ACF ga Ibo: Babu kasar da ke iya jure yakin basasa sau biyu
Aminiya: Ya kuka ga yunkurin da ’yan Kudu maso Gabas ke yi na neman taso da batun Biyafara?Comassie: Da muka zo maganar wata jiha a Kudu maso Gabas. An yi yakin basasa da su, su suka dauki bindiga da harsasai suka yaki kasa baki daya. Aka yi wata 30 ana wannan yakin. Aka zo aka […]

Aminiya: Ya kuka ga yunkurin da ’yan Kudu maso Gabas ke yi na neman taso da batun Biyafara?
Comassie: Da muka zo maganar wata jiha a Kudu maso Gabas. An yi yakin basasa da su, su suka dauki bindiga da harsasai suka yaki kasa baki daya. Aka yi wata 30 ana wannan yakin. Aka zo aka gama a 1970, shi Shugaban kasa a lokacin, Janar Yakubu Gawon, shi da kansa ya ce ku zo a tafi tare, babu wanda ya yi nasara, ba wanda aka yi nasara a kansa. Ya kuma zo ya kawo abubuwa guda uku don gyara da sasantawa (Rehabilitation, Reconstruction, Reconciliation). Wa zai ce ba a kyautata wa mutanen nan ba? Komai ya zama daidai. Wannan abin shekara 45 ke nan da yinsa. Sai ga shi wadansu sun fito da maganar Biyafara din nan yanzu. Har suka kara fito da rediyon nan da aka rufe tun lokacin yakin basasa din. Kuma yawancin wadanda ke yin wadannan maganganun ba a Najeriya suke zaune ba, suna zaune ne a kasashen waje. Suna da gidaje suna jin dadinsu, amma sun zo suna so su tayar mana da hankali.
Kwanan nan akwai wani daga wannan sashen da ya kira taron tunawa da ranar haihuwarsa (birthday party), tare kuma da kaddamar da wadansu littattafai biyu. Aka yi hayar wuri babba, ya tara mutane, ’yan kudu maso gabas suna da yawa a wajen, kowa da jar hularsa. Akwai wadansu wadanda ba daga can suke ba, abokansa ne da ya gayyace su. Da aka fara biki, duk jawabin da ake yi, Biyafara! Biyafara!! Biyafara!!! Wadanda ba wannan ta kai su ba, hankalinsu ya tashi, suka fara tashi suna sulalewa suna fita. Shi kuma da ya ga haka, sai ya rika binsu yana rokon su yi hakuri su dawo. Su kuma sai suna ce masa, a’a, ba abin da ya kawo mu nan ba ke nan. Ba maganar Biyafara ta kawo mu nan ba. Ka ga abubuwa sun yi yawa. Kuma akwai shugabannin Ibo a wajen taron, amma ba su ce komai ba.
Lokacin da ake yin rikicin Boko Haram a nan yankin na Arewa, su da Yarabawa sun fito fili suna ta kushe wannan abin da ake yi. To amma sai ga wadannan suna neman su kara tunzuro wata tarzoma a kasar nan, wacce za ta kai ga yakin basasa. Ka san kuma kasa ba ta kai wa labari idan aka yi yakin basasa sau biyu. An yi na daya, Allah Ya taimake mu mun fita. Ga shi muna fita daga wannan tarzomar ta Boko Haram, sannan ga wadansu kuma suna so su bude wata sabuwar tarzomar. Muka ce ya kamata mu yi magana a kansa. Shi ne na yi maganar kamar yadda na fada maku. Na ce mu ba a shirye muke mu fita daga wata tarzomar, mu koma wata ba. Wadannan sune maganganun da muka yi. Maganar Boko Haram da kuma ta Biyafara.
Aminiya: Me za ka ce kan shawarar da Sakataren Majalisar dinkin Duniya Ban-Kin Moon ya ba Shugaban kasa kan kar ya yarda ya yi tattaunawar sulhu da ’yan Boko Haram?
Commasie: Na goyi bayan Ban-Kin Moon, kuma ni ma na ba Shugaban kasa shawarar kar ya yarda da maganar tattaunawar sulhu da ’yan Boko Haram. Na daya, a lokacin da ake tsakiyar wannan tarzoma an yi maganar a yi sulhu din nan, har wata kungiya daga Kano ta Dokta Datti Ahmad ta ce za ta shiga tsakani. Ba a dade ba ‘yan Boko Haram suka ce babu wannan shirin, gwamnati ma ta ce ba wannan shirin. Amma ana nan ana ta kashe mutane. Shaikh dahiru Bauchi ya so ya shiga cikin maganar tattaunawar sulhu. Shaikh dahiru Bauchi da shi kansa Shugaban kasa, Muhammdu Buhari suna daga cikin wadanda aka so a kashe a cikin garin Kaduna. An kashe wadansu. Sai yanzu za a tattauna? Saboda me?
Saboda haka na ce na gode wa Ban-Kin Moon. Kuma ina ba Shugaban kasa shawara, ya dauki shawarar nan da Ban-Kin Moon ya ba shi, ba wata maganar tattaunawa. Kuma a kan me za a tattauna? Ai shi Shugaban kasa, tun daga lokacin da aka rantsar da shi ya dauki matakai da yawa. Dama ya fada a wajen kamfen da kuma wajen rantsar da shi, muhimman abubuwan da zai fuskanta su ne; tsaro da samar da aikin yi ga matasa da makamashi da yaki da cin hanci da rashawa. Kuma a kan tsaro, wanda yake shi ne kan gaba, ya dauki matakan da suka dace. Rundunar sojoji da suke wannan yakin ya ce ba a Abuja za su zauna ba, su mayar da hedkwatarsu Maiduguri inda ake yakin. Kuma kowa ya sani, ya ce masu wata uku ya ba su, su gama da wannan abu. Kuma kowa ya sani, akwai ci gaba a cikin wannan. Sannan ya je kasashe makwabtanmu wadanda abin ya shafa. Ya je Kamaru ya ga Paul Biya. Ya je Chadi wajen Idiris Deby sun tattauna. Ya je Nijar ya samu Shugaban kasa sun tattauna. Ya je G7, sun yi alkawarin za su taimaka masa, ya je Amurka, duk sun tabbatar za a taimaka masa. Don Allah wacce tattaunawa za a yi da wadannan mutane? An makara. A bari Allah Ya kara taimaka masa a ga yadda za a shawo kan wannan matsalar don a magance ta har abada.
