Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo
Aƙalla ’yan takara 17 ne za su fafata a zaɓen da suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya.
A yau Asabar, 21 ga watan Satumban 2024, mazauna Jihar Edo ke fita domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar da zai maye gurbin Godwin Obaseki.
Da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar za a fara kaɗa ƙuri’a kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta tabbatar, sai dai ta ce jami’anta za su isa rumfunan zaɓen kafin wannan lokaci.
Alƙaluman da INEC ta fitar sun nuna cewa mutum 2,629,025 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar da ke da ƙananan hukumomi 18 da rumfunan zaɓe 4,519.
Sai dai masu sharhi na cewa mutanen da za su kaɗa ƙuri’ar ba za su kai haka ba la’akari da yadda aka saba gani a sauran zaɓuka.
Kazalika, ita ma INEC ta ce a cikin wannan adadi, masu kaɗa kuri’a 2,249,780 ne kaɗai suka karɓi katinsu na zaɓe.
Wannan adadi a cewar INEC, ya nuna kashi 85.57 cikin ɗari na adadin masu kaɗa ƙuri’a a yayin da mutum 379,245 ba su karɓi nasu katin zaɓen ba.
Idan aka kwatanta da zaɓen gwamna da ya gabata a jihar a shekarar 2020, daga cikin mutane 2,210,534 da suka yi rajista, 557,443 ne kawai suka fito domin tantancewa a ranar zaɓe, amma 550,242 kawai suka kaɗa ƙuri’a.
’Yan takarar kujerar Gwamnan Edo
Aƙalla ’yan takara da jam’iyyun siyasa 17 ne za su fafata a zaɓen da suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya, inda manyan jam’iyyun suka kasance APC da PDP da kuma jam’iyyar Labour.
Ga jerin sunaye da kuma jam’iyyun ’yan takarar
Iyere Kennedy — Accord Party (A)
Iseghohi Tom — Action Alliance (AA)
David Udoh Oberaifo — African Action Congress (AAC)
Derek Izedonmwen Osarenren — Africa Democratic Congress (ADC)
Kingson Akhimie Afeare — Action Democratic Party (ADP)
Monday Okpebholo — All Progressives Congress (APC)
Isaiah Osifo — All Progressives Grand Alliance (APGA)
Odaro Ugiagbe — Allied Peoples Movement (APM)
Amos Areloegbe — Action Peoples Party (APP)
Edeipo Osiariame — Boot Party (BP)
Olumide Akpata – Labour Party (LP)
Friday Azemhe Azena — New Nigeria Peoples Party (NNPP)
Asuerinme Ighodalo — Peoples Democratic Party (PDP)
Patience Key Ndidi — Peoples Redemption Party (PRP)
Abdulai Anerua Aliu — Social Democratic Party (SDP)
Paul Okungbowa Ovbokhan — Young Progressives Party (YPP)
Akhalamhe Amiemenoghena — Zenith Labour Party (ZLP)
Sai dai wasu masu sharhi na ganin takarar za ta fi zafi tsakanin PDP da APC.
’Yan sanda sun taƙaita zirga-zirgar jama’a
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirga a jihar ta Edo gabanin zaɓen.
Babban sufeton ‘yan sandan ya ce an yi haka ne domin tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace wajen gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da lumana.
A sanarwar da ya fitar jiya Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi ya ce babban sufeton ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirgar ababen hawa akan tituna da hanyoyin ruwa da dukkanin nau’ukan harkokin sufuri tun daga karfe 6 na safe har zuwa 6 na yamma a ranar zaɓen.
Ya kuma kara da cewa waɗanda umarnin ya tsame sun haɗa da, kafafen yaɗa labaran da aka tantance da jami’an zabe da motocin ɗaukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan ba da agajin gaggawa.
A mutunta tsarin dimokuraɗiyya — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su gudanar da ayyukansu cikin lumana da mutunta juna a yayin zaɓen.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga.
Sanarwar ta ce Tinubu ya roƙi ’yan takarar gwamnan da jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su mutunta tsarin dimokuraɗiyya da kuma zaɓin mutane.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyya na bunƙasa ne a kan wayewa da juriya da haƙuri da kuma mutunta ka’idojinsa.
Da yake kira ga Hukumar INEC da jami’an tsaro su kasance na kowa, Shugaba Tinubu ya ce dole kowane ɓangare ya gudanar da harkokinsa cikin lumana.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kasance cikin lumana da mutunta juna a yayin zaɓen.
Haka kuma, Tinubu ya umarce su da su warware kowace irin taƙaddama ta hanyar lumana ta hannun hukumomin da doka ta amince da su.