Adadin mutanen duniya zai ragu nan da ƙarshen ƙarni — Bincike
Binciken ya nuna yadda wasu kasashe za su saku karuwar adadin mutane.
Wani bincike da ‘Mujallar The Lancet’ ta yi, ya nuna cewa, yawan al’ummomin kasashen duniya zai ci gaba da raguwa har zuwa karshen wannan karni.
Binciken da kwararrun suka yi, ya yi kokarin hasashen adadin yawan al’ummar duniya baki daya, inda suke amfani da tarin alkaluman haife-haife da mace-mace da kuma abubuwan da ke haddasa karuwar jama’a.
- El-Rufai Ya Kai Ziyara Sakatariyar Jam’iyyar SDP
- An gurfanar da Amal kan zargin bai wa dan sanda cin hanci
Binciken ya kuma yi gargadin cewa, za a samu karuwar jariran da ake haihuwarsu a kasashen duniya masu tasowa, sabanin kasashen da suka ci gaba, inda haihuwar jariran za ta samu koma-baya, lamarin da zai haddasa gagarumin sauyi a tsakanin al’ummomin bangarorin biyu.
Tuni dai yawan haihuwa ya ragu a rabin kasashen duniya, ta yadda ba za a iya habbaka adadin mutanen ba zuwa mizanin da ake bukata kamar yadda tawagar daruruwan masu binciken kasa da kasa ta bayyana a ‘Mujallar The Lancet’.
Nan da shekara ta 2050, za a samu raguwar kashi daya bisa uku na yawan jama’ar kusan daukacin kasashen duniya kamar yadda cibiyar da ta gudanar da bincikenta.
Binciken, ya ayyana Samoa, Somalia, Tonga, Nijar, Chadi da Tajikistan a matsayin kasashen da ake sa ran za su samu karuwar al’umma fiye da mizanin da ake bukata nan da shekara ta 2100.