suka jikkata, 10 daga cikinsu ƙananan yara ne, bayan da wani makami mai linzami na Rasha ya afkawa wasu gidaje biyu a birnin Kryvyi Rih na tsakiyar ƙasar Ukraine.
  • Ƙungiyoyin mayaƙan sa kai na Rasha masu goyon bayan Ukraine masu adawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin sun ce, sun kai hare-hare daga Ukraine zuwa yankunan Kursk da Belgorod na Rasha. Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce, ta daƙile hare-hare bakwai kuma an kashe wasu mayaƙa 234.
  • Moscow ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine guda 25 a yankuna takwas da ke wani bangare na harin da aka kai kan cibiyoyin makamashi ciki har da matatar mai ta biyu mafi girma a Rasha.
  • Rasha ta yi iƙirarin cewa ta karɓe ikon ƙauyen Nevelske da ke yankin gabashin Donetsk na Ukraine. Babban ma’aikatan Ukraine sun ce an daƙile hare-haren Rasha a yankin.
  • Hukumar leƙen asiri ta SVU ta Ukraine ta ce, ta gano wasu mambobi 15 na wata hanyar sadarwa da ta yi zargin cewa suna da hannu a cikin samo bayanan sirri, masu goyon bayan Rasha. Hukumar SBU ta ce, ta tsare huɗu daga cikinsu, ciki har da wani limamin Cocin Orthodox na Ukraine (UOC) mai alaƙa da Moscow. SBU ta ce cibiyar sadarwar tana da alaƙa da Hukumar Tsaro ta Tarayya ta Rasha (FSB).

Ɓangaren Siyasa da diflomasiya

  • FiraiMinistan Poland, Donald Tusk ya ziyarci Amurka inda ya buƙaci Kakakin Majalisar Wakilai na Republican, Mike Johnson da ya gaggauta zartar da wani ƙudirin doka da zai bai wa Ukraine dalar Amurka biliyan 60 a sabon taimakon soja. Tusk ya ce, gazawar Johnson na ɗaukar matakin zai janyo asarar “dubban rayuka”.
  • Buƙatar Tusk ya zo ne a daidai lokacin da ’yan jam’iyyar Democrat da mambobin ’yan jam’iyyar Republican masu tsattsauran ra’ayi suka ƙaddamar da wani yunƙuri na dogon lokaci don tilasta jefa ƙuri’a kan tarin taimakon, wanda aka dakatar da shi tsawon watanni a cikin adawa daga masu ra’ayin mazan jiya.
  • ’Yan majalisar dokokin Faransa sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da yarjejeniyar tsaron Ukraine na tsawon shekaru 10 wanda ya haɗa da alƙawarin aika da kuɗin da ya kai Euro biliyan 3 ($3.2bn) na taimakon soji zuwa Kyiv a shekarar 2024.
  • Dubban mutane ne suka fito kan titunan Bratislaɓa babban birnin ƙasar Sloɓakia domin nuna adawa da gwamnati da kuma nuna goyon bayansu ga Ukraine. Tun lokacin da ya hau kan karagar mulki a watan Oktoban da ya gabata, gwamnatin Firayi Ministan Ƙasar Robert Fico ta soki taimakon sojan da Turai ke baiwa Ukraine tare da matsa ƙaimi wajen sabunta alaƙa da Rasha.

Makamai

  • Fadar White House ta sanar da cewa za ta iya aika sabon taimakon soja zuwa Ukraine wanda darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 300 bayan “ba tare da sun yi tsammani ba” daga ajiyar kuɗin na kwangilolin Pentagon. Za a yi amfani da kuɗaɗen don alburusai na bindigogi da makamai masu linzamai High Mobility Artillery Rocket Systems (HIMARS).
  • Shugaban sojojin Ukraine Oleksandr Syrskyi da Ministan Tsaro Rustem Umerov sun tattauna ta wayar tarho da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin kan isar da makamai. Syrskyi ya ce harsashi da kayan kariya ta sama su ne manyan abubuwan da suka sa a gaba.
  • Ma’aikatar tsaron Denmark ta ce za ta samar da wani sabon tarin taimakon soji da suka haɗa da na’urorin sarrafa harsasai da harsashi ga Ukraine da darajarsu ta kai kimanin kuɗin Denmark Danish biliyan 2.3 (kwatankwacin dalar Amurka miliyan $336.6m).
  • Da alama ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai suna shirin cimma matsaya kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Turai, da buɗe wani asusun taimakon soji ga Ukraine  a ranar Laraba.

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe