ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Ƙungiyar ta ce dole ne a biya diyyar mutanen da rayukansu ya salwanta a harin.

ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi Allah-wadai da harin da sojoji suka kai ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Silame a Jihar Sakkwato, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

Ƙungiyar ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike tare da bai wa waɗanda abin ya shafa diyya.

“Wannan hari kuskure ne mai yawa,” in ji mai magana da yawun ACF, Farfesa Tukur Muhammad-Baba.

“Wannan ya tuna mana da harin da sojoji suka kai Tudun Biri, a Jihar Kaduna, da wasu jihohi kamar Adamawa da Nasarawa, waɗanda suka ga asarar rayuka ba tare da wani dalili ba.”

Ƙungiyar ta kuma soki martanin sojoji kan harin.

“Wannan sakaci ba za mu yarda da shi ba. Dole ne a hukunta masu hannu a wannan aika-aika,” in ji Muhammad-Baba.

Duk da haka, ƙungiyar ta yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, kan ziyartar al’ummar da abin ya shafa.

Gwamnan ya jajanta musu tare da alƙawarin bayar da tallafi ga waɗanda suka jikkata.