AC Milan ta dauki dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze
Samuel Chukwueze zai goya riga mai lamba 21 a Milan.
AC Milan ta sanar da kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Najeriya, Samuel Chukwueze, wanda ta dauko daga kungiyar Villarreal ta kasar Spain.
Labarin daga kungiyar ta AC Milan da ke rukunin kungiyoyi da ke cikin gasar Serie A a kasa Italiya, na nuna farin cikin kungiyar bayan daukar Samuel Chimerenka Chukwueze daga Villarreal CF.
- Gwamna Gombe ya sanar da sunayen kwamishinoni 17
- Mikel Obi ya zama mashawarcin Gwamnan Filato kan wasanni
Dan wasan na Najeriya ya kulla yarjejeniya da Rossoneri har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2028.
Tarihi ya nuna cewa an haife shi a Umuahia da ke Jihar Abiya a ranar 22 ga Mayu shekarar 1999.
Samuel ya zo ta bangaren matasa na Kwalejin Kwallon Kafa ta Diamond kafin ya koma Villarreal a 2017, kamar yadda jaridar labarun wasanni ta Goal ta wallafa.
Ya soma da ’yan ajin farko na kungiyar ta Spain, inda ya buga wasanni 20 kuma ya zura kwallaye hudu kafin ya fara buga wasa da babbar kungiyarsa.
A halin yanzu dai Samuel Chukwueze ya zabi goya riga mai lamba 21.