Adadin Alhazan da suka mutu ya haura 1,000 a Saudiyya
Galibin Alhazan da suka rasu ba su yi rajistar aikin Hajjin na bana ba.
Adadin waɗanda suka mutu a aikin Hajji na bana da aka yi a kasar Saudiyya sakamakon tsananin zafi ya haura 1,000.
Sai dai bayanai sun ce fiye da rabin waɗanda aka ba da rahoton rasuwarsu alhazai ne da suka sauke farali ba tare da sun yi rajistar aikin Hajjin ba.
Alƙaluma da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito a wannan Alhamis ɗin sun nuna an samu sabbin mace-mace daga cikin alhazan kasar Masar.
A cewar wani jami’in diflomasiyya na Masar, adadin ’yan kasar da suka rasu sun kai 658, bayan samun mutum 58 da suka rasu a bayan nan.
Ko a jiya Laraba wani jami’in diflomasiyyar Larabawa ya shaida wa AFP cewa mutanen da suka mutu a cikin alhazan Masar kaɗai sun haura zuwa aƙalla 600 daga sama da 300 a rana ɗaya da ta gabata, galibi saboda tsananin zafin ranar da wahala a jure masa.
Daga baya jami’in diflomasiyyar ya ƙara da cewa jami’an Masar a Saudiyya sun kuma samu rahoton ɓatan alhazai, ciki har da 600 da suka rasa rayukan nasu.
Baya ga Masar, ƙasashen Jordan da Indonesiya da Malaysia da Indiya da Iran da Senegal da Tunisiya da Sudan da Iraƙi ma sun tabbatar da mutuwar mutanensu, ko da yake a lokuta da yawa hukumomi ba su bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.
Daga cikin mutum 150,000, Pakistan ta bayyana cewa zuwa yanzu alhazanta 58 ne suka riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.
Indonesia mai kimanin mutum 240,000 da suka sauke farali ta rasa alhazai 183 kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Addini ta bayyana sabanin mamata 313 da ta samu a bara.
A bara ma fiye da alhazai 200 ne aka ba da rahoton mutuwarsu, mafi yawansu daga Indonesiya.
A cikin shekaru da dama da suka gabata, Hajjin kan faɗo a daidai lokacin bazara a Saudiyya.
Wani bincike na Saudiyya da aka wallafa a watan da ya gabata ya nuna cewa zafi na ƙaruwa da digiri 0.4 a ma’aunin salshiyas a kowace shekara 10.