Abubuwan da suka kamata a sani kan cutar Diphtheria da take yaduwa a Najeriya

Cutar ta diphtheria na yaduwa a tsakanin mutane cikin sauki.

Abubuwan da suka kamata a sani kan cutar Diphtheria da take yaduwa a Najeriya

Cutar sarke numfashi ta Diptheria ta barke a Jihar Yobe, inda ta kashe yara 30 sannan wasu 42 suna can a kwance a Asibitin Kwararru na Potiskum da ke jihar.

Daga cikin yankunan da cutar ta fi mamaya akwai Tandari, Misau Road, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Igwanda da Tezako, kamar yadda Aminiya ta gano.

Wakilinmu ya gano cewa, sama da yara 20 ne suka rasu a gidajensu, wasu hudu suna kwance a asibiti.

Daya daga cikin mahaifan yaran da suka kamu mai suna Abdullahi Muhammad ya ce, yara da dama sun mutu a gida kafin ma a kai su asibiti.

“Muna kira ga gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen ceto rayuwar yaran namu.

“Alamun cutar sun hada da zazzabi da tari da kuma raunin jiki,” in ji shi.

Wani dan jarida mazaunin Potiskum, Ibrahim El-Tafsir ya shaida wa Aminiya cewa, “Kodayake jami’an gwamnati sun ki fada mana yawan mutanen da suka rasu, amma akwai gidaje biyu da yara hudu suka mutu, kuma har yanzu muna ci gaba da binne wasu.”

Da wakilinmu ya tuntubi jami’in kula da riga-kafi na Karamar Hukumar Potiskum, Malam Buba, ya musanta yawan yaran da ake cewa sun rasu, amma ya amince cewa wadanda aka kwantar a asibiti sun kai 42.

Ya koka cewa, galibin yaran da suka rasu a gida suka rasu, ba a asibiti ba, inda ya ce iyaye ba sa kai su a kan lokacin da ya kamata.

Shi ma Daraktan Sashen Kula da Lafiya a Matakin Farko na Potiskum, Abdulrahman Musa ya ce, bisa ga rahotannin da suka tattara, suna ci gaba da wayar da kan mutane kan illar cutar.

A kwanakin baya ne Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da barkewar cutar a kasar nan, inda ta ce akalla mutum 80 ne suka rasu.

A sanarwar da NCDC ta bayar, zuwa ranar 30 ga Yuni mutum 798 ne suka kamu da cutar.

Sanarwar ta ce bayan barkewar cutar a watan Disamban 2022, ta samu rahoton bullar cutar a wasu jihohi da ke fadin kasar nan.

“Zuwa 30 watan Yuni 2023 an tabbatar da mutum 798 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 a jihohi takwas ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja,’’ in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, Jihar Kano ita ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar da mutum 782, sai jihohin Legas da Yobe da Katsina da Kuros Riba da Kaduna da kuma Osun da aka samu barkewar cutar.

Kuma kashi 71.7 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar yara ne ’yan shekara biyu zuwa 14.

Cutar sarkewar numfashin dai cuta ce da kwayoyin cutar bakteriya mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta. Wacce ke shafar hanci da makogwaro wani lokacin da fatar mutum.

Ta fi kama yara kananan da manyan mutane, musamman wadanda ba su yi allurar riga-kafin cutar ba.

Alamomin Diphtheria

Hukumar NCDC ta ce alamomin diphtheria sun hada da: zazzabi da yoyon hanci da bushewar makogwaro da tari da sa idanu su zama ja da kuma kumburin wuya.

Wani lokaci idan lamarin ya tsananta, gefen makogwaro kan kumbura, inda mai lalurar zai rika wahalar numfashi.

Adetifa ya ce, NCDC na aiki tare da ma’aikatun lafiya na jihohi da sauransu wajen fadada yaki da cutar.

Masu fuskantar hadarin kamuwa da cutar Shugaban Hukyamr NCDC ya lissafo wadanda suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar da suka hada da:

• Yara da manyan da ba su yi riga-kafin kamuwa da diphtheria ba.

• Mutanen da ke zaune a wuri mai cinkoso.

• Mutanen da ke zama a muhalli marar tsabta.

•Ma’aikatan kiwon lafiya da ke aikin kula da mutanen da suka kamu, ko ake zargin suna dauke da cutar.

Yaduwarta

Hukumar NCDC ta ce bakuwar cutar ta diphtheria na yaduwa a tsakanin mutane cikin sauki, ta hanyar mu’amala da mai dauke da ita ko feshi daga tari ko atishawar mai dauke da cutar da kuma tu’ammali da tufafi da abubuwa masu dauda.

Hukumar ta shawarci iyaye su tabbatar an yi wa ’ya’yansu riga-kafin cutar kamar yadda yake a tsarin yi wa yara riga-kafi.

Ta kuma shawarci duk wanda ya ga alamar cutar a tare da shi ya killace kansa sannan ya sanar da mahukunta mafi kusa ko ma’aikatan NCDC ko wata cibiya mai alaka da kiwon lafiya.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja