Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar ƙyandar biri

An fargar da likitoci game da yadda sabon nau’in cutar ƙyandar birin ke yaɗuwa cikin saurin.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar ƙyandar biri

Masana kimiya a Afirka na shirin ayyana dokar ta-ɓaci kan barazanar bazuwar ƙyandar biri a nahiyar, bayan ɓullar sabon nau’in cutar da ke yaɗuwa cikin sauri.

A ranar Talata ce ake sa ran masanan za su sanar da dokar ta-ɓacin kan cutar a Afirka.

Cutar na ƙara yaɗuwa cikin sauri a bana, bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango.

Ana sa ran jami’an cibiyar hana yaɗuwar cututtuka ta Afirka za su fitar da gargaɗi a kan yadda cutar za ta iya yaɗuwa sosai idan har aka gaza ɗaukar ƙwararan matakai.

An dai riga an fargar da likitoci game da yadda sabon nau’in cutar ƙyandar birin ke yaɗuwa cikin saurin.

Cutar na yaɗuwa ce a tsakanin mutanen da suka yi cuɗanya, kuma tana da alamomi masu kama da na mura, sai dai na ƙyandar biri ya fi tsanani.

A  Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango, inda cutar ke yaɗuwa sosai, mutum 27,000 aka tabbatar sun kamu da ita a bara, daga cikin su kuma fiye da dubu sun mutu.

Cutar ta kuma yaɗu zuwa ƙasashen da suka haɗa da Kenya da Rwanda da Burundi da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ana sa ran cewa ayyana dokar ta-ɓaci kan ƙyandar birin za ta taimaka wa gwamnatoci wajen tsara ayyukan gaggawa domin kai ɗauki da kuma ƙara inganta hanyar shigar da tallafin magunguna a wuraren da aka samu ɓullarta.

Cibiyoyin kula da lafiya a wajen Afirka ma za su sa ido a kan yadda lamarin zai kasance da kuma hasashen abin da zai faru nan gaba.

Yaya girman cutar ƙyandar biri yake kuma a waɗanne ƙasashe ta fi yaɗuwa?

Cutar ƙyandar biri wato Mpox, wata ƙwayar cuta ce ke haifar da ita da ake kira da monkeypox.

Tana daga cikin nau’o’in cututtuka irin na cutar farankama, kodayake ita farankama ba ta illa kamar Mpox.

Ƙwayar cutar ta samo asali ne daga dabbobi, inda take yaɗuwa zuwa ga ɗan Adam, to amma yanzu abin ya zarta haka.

An fi samun cutar a ƙauyukan da ke kusa da manyan dazuka a Afirka, kamar a ƙasashe irin su Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango.

A irin waɗannan yankuna, akwai ɗaruruwan mutanen da suka kamu da cutar har ma da waɗanda suka mutu ciki har da yara ’yan ƙasa da shekara 15 waɗanda su ta fi shafa.

Nau’i biyu na cutar na yaɗuwa

Nau’in farko shi ne mai suna “Clade 1” ya fi yaɗuwa a tsakiyar Afirka.

Sai nau’i na biyu kuma “Clade 1b,” wato sabon nau’in cutar mai matuƙar haɗari kuma ya janyo ƙara yaɗuwar cutar a yanzu.

Cibiyar CDC, ta ce an samu mutum 14,500 da suka kamu da cutar ƙyandar biri, sannan akwai fiye da mutum 450 da suka mutu sakamakon cutar a tsakanin farkon 2024 zuwa watan Yulin 2024.

Hakan ya nuna cewa, an samu ƙaruwa da kashi 160 ciki 100 na masu cutar, sannan waɗanda suka mutu kuma sun ƙaru da kashi 19 ciki 100, idan aka kwatanta da irin lokacin a 2023.

Yayin da kashi 96 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar ƙyandar biri ke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango, cutar na yaɗuwa zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Burundi da Kenya da Rwanda da Uganda.

Wani nau’in cutar marar illa sosai da ake kira “Clade ll” na yaɗuwa a ƙasashen Yammacin Afirka, wanda ya ɓarke a 2022.

