ACF da Balarabe Musa sun nuna rashin gamsuwa da haramta Boko Haram

kungiyar kare muradun Arewa (ACF)  da tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa sun bayyana damuwarsu game da haramta kungiyar Boko Haram da shugaba Jonathan ya yi.Dayake bayyani game da haramtawar, Sakataren yada labarai na kungiyar ACF  Mista Anthony Sani cewa ya yi,da farko gwamnati cewa ta yi za ta yi  amfani da karfi […]

ACF da Balarabe Musa sun nuna rashin gamsuwa da haramta Boko Haram
ACF da Balarabe Musa sun nuna rashin gamsuwa da haramta Boko Haram

kungiyar kare muradun Arewa (ACF)  da tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa sun bayyana damuwarsu game da haramta kungiyar Boko Haram da shugaba Jonathan ya yi.
Dayake bayyani game da haramtawar, Sakataren yada labarai na kungiyar ACF  Mista Anthony Sani cewa ya yi,da farko gwamnati cewa ta yi za ta yi  amfani da karfi da lalama a matsayin  dabarar  kawo karshen ayyukan ‘yan Boko Haram din. ‘’dominhaka muna fata gwamnati za ta iya amfani da karfi da lalama  domin a kawo karshen wannan matsalar.’’ Inji shi.
Dangane kuma da neman shugaban kungiyar da kasar Amurka ta sanya a yi kuwa, kungiyar ta ACF ta ce, hakan da Amurka ta yi ya nuna cewa matsalar Boko Haram ta wuce ta kasar nan kawai ta zama ta duniya baki daya.’’ Domin haka  ashe babu gaskiya a zargin da wadansu ke yi cewa shugabannin Arewa ne suka fito da Boko Haram domin shugabancin kasar nan ya gagari Jonathan, saboda la’akari da kabilarsa da addininsa da kuma yankin da ya fito.’’ Inji shi.
 A nasa bangaren, Alhaji Balarabe Musa cewa ya yi, gwamnatin tarayya tana bin abinda kasar Amurka ke so ne kawai. ‘’ Amurka ta ta ayyana kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda ce da kuma bayyana Shekau a matsayin wanda ake nemansa domin  jami’an tsaronta su samu damar kutsowa cikin kasar nan  da sunan suna neman ‘yan ta’adda.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba ta karfin jami’an tsaronmu ba, idan muka kyale kasashen Amurka da Isira’ila suka shigo kasar nan za su yi wa tsarin tsaronmu zagon kasa.  Ba haramta kungiyar ce mafita ba, abin da ya dace gwamnati ta yi shi ne ta tsaurara tsaro, ta magance matsalar da ke haifar da ta’adda su ne talauci da rashin aikin yi. Gwamnati kuma ta tabbatar  an gudanar da zabe mai inganci  da zai bai wa ‘yan Najeriya damar zaben mutanen da suke bakatar su shugabance su.’’ Inji shi.