Aminiya: Akwai masu ganin cewa da wa za a tattauna din don ba a san su ba?
Commasie: kungiyar nan tamu, a lokacin da aka ce za a tattauna muka ce a tsaya kan yarjejeniyar sai an san ko su waye, sai sun fito. Muka ce tun da kasa ta ba da tabbacin tsare lafiyarsu, muka ba da shawarar cewa a bar su su fito, kada jami’an tsaro su ce za su kama su a kan yaudara. Muka ce su dauki wannan damar na wannan tanadin da aka yi masu na cewa ba za a kama su ba, ba za a yi masu komai ba, su fito don a kashe wannan maganar, mu san meye manufarsu a cikin wannan tarzoma.
Aminiya: Wadansu na ganin maimakon yakin da Shugaban kasa yake yi da cin hanci kamata ya yi ya ja layi ne kawai?
Commasie: Ya za a ja layi? Shi da kansa sai da ya dauki kudi ya ba jihohi don su samu su daga. Ina kudadenmu? Ga kuma surutai da ake yi, maganar yakin Boko Haram din nan, an ce an kashe Naira Tiriliyan 7. Ina makaman da aka saya suke? Tsohon babban Hafsan tsaro ya fito yana cewa, yaushe rabon da su sayi makamai. Amma ana cewa an kashe kudade masu yawa wajen sayen makamai. Kai har sau biyu aka fada mana a Afirka ta Kudu an dauki kudadenmu, kudi hannu, an kama su, an ce za a sayo makamai ne ko? To gwamnatin wasa da wargi muke da ita ne? Saboda haka idan wadannan abubuwan sun bullo a bincika, idan akwai cin hanci da rashawa, a kama a hukunta wadanda ke da hannu a ciki, kuma a maido kudaden, ko kuma abin da aka samu a wajensu. Ai abubuwan da aka yi suna da yawa. Abin da ya gani lokacin da ya amshi mulkin nan kazamin abu ne sosai, da wuya a ce a ja layi?
Yanzu ba shi da kudaden da zai tafiyar da mulki, jihohi ma ba su da kudade. Wannan ai wargi ne a ce wai a ja layi kawai. Sauran abubuwan da suka faru a baya fa?
Aminiya: Amma ba ka ganin kamar wannan zai dauke hankalin ita gwamnatin daga yin abin da ya kamata?
Commasie: Ai ana yin wannan ana wancan ne. Ba zai yiwu yaki da cin hanci da rashawa ya dauke hankalin gwamnati ba. Ai yanzu ma yana yin wadansu abubuwan, kowa kuma ya gani. Tsoron ma da ake ji a Najeriya ai abu ne muhimmi. Yadda duk duniya ta sanya ido a kanmu muhimmin al’amari ne saboda an ga an samu shugaban da ya dace, mai gaskiya, mai tsoron Allah, mai adalci. To adalcin shi ne idan ka yi, a yi maka, in ba ka yi ba a kyale ka.
Aminiya: Kana ganin an taso da batun Biyafara din nan ne a yanzu don a kawo wa wannan gwamnatin cikas?
Commasie: Kai me ka gani? kuri’a nawa suka ba ta wajen zabe. Me aka yi masu? Me ya sa za su kirkiro da wannan? Me wannan gwamnati ta yi masu tun da ta kama aiki? Sun ce mukaman da ake nadawa, duk suna yankin Arewa ne, a ina a Arewa din? An gama ke nan? An nada ministoci ne da sauran mukamai gaba daya, an gama? Ka kirga mukamai nawa ne aka bayar? Mun ji Babban Hafsan tsaro da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, duk ’yan Arewa maso Gabas, shin ba a nan ne ake ta tarzomar nan ba? Ba da dan gari a kan ci gari ba? Kuma wadannan ba su suka san abubuwa ba? Ba ka ji kwanan nan ma an so a yi wa shi Babban Hafsan tsaro kwanton-bauna (ambush) ba? Saboda haka tatsuniya suke yi. Je ka fada masu, ni na fada. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana aikinsa a hankali yadda ya kamata, ba ya so ya yi kuskure. Kodayake dan Adam tara yake, bai cika goma ba, amma bi a hankali yana da amfani. Kuma ko wata uku din nan da ake cewa ba a yi ba, amma ana surutu. To ba daidai ba ne. A bari ya gama a gani. Kuma ya riga ya ce sai watan Satumba zai aika da sunaye, ko zai nada ministocinsa. Shin don Allah ba sai a jira sai an nada ba tukunna?
Aminiya: Wane kira kake da shi ga sauran al’ummar Najeriya gaba daya?
Commasie: kasar nan tamu ce, dole wani ya zama Shugaba ko daga ina ya fito, in dai Allah Ya sa jama’a sun ce shi ne Shugabansu, to a goya masa baya, a taimake shi ya yi nasara. A lura da kasar nan tamu, ita ake magana.