Abubuwan da ya kamata ka sani kan wasan hamayya na El Clásico

A halin yanzu, Barcelona take saman teburin gasar da maki 27 yayin da Real Madrid take biye da ita da maki 24.

Abubuwan da ya kamata ka sani kan wasan hamayya na El Clásico

A yau Asabar da misalin ƙarfe 8 na yamma, za a buga wasan hamayya na El Clásico inda Real Madrid za ta kece raini da Barcelona a filin wasa na Santiago Bernabéu da ke birnin Madrid – babban birnin Spain.

A halin yanzu, Barcelona take saman teburin gasar da maki 27 yayin da Real Madrid take biye da ita da maki 24.

Ana sa rai wasan na mako 11 a gasar LaLiga ta bana zai zama wata ɗamba ga Real Madrid wajen ƙwace kambun da Barcelona take riƙe da shi na buga mafi yawan wasannin LaLiga 43 a jere ba tare da an yi galaba a kanta ba – ko akasin haka.

A halin yanzu dai Madrid ɗin ta buga wasannin LaLiga har 42 a jere ba tare da an doke ta ba.

Rashin nasara na ƙarshe da Madrid ɗin ta yi shi ne wasan hamayyar birnin Madrid a fafatawarta da Atletico Madrid, a Satumbar bara a wasan da aka buga a gidan Atletico Madrid – inda mai masauƙin baƙin ta lallasa ta da ci 3 – 1.

Kundin tarihi ya nuna rabon da Real ɗin ta buga wasannin LaLiga masu yawa ba tare da an doke ta ba, shi ne wasanni 38 a jere da ta buga a kakar 1979-1980.

A ɗaya gefen kuma, rashin nasara na ƙarshe da Real ta yi a gida shi ne wasan da kulob ɗin Villareal ta lallasa Madrid ɗin da ci 3 da 2 a ranar 8 ga watan Afrilun 2023.

Masu kallon El Clasico

A cewar shugaban hukumar gasar LaLiga Jaɓier Tebas ana samun masu kallon wasan na El Clasico a fiye da ƙasashe 180 ta akwatunan talabijin inda wasannin El Clasico na baya-bayan nan aka samu ƙaruwar masu kallo da fiye da mutum miliyan 650 a bisa ƙiyasi.

Tebas ya kuma ce an yi ƙiyasin masu Kallon LaLiga ta allunan talabijin a duniya sun haura mutum biliyan 2.5.

Saboda muhimmancin wasan, akwai faɗar da ake yi da cewa duniya kanta kan tsaya cak har na tsawon mintuna 90 da zarar an fara taka leda a wasan hamayyar El Clasico.

Muhimman bayanai game da El Clasico

A ranar 17 ga Fabrairun 1929 aka buga wasan El Clasico na farko a filin was ana Les Corts, wato tsohon filin Barcelona, inda Real Madrid ta bi Barcelonan har gida ta lallasa ta da ci 2-1 a wasan mako na 2 na LaLigar kakar.

Wasan gobe zai zama wasa na 189 da ƙungiyoyin za su buga. Real Madrid ce da yawan nasarori inda ta ci wasanni 79 yayin da Barcelona take da nasarori 74; sun yi canjaras a wasanni 35 jimilla.

Haka nan ma a yawan jefa ƙwallaye, Madrid ɗin ce take kan gaba da ƙwallaye 304; Barcelona tana da 301.

Har wa yau, a samun nasarar wasannin da aka buga a gida, nan ma Madrid ɗin ce take gaban Barcelona da nasara a wasanni 56 tana ci gidanta; yayin da ita kuma Barcelona ta ci wasan El Clasicon a gidanta har sau 51.

Sau 15 Madrid ta yi canjaras a gidanta, ita kuwa Barcelona sau 20. Sun doke juna sau 23 kowannesu a wasannin waje.