Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

A shekarar 2024, Najeriya ta samu gagaruman sauye-sauye da al’amura masu muhimmanci da suka shafi harkokin kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, da kuma ci gaban masana’antu.

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Emanuella da mahaifiyarta tare da ‘yan uwanta cikin yanayi na farin ciki

A shekarar 2024, Najeriya ta samu gagaruman sauye-sauye da al’amura masu muhimmanci da suka shafi harkokin kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da wasanni da kuma ci-gaban masana’antu.

Daga kaddamar da rigakafin zazzabin cizon sauro na farko a duniya zuwa fara biyan tallafin karatu ga daliban manyan makarantu, har zuwa fara aikin matatar Dangote, Najeriya ta samu abubuwa da suka faranta ran ’yan ƙasarta a 2024.

Wannan rahoton na musamman zai fayyace manyan abubuwan da suka faru tare da nazari kan tasirin su ga rayuwar ’yan Najeriya.

Rigakafin cutar Maleriya

An fara yi wa ƙananan yara allurar rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro na farko a duniya, mai suna RTS,S a kasar Kamaru.

Wata yarinya mai wata takwas a duniya ce dai aka fara yi wa allurar rigakafin a wata cibiyar kiwon lafiya da ke kusa da birnin Yaoundé da ke ƙasar Kamaru.

Ƙaddamar da allurar rigakafin na daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka domin ceto rayukan dubban yara a faɗin Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar cewa a mutum 600,000 ne ke mutuwa a Afirka a duk shekara sakamakon zazzaɓin cizon sauro.

WHO ta ce a cikin wadanda ke mutuwa a sakamakon cutar, yara ’yan kasa da shekaru biyar su ne aƙalla kashi 80 cikin 100.

Tallafin Karatu

Ɗaliban manyan makarantu a Najeriya sun fara karɓar kuɗin tallafin karatu na wata-wata daga Gwamnatin Tarayya.

Asusun Tallafin Karatu na Ƙasa (NELFUND) ya bayyana cewa tuni ɗalibai 20,371 da suka yi nasara daga manyan makarantu shida a fadin Najeriya suka samu kuɗin tallafinsu na watan Yuli.

Manajan-Daraktan NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, ya ce manyan makarantun da aka fara da biyan ɗalibansa su ne:

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK)
Jami’ar Maiduguri, Jihar Borno
Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Katsina
Jami’ar Ilorin, Jihar Kwara
Jami’ar Benin, Jihar Edo
Jami’ar Ibadan, Jihar Oyo
A cewarsa, nan da makonni biyu za a kammala biyan daliban wasu manyan makarantu 55.

Sawyerr ya ce NELFUND za ta yi duk abin da ya dace domin ganin daliban da ke cin gajiyar tallafin karatun suna samun kuɗaɗensu a kan lokaci.

Daraktan Kuɗi na NELFUND, Ibom Uche, wanda shi ne ya sanya hannu kan sanarwar, ya ce Tinubu ya ba da ƙarin Naira biliyan 50 domin dalibai su amfana.

Ma’aikatar Kiwon Dabbobi

Shugaba Tinubu ya naɗa Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi, makonnni kaɗan bayan ya karɓi rahoton Kwamitin Shugaban Ƙasa kan kafa ma’aikatar.

Shugaban ƙasan ya kuma sanar da naɗin Idi Mukhtar Maiha a matsayin ministan sabuwar ma’aikatar.

Naɗin ministan na cikin jerin sabbin ministoci bakwai da shugaban ƙasan ya naɗa bayan sallamar wasu ministoci daga gwmanatinsa.

Fara Aikin Matatar Dangote

Matatar mai ta Dangote ta fara sayar da albarkatun man fetur a yunkurin da ƙasar ke yi na samun dogaro da kanta a fannin makamashi.

Daraktan rukunan kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa sun fara sayar da man dizel da man jiragen sama a ƙasar

Wannan babban matakin tsayawa da ƙafafu ga Nijeriya wajen biyan buƙatar makamashi da take da ita.

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote ne ya gina matatar man, mafi girma a nahiyar a gaɓar tekun Legas kan dala biliyan 20, kuma an kammala aikin bayan tsaiko na shekaru da dama da aka samu.

Matatar na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 kowace rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai.

Nijeriya ce kasar da ta kowace yawan jama’a a Afirka, kuma tana kan gaba a tsakanin ƙasashen da ke fitar da albarkatun mai, amma tana sayo mai daga waje saboda ba ta da matatu.

Tashin Matatar Fatakwal

Matatar Mai Ta Fatakwal ta fara aikin gwaji bayan shafe shekaru ba ta aiki, duk da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ta yi ta kashewa domin farfaɗo da ita.

Matatar Mai ta Fatakwal, kamar sauran da gwamantin Najeriya ta jima tana kashe kudi domin farfaɗo da su, ta tashi ne bayan aikin gyaran ta da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayar.

Rahotanni sun nuna matatar na da ƙarfin tace ganga 210 na danyen mai a kullum ta fara aiki.

Sabon mafi ƙarancin albashi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan dokar fara biyan N70,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikata a Najeriya.

Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin albashin a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC), wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran jagoroin bangaren majalisa suka halarta a Fadar Shugaban Kasa.

Halartarsu taron a lokacin na da nasaba da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a fadin Najeriya daga ranar 1 ga watan Agustan 2024.

Daga bisani gwamnonin jihohi sun shiga ayyana adadin kudin da za su biya ma’aikatan jiharsu a matsayin mafi karancin albashi a wannan shekara.