Abubuwan kiyayewa a Ramadan
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ya zaki da dadi da gardin wannan wata na Ramadan? Da fatan Allah Ya sa mu ga karshensa lafiya, Ya hore mana albarkar da ke cikinsa, kuma Ya sa muna daga cikin ‘yantattun bayinSa, amin.Ga bayani mai dauke da amsoshin tambayoyin da wadansunku suka aiko game […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ya zaki da dadi da gardin wannan wata na Ramadan? Da fatan Allah Ya sa mu ga karshensa lafiya, Ya hore mana albarkar da ke cikinsa, kuma Ya sa muna daga cikin ‘yantattun bayinSa, amin.
Ga bayani mai dauke da amsoshin tambayoyin da wadansunku suka aiko game da yanayin mu’amula tsakanin ma’aurata a cikin wannan wata na Ramadan, watau abubuwan da suka dace da wadanda ba su dace ba. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Abubuwan da suka halarta:
1. Babu laifi rike hannun juna, rungumar juna ko sumbatar juna tsakanin ma’aurata da rana in dai yin hakan ba zai motso musu da sha’awa ba, domin Ummuna A’isha RA ta ce Annabi SAW yana yin haka, sai dai ya zarce kowa wajen karfin halin dannewa da kuma tsare sha’awarsa; saboda haka sai a kiyaye sosai, in an tabbatar akwai yiwuwar motsuwar sha’awa komai kankantarta, to sai a kauce wa yin hakan. Da fatan Allah Ya ba da ikon kiyayewa, amin.
Ya ’yan uwa mu lura da muhimmancin wannan ayyuka cikin rayuwar aure, ta yadda har ga shi daukar azumi bai sa Manzon Allah (SAW) ya daina yinsu ba, saboda mahimmancin su. Mu kuwa al’ummar Hausawa ko ba cikin azumi ba ne ba a yinsu, kuma su ma din sunna ce kamar yadda Sallolin Nafila su ke sunna, sai ya kasance ma’aurata ba su taba juna sai lokacin ibadar aure kadai, rashin irin wannan ne ke sa ma’aurata su zama kamar ba ma’auratan ba, ba wani irin kusancin da shakuwa na musamman tsakaninsu. Da fatan za mu fara rayar da wannan sunna daga wannan wata, ya kasance ana rike hannu, runguma da sumba amma na isar da so, kauna da kulawa ba na motsar da sha’awa ba.
2. Maganganu da wasu dabi’un nuna soyayya da rana ba haramun ba ne idan har hakan ba zai motso da sha’awa ba, kuma ma’aurata su tabbatar za su iya danne sha’awarsu.
3. Idan asuba ta riski ma’aurata da janaba, azumin su na nan, kuma ba laifi yin sahur cikin janaba, haka kuma ba laifi don sun jinkirta wanka zuwa lokacin da rana ta fito, amma ya fi kyawu su yi wankan nan-da-nan don yin sallah cikin lokacinta, kuma don Mala’ikun Rahma su samu kusantarsu.
Abubuwan da suka haramta a Ramadan
1. Kowa dai ya san matsayin yin ibadar aure da rana lokacin Ramadan, babban alkaba’i ne, kuma bayan rama azumin sai an yi kaffara da azumi 60 ga duk dayan da a ka bata ta wannan hanyar.
2. Ga ma’auratan da suka aje azumi saboda lalurar tafiya, shayarwa ko rashin lafiya, bai kamata su yi ibadar aure da rana ba, ya fi kyau su kame don girmama wannan wata mai alfarma.
3. Ma’aurata su guji yin duk wani abu da zai motso da sha’awar junansu, ba laifi yin kwalliya ko sa turare ko kunna turaren kamshi na wuta da rana, amma in hakan zai motso da sha’awar juna sai a guji yin hakan.
4 Fitar da maniyyi ido biyu (ba a mafarki ba) sai an rama azumin, in kuma aka fitar da shi da gangan ta dalilin zinar hannu ko ibadar aure, to sai an rama azumin tare da kaffara.
Abubuwan kiyayewa:
1. Fitar da maziyyi ko wadiyyi ba ya karya azumi sai dai a tsabtace wajen a yi alwalla, haka ma fitar maniyyi a dalilin mafarki da rana bai karya azumi, sai dai a yi wanka a ci gaba da ibada.
2. Ma’aurata su dage wajen yin hakuri da juna cikin wannan wata, maigida ya yi hakuri kada ya yi fushi da uwargida don ba ta kammala abincin buda baki da wuri ba, kada kuma ya matsa mata da dole sai ta girka sabon abinci lokacin sahur. Uwargida kuma a kara dagewa, kada ki bari aikin gida ya hana ki yin ibadar ki cikin lokacinta, ki sani hakkin Allah a kanki yana sama da hakkin iyalinki ko da ke kanki.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in Allah Ya kai mu. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa kodayaushe, Ya hada mu duka a kofar Ar-Rayyan, amin.