Abubuwan tausayi da ban mamaki da suka faru a ranar Sallah a jihohin Kurmi
Wasu muhimman abubuwa guda 3 na tausayi da mamaki da ban haushi sun auku a ranar Juma’ar da ta gabata, a daidai lokacin da al’ummar Musulmi suke yin Sallar Idi garuruwa uku na jihohin Ogun da Oyo da Osun. A Jihar Ogun, wani abun tausayi ne ya auku a lokacin da wata babbar mota dauke […]

Wasu muhimman abubuwa guda 3 na tausayi da mamaki da ban haushi sun auku a ranar Juma’ar da ta gabata, a daidai lokacin da al’ummar Musulmi suke yin Sallar Idi garuruwa uku na jihohin Ogun da Oyo da Osun.
A Jihar Ogun, wani abun tausayi ne ya auku a lokacin da wata babbar mota dauke da kutattarin ita ce da ake sarrafawa zuwa katako ce ta auka wa sahun dinbin Musulmi a babban filin Idi na Atikori a garin Ijebu-Igbo a inda ta yi sanadin mutuwar mutane biyu a nan take, wasu kuma suka samu munanan raunuka. Ganin haka ne jama’a suka husata suka far wa direban da duka, inda wani dan sanda sanye da rigar sarki ya yi kokarin kubutar da direban daga hannun jama’a domin tafiya da shi ofishinsu. Sai dai bai yi nasarar kubutar da direban ba, a maimakon haka, jama’a suka rufar masa da duka, har ya rasa ransa.
A Jihar Oyo, wani abun mamaki da ya auku a birnin Ibadan shi ne rashin ganin babban Sarki, wato Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji a babban filin Idi na Agodi domin yin Sallar Idin bana, wacce babban limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere ya jagoranta. A tarihi, wannan shi ne karo na farko da babban sarkin gari wato Olubadan ya ki halartar filin Idi kamar yadda ya saba a baya. Sai dai an ga Gwamna Abiola Ajimobi da wasu kusoshin gwamnati a cikin sahun Sallar Idin.
Aminiya ta gano cewa, rashin ganin Olubadan a Idi ba zai rasa nasaba da takaddama tsakaninsa da Gwamna Ajimobi ba, a kan batun daukaka matsayin Hakimai 21 zuwa Sarakuna a masarautar Ibadan da gwamnan ya yi mako biyu day a gabata.
Da yake fadin dalilin da ya sa ya dauki wannan mataki cikin takardar sanarwa da ta fito daga fadarsa mai dauke da sanya hannun Sakataren Labarai Mista Abbas Oloko, Olubadan ya ce ya yanke shawarar yin Idi a harabar fadarsa ne domin tabbatar da zaman lafiya da kyautata tsaron al’ummar masarautar Ibadan. Ya ce an dauki matakin ne domin gujewa hargitsi a babban filin Idi na Agodi, wanda kimanin shugabannin zuri’a (mogaji) 350 da ke goyon bayan Olubadan ke iya amayar da abun da ke cikinsu, idan suka yi kicibis da gwamna a filin Idin.
A Jihar Osun, wani abun mamaki ne ya auku a lokacin da gardama ta kaure tsakanin Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Osun Dakta Ajibola Bashiru da Asiwaju (jagoran) Musulmi na kasar Yarbawa Alhaji Tunde Badmus. An tayar da jijiyar wuya a tsakanin wadannan manyan mutane ne a kan mutumin da ya kamata ya zauna a bayan liman a cikin sahun farko na sallar idi da aka yi a filin idi na Oke Baale dake birnin Osogbo.
Gwamna Rauf Aregbesola ne ya saba zama a bayan liman a kowace shekara a lokacin Sallar Idi amma a dalilin tafiya aikin Hajjin bana da gwamnan ya yi sai Kwamishinan Shari’a Dakta Ajibola Bashiru ya wakilce shi domin zama a wurin da aka kebe masa. Gardamar ta kaure ne a lokacin da Asiwaju Musulmi Alhaji Tunde Badmus tare da ’ya’yansa 2 suka isa filin Idin, a inda kwamishinan shari’a ya yi kokarin gaisawa da shi amma ya ki amsawa. A maimakon amsa gaisuwar ya nemi kwamishinan ya tashi ya canza wurin zama. kokarin da aka yi na sasanta al’amarin ya ci tura, a maimakon haka ma daya daga cikin ’ya’yan Asiwaju mai suna Lekan ne ya gaura wa daya daga cikin abokan kwamishinan mari a kumatunsa inji wata majiya mai tushe.
Sai dai Lekan ya musanta batun mari da aka ce ya yi wa Injiniya Taofeek Badmus. Ya ce: “Ni ban mari kowa ba amma Bashiru (Kwamishinan Shari’a) da mutanensa sun zo filin Idi ne domin su tayar da hargitsi saboda kowa ya sani cewa wannan sahu na bayan liman an kebe ne domin shugabannin addinin Musulunci. Bai zo wannan wuri a madadin Gwamna ba kamar yadda ya fadi,” inji Lekan.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Kwamishinan Shari’a: “Babu wata hatsaniya da aka yi a tsakanina da Asiwaju Musulmi a filin Idi na Osogbo. Bayan kasacewata Musulmi dan asalin garin Osogbo kuma Antoni-Janar kuma kwamishinan Shari’a, na zo filin Idi ne domin wakiltar Gwamna Rauf Aregbesola. Mun riga mun kebe masa wurin zama da jama’arsa amma sai na yi mamakin irin matakin da ya dauka na kin amsa gaisuwar da na yi masa da yunkurin wulakanta ni a gaban jama’a da ya yi.”