Shi wannan nau’in cuta ya yaɗu a kusan ƙasashe 100 ciki har da wasu a Turai da Asiya, inda da wuya a samu cutar, to amma an shawo kanta ta hanyar yi wa waɗanda ke da yiwuwar kamuwa da cutar allurar riga-kafi.

Akwai ƙarancin allurar riga-kafin cutar ƙyandar biri da magungunanta a Kwango, sannan jami’an lafiya a ƙasar na nuna matuƙar damuwa game da yaɗuwar cutar.

Mene ne alamomin cutar ƙyandar biri?

Alamomin farko sun haɗa da zazzaɓi da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da kuma ciwon gaɓoɓi.

Idan aka fara zazzabi, sai ƙuraje su fito a fuska daga nan sai su yaɗu zuwa sassan jikin mutum yawanci tafin hannu da tafin ƙafa.

Ƙurajen waɗanda ke da ƙaiƙayi sosai ko zafi, na sauyawa a hankali su zama maruru, daga na sai su fashe.

Ƙurajen na zama a jikin mutum tsawon mako biyu ko uku, daga nan sai su washe.

To amma idan cutar ta yi tsanani ƙurajen kan yaɗu zuwa dukkan jikin mutum, musamman baki da idanu da kuma gaban mutum.

Ta yaya cutar ke yaɗuwa?

Cutar ƙyandar biri na yaɗuwa tsakanin mutum da mutum ta hanyar haɗa jiki da wanda ke da ita, har da ta hanyar jima’i da numfashi da kuma sumbata.

Sannan ana daukar cutar ta hanyar taɓa abubuwa da mai cutar ya yi amfani da su kamar zanin gado da kayan sawa da ma tawul.

Sannan mu’amala da dabbobin da ke da cutar kamar biri da ɓera da kurege na sanya a kamu da cutar.

A lokacin da aka samu ɓarkewar cutar a 2022, yawanci cutar ta yaɗu ne ta hanyar jima’i.

Yaɗuwar cutar da aka samu ma a yanzu a Kwango ana alaƙanta ta da jima’i.

Su wane ne suka fi haɗarin kamuwa da cutar?

Yawanci ana samun cutar ne a tsakanin mutanen da suke yawan jima’i da kuma mazan da ke neman ’yan uwansu maza (’yan luwaɗi). Mutanen da ke jima’i da mutane da dama sun fi haɗarin kamuwa da cutar.

To amma duk wanda ya yi alaƙa da wanda ke da alamomin cutar ma zai iya kamuwa da ita ciki har da jami’an lafiya da kuma iyalan mutum.

Shawara ita ce a riƙa kauce wa alaƙa ta ƙut-da-ƙut da duk wanda ke da cutar, sannan a riƙa wanke hannaye da sabulu da ruwa idan akwai cutar a gida ko unguwa ko kuma garin da aka samu ɓullar cutar ta ƙyandar biri.

Abu na biyu kuma ga waɗanda ke da cutar, shi ne su killace kansu daga shiga mutane har sai sun warke.

Sannan ga wanda ya warke daga cutar idan zai yi jima’i to ya riƙa amfani da kwaroron roba har sai ya yi mako 12 da warkewa, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ta yaya za a magance cutar?

Za a iya amfani da hanyar da ake bi wajen magance cutar farankama domin maganin cutar ƙyandar biri, to amma ba lallai a warke ba.

Za a iya shawo kan ɓarkewar cutar ƙyandar biri ta hanyar hana yaɗuwar cutar musamman yin riga-kafi.

Akwai alluran riga-kafi uku da ake yi, to amma ana yi wa mutanen da ke da yiwuwar kamuwa da cutar ne riga-kafin ko kuma waɗanda suka yi alaƙa ta ƙut-da-ƙut da masu cutar.

Har yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta bayar da shawarar a yi wa kowa riga-kafin ba.

A baya-bayan nan Hukumar Lafiya ta Duniya ta buƙaci masu yin magunguna su ƙara samar da riga-kafin cutar saboda amfanin gaggawa, ko da kuwa alluran riga-kafin ƙasashe ba su amince da su ba a hukumance.

(Daga BBC Hausa).