Abubuwan tarihi da ke jan hankali a birnin Makka da Madina

Abubakar Haruna, (wanda ya ziyarci Saudiyya) Duk wanda Allah Ya kai shi kasar Saudiyya domin yin aikin Hajji ko Umara zai ga abubuwan tarihi iri-iri da za su dauke masa hankali a wurare daban-daban a biranen Makka da Madina.Hakazalika, gine-gine na masallatai da kaburbura da gidaje da alamu masu yawa sun isa su gamsar da […]

Abubuwan tarihi da ke jan hankali a birnin Makka da Madina
Abubuwan tarihi da ke jan hankali a birnin Makka da Madina

Abubakar Haruna, (wanda ya ziyarci Saudiyya)

Duk wanda Allah Ya kai shi kasar Saudiyya domin yin aikin Hajji ko Umara zai ga abubuwan tarihi iri-iri da za su dauke masa hankali a wurare daban-daban a biranen Makka da Madina.
Hakazalika, gine-gine na masallatai da kaburbura da gidaje da alamu masu yawa sun isa su gamsar da mutum cewa lallai biranen Makka da Madina wurare ne masu tsarki kuma da aka yi gwagwarmaya a cikinsu. Sannan kuma wuraren za su sanya mutum ya kara jaddada imaninsa ga Allah da Mazonsa Annabi Muhammdu tsaira da aminci Allah su tabbata a gare shi.
Wuraren tarihin za su sanya wanda ya je ziyara wurin ya jinjina wa sahabban Annabi wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don yadawa da bunkasa da kuma ci gaban addinin Musulunci da karfinsu da kuma dukiyoyinsu ba tare da wata fargaba ba.
Wuri na farko da zai fara jan hankalinka shi ne masallacin Manzon Allah. Irin yadda aka kawata shi ta hanyar yi masa ginin zamani da kuma kayan alatun da aka sanya masa. Za ka ga masallacin da babu kamarsa daraja da girma da kuma kwalliya. Wani abu da zai ba ka sha’awa shi ne irin yadda ake tsaftace masallacin ba tare da gajiyawa ba.
 Ba za ka rude ba sai ka shiga inda kabarin manzon Allah yake da kabarin sayyidina Abubakar da na Umar. Irin yadda aka kawata su, aka killace su don gudun kada jahilai su yi wauta, abin sha’awa ne. Wani abin mamaki shi ne, sashin inda ‘Rauda’ take a masallacin. Duk wanda ya shiga ‘Rauda’ tamkar ya shiga wani dausayi ne daga dausayin Aljanna. Da ka shiga za ka ji duk bakin cikinka ya gushe, ka manta da komai, ka shiga farin ciki da annashuwa. Ana gane mutum ya shiga Rauda idan ya hau kan koriyar dardumar da aka shimfida a cikin masallacin.
Sai munbarin Manzon Allah mai daukar hankali, shi ma wani abu ne na tarihi da za ka gani kuru-kuru ba tare da wani ya kare maka ba. Daga gefen masallacin za ka hangi makabartar Baki’a wacce aka binne da yawa daga cikin sahabbai da waliyyai masu yawa. Makabartar tana daya daga cikin abubuwan tarihi da ke tuna wa mutum lahira, ya mance da duniya gaba daya. Da mutum ya shiga makabartar sai ya mance da kansa duk mukaminsa da arzikinsa a duniya zai ga wadanda suka fi shi daraja sun mutu kuma an binne su. Makabartar ta zama wani wuri na wa’azi ga masu ziyara da tuna musu girman Allah.
Daga nan sai masallacin kuba wanda Manzon Allah yake yin sallar nafila a ciki. An ruwaito cewa Manzon Allah yakan ziyarci masallacin duk ranar Asabar, ya yi Sallah raka’a biyu. Shi ma wuri ne da zai kara tabbatar maka cewa Musulunci shi ne addinin gaskiya. Sai masallacin kiblataini wato masallaci mai alkibla biyu. inda aka sauya wa Manzon Allah alkibla daga masallacin kudus zuwa kallon ka’aba. Sai makabartar Shahidan Uhudu da dutsen Uhudu. Shi ma dutse ne wanda manzon Allah ya yi masa shaida. Wani abu da ke daukar hankali a makabartar Uhudu, shi ne kabarin sayyidina Hamza.
Da ka shigo cikin birnin Makka, farkon abin da zai fara jan hankalinka ita ce husumiyar masallacin Harami da kuma dogayen gine-ginen da ke kewaye da masallacin Haramin Makka. Wani abu mai ban sha’awa a masallacin Harami shi ne yadda aka tsara kofofin daki-daki kuma kowace kofa da sunanta ta yadda mai ziyara ba zai bata ba. Da ka shiga ta kofar Sarki Fahad ko kuma ta kofar Sarki Abdul’aziz za ka tafi kai tsaye zuwa ka’aba wurin dawafi.
ka’aba ta fi komai jan hankalin mai ibada saboda yadda take a tsakiyar masallacin da kuma yadda aka yi mata kwalliya da launin baki da ja da kuma fari. Sannan ga bakin dutse wanda ake tsotsa ko a shafa ko kuma a nuna shi da hannu. Hijiri Isma’ila, inda ake yin Sallar nafila raka’a biyu a ciki shi ma wani abu ne da ke jan hankali. Haka ma Mukamu Ibrahima da kuma alamun tafin kafar Annabi Ibrahim da ke kusa da ka’aba, su ma abubuwan tarihi ne da suke jan hankalin mutum. Ga wuraren shan zamzam iri-iri birjik, an jera sai wanda ka zaba. Tare da shan duk irin nau’in ruwan da kake bukata walau na sanyi ko na zafi ko kuma tsak-tsaki. Daga nan sai wurin Safa da Marwa, wanda aka kawata tare da na’urar sanyaya wuri ta yadda mutum ba zai yi gumi ba.
Akwai wurare kamar Kogon Hira, inda Manzon Allah da abokinsa Sayyidina Abubakar suka buya a ciki. Dutsen Arfa, shi ma wani abu ne da ke jan hankalin mutumin da ya je ziyarar birnin Makka. Wani abu da ke ba da sha’awa shi ne dogayen benaye da ke kewaye da masallacin Harami na Makka, kamar su ginin da aka yi masa lakabi da Darul Tajweed da kuma dogon bene mai dauke da agogon bangon mai jan hankali; kai ka ce a birnin Landan ne a kasar Birtaniya. Sai kuma katafaren wurin sayar da kayayyaki mai suna Bin Daud.
Abubuwan tarihi suna da yawa a birnin Makka da Madina kuma duk yadda mutum ya kai ga iya jawabi ba zai iya kididdige su ba.