Abuja: Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa

Mutumin ya ce dole ne gwamnati ta dawo da biyan tallafin man fetur ko ya hallaka kansa.

Abuja: Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa

Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya hau saman ƙarfe a yankin Katampe A Abuja, inda ya yi barazanar kashe kansa matuƙar Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da biyan tallafin man fetur da kuma kawo ƙarshen matsin rayuwa da ake fuskanta.

Aminiya ta gano mutumin mai suna Shuaibu Alhaji Yusuf daga Maiduguri a Jihar Borno, ya rubuta wata wasiƙa, inda ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa Maso Gabas da kuma Arewa Maso Yamma.

Ya zayyano wasu buƙatu guda tara da yake so gwamnati ta cika su, inda ya ce “A madadin ’yan Najeriya, ina buƙatar waɗannan: Gwamnati ta dawo da biyan tallafin man fetur, gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Katsina, Kaduna, Neja da Borno kan matsalar tsaro kuma a ɗauki matakai cikin gaggawa a jihohin da na zayyano.

“Waɗannan su ne manyan matsalolin ’yan Najeriya kuma a shirye nake na sadaukar da rayuwata domin sama musu mafita. Ina kira ga sauran ’yan Najeriya su goya min baya a wannan tafiyar.”

Aminiya ta ruwaito cewa, muƙaddashiyar Darakta-Janar ta Sashen Bayar da Agajin Gaggawa na Abuja, Misis Florence Wenegieme, wadda ta je wajen da lamarin ya faru, ta lallashi mutumin, wanda aka yi nasara ya sauko.

An kai shi ofishin FEMD, amma daga bisani rahotanni sun bayyana cewar ’yan sanda sun tsare shi.

Kamfanin da ya daina aka ba kwangilar titin Abuja-Kaduna

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump