Labaran da suka girgiza duniya a 2023

Ga wasu muhimman abubuwan da duniya ba za taba mantawa da su ba, da suka faru a shekarar 2023 da ke bankwana

Labaran da suka girgiza duniya a 2023

Ma’aikacin ceto a girgizar kasar Turkiyya

A yayin da jin 2023 ke karewa a yau, ga wasu daga cikin labaran da duniya ba za taba mantawa da su ba, da suka faru a shekarar.

Girgizar Kasar Turkiyya:

A watan Fabrairu aka yi girgizar kasa mafi muni a kasar Turkiyya da wani yanki na Syria, wanda ya yi ajalin sama da mutum 59,250, wasu 107,204 suka ji rauni.

Mutum miliyan 15.73 ne suka rasa muhallansu, wasu 297 suka bace a sakamakon iftila’in a 11 daga cikin larduna 17 da ke kasar Turkiyya.

Gidaje sama da 345,000 ne aka tabbatar sun lalace a sakamakon girgizar kasar, wadda ta farko ke da karfin maki 7.8, kuma ita ce mafi karfi a shekaru 84.

Bayan sa’o’i tara kuma aka sake wata mai karfin maiki 7.5.

Yakin Sudan:

A tsakiyar watan Ramadan, yaki ya barke a Khartoum, babban birnin kasar Sudan tsakakin sojojin gwamnati da Rundunar sa kai ta RSF, wanda mataimkain shugaban kasar ke jagoranta.

Yakin wanda aka fara bagatatan ya barke ne jim kadan bayan wani zama da bangarorin suka yi.

Rikicin shugabancin kasar Sudan tsakanin bangarorin biyu, ya jefa al’ummar kasar cikin tashin hankali, inda cikin dan kankanin lokacin aka rika fasa bankuna ana kwasar ganima.

’Yan kasashen waje, ciki har da dalibai da ke karatu a Sudan da kyar suka samu damar ficewa daga kasar.

Bikin Nadin Sarki Charles III

A ranar 6 ga watan Mayu aka yi bikin nadin Charles III a masayin Sarkin Ingila.

An yi bikin na nadin Sarki Charles III be bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth, wadda ta rasu ranar 8 ga Satumba,  2022 tana da shekaru 96.

Baki daga sassan duniya sun halarci gagarumin bikin da aka gudanar, aka kuma yada kai-tsaye a talabijin, inda a Birtaniya kadai mutum miliyan 20.4 suka kalli bikin kai-tsaye.

Hakan ya sa bikin ya zama shirin talabijin na kai-tsaye da aka fi kallo a Birtaniya a 2023.

Ambaliyar Libya:

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya da ta shanye sassan Gabashin kasar Libya a ranar 9 ga wayan Sayumba.

Bayan kwanaki biyu kuma wasu katafarun madatsan ruwa a yankin suka fashe.

Ruwansu ya shanye rubu’in birnin Derna, musamman a yankunan Bayda, Marawah, Jabal al Akhdar, da Al Abraq.

Ofishin Agaji na Majalisar Dinkin Duniya (UNOCHA) ya tabbatar da mutuwar mutane 4,352, wasu sama da 8,000 suka bace da ake zargin teku ne ya wuce da su.

Mutane 44,862 aka tabbatar sun rasa muhallansu a sakamkon lalatacewar gine-gine kimanin 10,000 a ambaliyar.

Juyin Mulkin Nijar

A watan Yuli sojojin Jamhuriyar Nijar suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum, suka ayyana Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin shugaban mulkin soji.

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin na Nijar, amma wasu ’yan kasar sun yi na’am da shi, musamman saboda yadda sojojin suka bukaci sojojin Faransa sun bar kasar.

Sojojin sun zargin Bazoum da zama karen farautan Faransa, rashin magance matsalar tsaro, da durkushewar tattalin arzikin kasar.

Kungiyar ECOWAS ta bukaci sojojin su koma bariki su dawo da Bazoum kan kujerarsa, amma hakan bai yiwu ba.

Duk da tattaunawar da bangarorin suka yi, da ma takunkuman da ECOWAS da sauran kasashe suka ƙaƙaba wa Nijar, sojojin sun ki ba da kai bori ya hau.

Daga cikin takunkuman har da yanke wutar da kasar take samu daga Najeriya, rufe iyakokin Nijar da kasashen ECOWAS da kume janye tallafin da Faransa da Amurka da sauransu suke ba wa Nijar.

Amma duk da haka, har yanzu Janar Tchiani ne ke kan mulki, kuma sojojin ci gaba da tsare Bazoum da ake neman su saki.

Sannan sauran kasashen Yammacin Afirka (Guinea, Burkina Faso da Mali) da sojoji suka yi juyin mulki a sun bayyana goyon baya ga gwamnatin sojojin Nijar kan shirin ECOWAS na daukar matakin soji a kansu.

Juyin Mulkin Gabon:

A daidai lokacin da ake neman dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar ne kuma sojojin kasar Gabon suka kifar da shugaba Ali Bongo a ranar 30 ga watan Agusta, jim kadan bayan an sanar da shi a matsayin wanda ya lashe shugaban kasar inda ya yi tazarce  domin fara wa’adinsa na uku.

Juyin mulkin da Janar Brice Oligui Nguema ya jagoranta ke da wuya sojojin suka soke zaben mai cike da Ali Bongo ya lashe, suka ce ba shi da sahihanci.

A halin da ake ciki dai Ali Bongo, wanda ya mulki kasar tun daga 2009, yana tsare a hannun sojojin tare da iyalinsa.

Ali Bongo ya zama shugaban kasar Gabon ne bayan rasuwar mahaifinsa da Omar Bongo Odimba, wanda ya mulki kasar na shekaru 42.

Al’ummar kasar dai sun yi na’am da juyin mulkin, sai dai wasu na ganin juyin mulkin taimake ci gaban daukar Bongo ce, saboda dangantakar Janar Brice da Ali Bongo.

A kwanakin farko na juyin mulkin sojojin sun bukaci kafofin yada labaran Faransa su bar Gabon, ko da yake daga bisani sun ba su izinin dawowa su ci gaba aiki a kasar.

Girgizar Kasar Moroko:

Girigizar kasa mafi muni a shekaru 120 a kasar Moroko ta auku a daren Juma’a 8 ga Satumba.

Girgizar kasar ta shafi mutane 380,000 zuwa miliyan 2.8, sannan 500,000 suka rasa muhallansu.

Akalla muum 2,800 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sai wasu 2,562 da suka gamu da munanan raunuka.

Gidaje 59,000 sun lalace, wasu 19,000 kuma suka tashi aiki gaba daya a sakamkon iftila’in.

Harin Hamas:

A ranar 7 ga Oktoba kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kai hari a Isra’ila, inda ta kashe mutane kimanin 2,000 ta sace wasu kimanin 200.

A sakamakon haka Isra’ila ta kaddamar da hari mafi muni a shekara 70 a Zirin Gaza.

Kawo yanzu sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa sama da 21,000, akasarinsu kananan yara da mata da kuma tsofaffi.

Duk da la’anta da Isra’ila ke sha daga kasashen duniya, manyan kasahen duniya kawayenta irinsu Amurka da Faransa da sauransu suna goyon bayanta.

A wani lokaci ma Amurka ta hau kujeran-na-ki a majalisar dinkin duniya kan tsagaita wuta a Gaza.

Kawo yanzu Falasdinawa sun rasa kusa daukacin muhallansu a yayin da ake kokarin sulhu tsakanin bangarorin.