AC Milan ta sallami Massimiliano Allegri

Milan ta kammala kakar Serie A a matsayi na biyar bayan shan kashi da ci 2-1 a hannun Cagliari a wasan ƙarshe.

AC Milan ta sallami Massimiliano Allegri

Image ref 165997071. Copyright Shutterstock No reproduction without permission. See www.shutterstock.com/license for more information.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan ta sanar da sallamar kocinta Massimiliano Allegri, bayan kakar wasa mai cike da koma-baya da ta hana ƙungiyar samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai mai zuwa.

Shugabannin ƙungiyar sun bayyana kakar bana a matsayin “babbar gazawa mai girma”, bayan da Milan ta kasa cimma manyan burikanta duk da manyan sauye-sauyen da aka yi kafin soma kakar.

Milan ta kammala kakar Serie A a matsayi na biyar bayan shan kashi da ci 2-1 a hannun Cagliari a wasan ƙarshe da aka buga ranar Lahadi, lamarin da ya sa ƙungiyar ta sake rasa tikitin zuwa gasar Champions League karo na biyu a jere.

Milan dai ta shafe makonni tana fafutukar kasancewa cikin manyan ƙungiyoyi huɗu a saman teburin gasar, amma rashin daidaito da yawan rashin nasara a ƙarshen kakar ne suka jefa ta cikin matsala.

Inter Milan da Napoli da Roma da kuma Como — wacce za ta buga Champions League karo na farko a tarihinta — su ne za su wakilci Italiya a gasar ta Turai a kakar bana, yayin da AC Milan tare da Juventus za su buga gasar Europa League.

Allegri mai shekara 58 ya dawo AC Milan ne a watan Mayun shekarar da ta gabata domin fara wa’adi na biyu a kulob ɗin, bayan maye gurbin Sergio Conceição.

Kocin ya taɓa jagorantar Milan tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014, inda ya lashe kofin Serie A a kakar 2010 zuwa 2011, sannan ya ƙara da lashe Italian Super Cup a kakar da ta biyo baya.

Sai dai dawowarsa karo na biyu ba ta yi armashi ba, domin Milan ta fuskanci matsaloli da dama a kakar nan, ciki har da rashin tabbas a tsarin wasa da kuma yawan rasa maki a muhimman wasanni.

Ƙungiyar ta sha kashi a wasanni bakwai cikin 13 na ƙarshe da ta buga a Serie A, abin da ya ƙara nuna taɓarɓarewar yanayin ƙungiyar a ƙarshen kakar.

A yayin da Milan ke fama da koma-baya, babbar abokiyar hamayyarta Inter Milan ta ci gaba da ƙara hazaƙa, inda ta lashe kofin Scudetto karo na biyu cikin shekaru uku.

Rahotanni daga Italiya na nuni da cewa shugabannin AC Milan sun fara nazarin sunayen sabbin masu horarwa da za su maye gurbin Allegri, yayin da magoya bayan ƙungiyar ke fatan ganin sauyi kafin fara kakar wasa mai zuwa.