Adadin kayayyakin da Najeriya ke samarwa a ciki gida ya ƙaru —NBS

Bangaren noma da ayyuka ne kan gaba a yayin da aka samu ƙaruwar kayayyakin da Najeriya ke samarwa a cikin gida.

Adadin kayayyakin da Najeriya ke samarwa a ciki gida ya ƙaru —NBS

Adadin kayan da Najeriya take samarwa a ciki gida ya ƙaru da kashi 3.19% daga watan Afrilu zuwa watan Yuni 2024.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBSa) ce ta sanar cewa bangaren noma shi ne kan gaba wajen wannan nasara da aka samu.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da ta fitar kan yanayin alƙaluman kasar a watanni uku na biyun cikin shekarar (Afrilu zuwa Yuni).

Rahoton ya bayyana cewa yawan kan da aka samar a Najeriya a cikin watanni ukun ya zarce kashi 2.98 cikin 100 da aka samu a watanni ukun farkon shekarar.

Hukumar ta bayyana cewa a watanni uku na farkon 2023 kuwa, 2.51% ne kason kayan da aka samar a cikin gida a Najeriya.

 

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara