ACF ta ga sunan ’yan Arewa da za a ba hanci don zaben Jonthan a shekarar 2015

kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ta tabbatar da cewa ta ga jerin sunayen wasu manyan dattawan Arewa da wasu da ake zargin suna aiki ga Shugaba Goodluck Jonathan suka tsara domin ba su cin hanci a sake zabensa a shekarar 2015.Wata sanarwa da Shugaban ACF, Alhaji Aliko Mohammed ya sanya wa hannu da kansa, ta […]

ACF ta ga sunan ’yan Arewa da za a ba hanci don zaben Jonthan a shekarar 2015

Alhaji Aliko Mohammed Shugaban ACFkungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ta tabbatar da cewa ta ga jerin sunayen wasu manyan dattawan Arewa da wasu da ake zargin suna aiki ga Shugaba Goodluck Jonathan suka tsara domin ba su cin hanci a sake zabensa a shekarar 2015.
Wata sanarwa da Shugaban ACF, Alhaji Aliko Mohammed ya sanya wa hannu da kansa, ta ce jerin sunayen ya kunshi sunayen mafi yawan mutanen da ake girmamawa a Arewa.
 “Sai dai kuma mun gudanar da bincike a cikin gwamnati kuma mun yi magana da mutane da dama da sunansu ya bayyana a jerin sunayen, kuma sun tabbatar mana cewa ba su san komai game da hakan ba. Babu wanda ya gana da su kuma ba su sha’awa ko burin ganawa da kowa kan wannan batu,” inji sanarwar.
ACF ta kara da cewa, “Wadanda suke nema ko suke ba Shugaban kasa shawarar ya ba da cin hanci domin neman goyon baya, a fili sun kawar da batun sake zaben nasarar da Shugaban kasar ya samu a matsayinsa na Shugaban kasa zuwa wani abu daban. Kuma idan haka lamarin yake, to ana ba su shawarar su cire shugabannin Arewa daga wannan harka, domin wannan jerin sunaye da muka gani hakika ya kunshi sunayen wasu manyan mutanen Arewa da ake girmamawa.”
Idan za a iya tunawa Gwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ne ya fara fallasa cewa akwai jerin wadannan sunaye.
Sai dai mashawarcin Shugaban kasa kan al’amuran siyasa Ahmed Gulak ya musanta zargin, har ma ya zargi Gwamnan Neja da cewa ya sha kirkirar karya ga Shugaba Jonathan.
 “Abin da kawai zan iya cewa shi ne Shugaban kasa ba ya ba da cin hanci ga jama’a. Muna kalubalantar Aliyu ya fadi sunayen muanen da aka ba su cin hancin,” inji shi.