Adabin ketare: Bunkasar tunanin marubuci
Marubuta kagaggun labaran Hausa na zamani ko kuma kamar yadda aka fi kiransa da ‘Adabin Kasuwar Kano’ (tunda dai ba a canza wa tuwo suna) sun sha suka ko hantara ko kuma zargi kan cewa suna kwafo kayan aikinsu daga Larabawa da Turawa, domin gina tunaninsu kan ayyukansu na adabi, to ku sha kuruminku, domin […]
Marubuta kagaggun labaran Hausa na zamani ko kuma kamar yadda aka fi kiransa da ‘Adabin Kasuwar Kano’ (tunda dai ba a canza wa tuwo suna) sun sha suka ko hantara ko kuma zargi kan cewa suna kwafo kayan aikinsu daga Larabawa da Turawa, domin gina tunaninsu kan ayyukansu na adabi, to ku sha kuruminku, domin kuwa ai dama haka fasalin adabin kasuwa yake a duniya. Dubi dai bunkasuwar adabi a Ingila, musamman wadanda ake yi wa lakabi da na ‘Grub Street Literature’ ko kuma na ‘Chapbooks’ da suka samu domin biyan bukatar masu karamin karfi kuma ko da hada-hadar dab’i da rubuce-rubuce ta kankama daga karni na 15 da na 16, akwai ire-iren wadannan ayyuka masu araha. Yawancinsu sun fita kasuwa ne daga karni na 17 da na 18 a Ingila. Kun san cewa ko William Shakespeare ya dogara da aikin Thomas Kyd ne na “The Spanish Tragedy” har ya samar da littafin ‘Hamlet.’
Haka kuma wakar da Thomas Wyatt ta Sonnet da ya gabatar, ita ta ba shi Shakespeare din da wasu marubuta da dama na zamanin “Shakes” din suka yi ta tallatawa, kamar su Thomas Champion. Wato dai marubutan Adabin Ingilishi na birnin Landan da suka rayu tsakanin karni na 17 da 18, irin su Christopher Marlowe da marubuta wakoki, irin su Edmund Spenser da Tottel duk sun yi amfani da ayyukan adabi na wasu marubuta da suka gabace su.
A Jamus ma an samu irin wannan fasalin cikin karni na 18 da 19, inda aka samar da Adabin Kitsch wanda shi ma yake bayyana wani aiki na jabu ko gwanjo ko dai kawai ka ce aikin da aka yi kwashe-kwashe, aka samar da shi. Shi ma din dai ya tada zaune-tsaye tsakanin marubutan da kuma masu nazari da sharhi suke ganin ba wani abin damuwa ko nazari ne da har za a maida kai kansa ba kuma suka jaddada cewa yana da alaka da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karbuwa daga masu karatu.
Su kuwa kagaggun labarun Masar, samuwarsu ya fara ne tun zamanin mulkin Sarki Muhammad Ali (1805-1848), wanda ya tura masana zuwa Faransa da Italiya domin su samo kwarewar da za su karantar da daliban Misira. A 1820 ya kafa kamfanin wallafa Bulak inda ake wallafa ayyukan adabin da aka fassaro daga kasashen ketare da kuma na Arabiyya. Bayan kwashe-kwashe na fassara da Misirawa suka gama yi, an tabbatar da cewa sun fara gina nasu tunanin a cikin ayyukan adabinsu, domin ya dace da yanayin rayuwarsu da al’adunsu da kuma zamantakewarsu. Wannan ne ya sanya ake ganin littafin ‘Zaynab’ na Muhammad Husayn Haykal da ‘Adraa Denshawi’ na Muhammad Tahir Hakki da kasancewa ayyukan adabi na farko a karni na 18.
Adabin Kasuwar Kano kuwa ya sha mangara da harbi da bulala daga masana da manazarta da dalibai (irina), duk da cewa da ni, da kai, da ke, kai! da kowa da kowa mun yadda da cewar ‘AKK’ yana samun tasiri ko fassara ko cakudedeniya daga wasu wuraren, musamman marubutan dauri. Canzawar fasalin abin murna ne gare mu kamar yadda na Masar ya canza da dadewa. Duk da cewa ba a rasa nono a ruga amma yanzu da wuya a cikin irin wancan fasalin a samu kwashe-kwashen a adabin Masar.
Me ye mafita ga tunanin marubuta Adabin Kasuwar Kano? (Kar ku manta ba ni na kashe zomon ba, hasalima, ni ko farautar ban je ba)!
Malam Bashir yana dalibtar digirin-digirgir ne a Jami’ar Azhar, Al kahirah, Masar.