Adadin al’ummar duniya ya kai biliyan takwas —MDD
Al’ummar duniya za ta ci gaba da karuwa zuwa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin al’ummar da ke ban kasa a yanzu ya kai biliyan takwas.
MDD ta ce an cimma wannan alkaluma ne bayan tarin jariran da aka haifa yau talata, sabanin biliyan 7 da ake da su shekaru 12 da suka gabata.
- An kashe shugabannin ’yan ta’adda Halilu Sububu da Gwaska Dankarami
- Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a 2022
Sanarwar Majalisar da ke bayyana wannan alkaluma ta ruwaito Antonio Guterres na cewa matakin abin farin ciki ne.
Sai dai kuma Guterres ya ce babban nauyi ne da ya sake rataya kan mahukunta dangane batutuwan da suka shafi jinkai da zaman lafiyar Duniya baya ga samar da abubuwan more rayuwa.
A cewar Majalisar wannan adadi na nufin cewa al’ummar duniya sun karu da biliyan guda a cikin shekaru 12 da suka wuce.
Majalisar ta danganta wannan bunkasa ta al’ummar duniya da yadda ake samun tsawon rai, sakamakon irin ci gaba da aka samu a bangaren kiwon lafiya, sarrafa abinci mai gina jiki da kuma dabarun kiyaye tsaftar jiki da ta muhalli.
A kasashe matsakaita a fannin tattalin arziki, akasari a nahiyar Asiya ne aka fi samun yawan jama’a a cikin shekaru 10 da suka wuce, inda yawansu ya karu da miliyan dari 7 tun daga shekarar 2011.
Amma a yayin da da dama suke nuna damuwar cewa mutane biliyan 8 sun yi wa duniya yawa, akasarin kwararru na cewa babbar matsalar ita ce yadda masu hannu da shuni suka yi kane-kane a kan arzikin duniya.
Sai dai duk a yayin da al’ummar duniya suka kai wannan adadi, kwararru sun ce ya yi ta raguwa da kasa da kaso 1 a duk shekara, abin da suke ganin shi zai hana yawan al’ummar duniya kai wa biliyan 9 har zuwa shekarar 2037.
Saura kiris a kai biliyan takwas —MDD
Tun a makon jiya ne Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa al’ummar duniya za su kai biliyan 8 a ranar 15 ga watan Nuwamba.
Ta yi kiyasin cewa karuwar za ta kasance ninki 3 kenan na yawan al’ummar duniya a shekarar 1950, lokacin da ake da mutane biliyan 2 da rabi.
Jami’ar hukumar, Rachel Snow ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa bayan karuwar da al’ummar duniya suka yi cikin sauri a cikin shekarun 1960, yanzu yana tafiyar hawainiya.
Yadda al’ummar duniya ke yaduwa ya ragu daga kashi 2 da digo 1 a tsakanin shekarun 1962 da 1965 zuwa kasa da kashi 1 a shekarar 2020.
Adadin na iya raguwa zuwa kasa da rabin kashi zuwa shekarar 2050, sakamakon yadda ake ci baya wajen samun rabo na haihuwa, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta yi hasashe.
Sai dai majalisar ta yi wani hasashen na daban da ke nuni da cewa duba da yadda ake samun karin tsawon rai, inda ake kai wa shekaru 72, da kuma karuwar wadanda suka kai munzulin haihuwa, al’ummar duniya za ta ci gaba da karuwa zuwa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030.
Haka kuma, ta yi hasashen al’ummar za su kai biliyan 9 da dubu dari 7 a 2050, sannan a 2080 adadin zai kai biliyan 10 da dubu dari 4.