ACF da JNI sun yi Allah wadai da harin bam a Kano

kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa (JNI) da takwararta ta Kare Muradun Arewa (ACF) sun yi Allah wadai da harin bam da aka kai a Sabon Gari a Jihar Kano wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama wasu kuma suka samu raunuka.Wata takarda dauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar JNI, Sheikh Khalid Aliyu […]

ACF da JNI sun yi Allah wadai da harin bam a Kano
ACF da JNI sun yi Allah wadai da harin bam a Kano

kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa (JNI) da takwararta ta Kare Muradun Arewa (ACF) sun yi Allah wadai da harin bam da aka kai a Sabon Gari a Jihar Kano wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama wasu kuma suka samu raunuka.
Wata takarda dauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar JNI, Sheikh Khalid Aliyu Abubakar da aka raba wa manema labarai a Kaduna ta jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ta bayyana harin da wata alama ta rashin imani kuma ta bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya da junansu.
“Muna fatan Musulmi za su tashi tsaye wajen addu’ar neman Allah Ya tona asirin duk wadanda suka kai wannan hari da kuma manufarsu. Insha Allahu kuma ba za su yi nasara ba.”  JNI na mamakin yadda aka kai harin duk da cewa akwai sojoji a kan hanyoyi suna binciken ababen hawa a Arewacin kasar nan. Abin damuwa shi ne yadda wannan hari ya faru sa’o’i 24 bayan kai hari a wasu kananan hukumomi biyu na Jihar Borno. Wannan ya sa muke ganin akwai bukatar a tashi tsaye domin kawo karshen wannan matsala,” inji JNI.
Sheikh Abubakar ya ce kila masu kai wadannan hare-hare na yin su ne domin kirkiro rikici a Arewa.
kungiyar ACF ma ta yi Allah wadai da yawan kashe-kashen da ke faruwa a Arewa da kuma harin da aka kai Kano.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin kungiyar Anthony Sani ta ce tattaunawa ce mafita kawai.