Actibate Nigeria ta yi fatan kawo karshen hare-hare a Najeriya
kungiyar Actibate Nigeria reshen Arewa ta Gabas ta taya al’ummar Musulmi murnar bikin Babbar Sallah, inda ta yi fatan Allah Ya kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin da ma kasa baki daya.kungiyar ta bayyana haka ne a sakonta na Babbar Sallah inda ta ce tuni mabiya addinan da ke kasar […]
kungiyar Actibate Nigeria reshen Arewa ta Gabas ta taya al’ummar Musulmi murnar bikin Babbar Sallah, inda ta yi fatan Allah Ya kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin da ma kasa baki daya.
kungiyar ta bayyana haka ne a sakonta na Babbar Sallah inda ta ce tuni mabiya addinan da ke kasar nan suka gano cewa kashe-kashen da wasu ke yi da sunan addini, ba addini, ba ne.
kungiyar Actibate Nigeria ta ce addinin Musulunci addini ne mai son zaman lafiya, kuma wadanda ba Musulmi da dama sun san haka, inda suka fahimci cewa wasu batagarin mutane ne kawai suka fake da addini suna aikata ta’addanci.
kungiyar ta kuma yi fatan ci gaba da samun zaman lafiya da hadin kai domin ci gaba kasar nan, tare kuma da yaba wa Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kan kwamitin da ya kafa don tallafa wa wadanda rikicin ta’addancin ya shafa a yankin Arewa maso Gabas, kuma ta ce tana da tabbacin cewa kwamitin zai taimaka wa wadanda lamarin ya shafa a daidai wannan lokaci na bikin Sallah.