Adalci ginshikin zaman lafiya

Masallacin Al-Bayan Jos Godiya ta tabbata ga Allah Mai kowa Mai komai, wanda Ya sanya adalci ginshikin tsayuwar sama da kasa. Mun shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.Salati da sallamewa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa […]

Adalci ginshikin zaman lafiya
Adalci ginshikin zaman lafiya

Masallacin Al-Bayan Jos

Godiya ta tabbata ga Allah Mai kowa Mai komai, wanda Ya sanya adalci ginshikin tsayuwar sama da kasa. Mun shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.
Salati da sallamewa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda ya yi imani da shi ya yi aikin kwarai har tashin kiyama.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Allah Ya umarce mu da yin adalci a bayan kasa, kuma da adalci sama da kasa suka tsayu. Allah na taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancinta.
Hudubarmu ta yau tana bayani ne kan abubuwa uku: Kan adalcin da Musulmi suka rasa a duniya da tsaron kasa da aminci ga ’yan kasa da kuma wadanda masifa ta shafa.
Game da adalcin da Musulmi suka rasa a duniya, Allah Madaukaki Ya umarci Musulmi su yi adalci a kowane hali, inda Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci shi ne mafi kusa da takawa.”
Kuma Ya ce: “Kuma idan kun fadi magana to ku yi adalci, kuma koda ya kasance ma’abaucin zumunta ne….”
Kuma Ya sake cewa: “Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kayutatawa…”
Ya ku bayin Allah!! Shin yanzu akwai adalci a bayan kasa? A duniyance akwai adalci ga Musulmin Duniya? A Najeriyance ana yi wa Musulmi adalci? A jihance, Jihar Filato tana yi wa Musulmi adalci? Amsa ita ce: Babu adalci.
Ba sai na yi bayanin abin da ya faru da Musulmi a Kafanchan, ko Zangon Kataf, ko wasu wurare ba, amma a nan Jihar Filato ga kadan daga cikin abin da aka yi wa Musulmi:
– A 1992 a kauyen Gero an far wa Musulmin garin ’Yan Lambu aka kashe fiye da mutum 17, aka raunana wadansu, amma ba wanda aka kama aka hukunta. Don me? Don Musulmi aka kashe.
– A 1994 Gwamnan soja na wancan zamani ya nada Alhaji Aminu Mato a matsayin kantoman karamar Hukumar Jos ta Arewa saboda cancanta, Kiristocin Jos suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka yi mummunar zanga-zanga suka kashe Musulmi suka kone musu dukiya, amma wannan aika-aika ba ta’addanci ba ne!
– A shekarar 2001, an turo wata mace Kirista ta ratso tsakiyar masallata a ranar Juma’a a Jos ana yi mata magana sai wasu bakaken arna da kwari da baka suka kewaye masallata suna harbinsu, kafin rabin awa, duk Jos ta dauka domin abin shiryayye ne, gwamnatin Filato ta yi kokari ta kama Musulmin da aka kashe musu ’yan uwa aka kone musu gidaje ta kulle sama da Musulmi 500, a yayin da aka kama Kiristoci 65. Ga garin Dilimi an karkashe maza da mata, a yanzu ba kowa a garin duk an kori mutanen garin, wa ya yi magana?
4- A shekara ta 2002 a watan Fabrairu an kone babbar kasuwar Jos wadda take kewaye da masu gadi barkatai, an kuma kone kasuwar Laranto/ Katako ’Yan Hatsi, amma ko kwamitin jeka-na-yi-ka ba a kafa don bincike ba, bugu-da-kari ba a kama ko kare ba.
5- A shekara ta 2002, an dauke mazabu da suke wuraren Musulmi aka mayar tsakiyar unguwannin Kiristoci a Eto-Baba, Musulmi sun je kada kuri’unsu aka rutsa su aka rika kasha su aka kone motocinsu, aka turo ’yan sandan kwantar da tarzoma suka je makarantar Sakandaren Al-Iman sashin firamare suka harbe yara biyu suna aji suna karatu, ba wanda aka kama, ba wanda ya yi magana a manyan kasashe da kanana.
6- A shekara ta 2004 an kai mummun hari a garuruwan Yalwan Shendam da Shendam da Garkawa da Zomo da Bakin Ciyawa da Yamini da Tunkus da Filgani da Langtang da Wase da Dengi da Kabir (Amfer) da sauransu, An karkashe mata da yara an sace matan Musulmi sun zama ganima, har yanzu ba a ga wadansu matan ba, amma wannan ba laifin da ya kamata a yi bincike a gano masu hanu a ciki ba ne, kuma bai kai manyan kasashe su tsawatar ba. A lokacin Obasanjo yana shugaban kasa ne da ya ga alamar kasar za ta yamutse ya kafa dokar ta baci a jihar.
7- A shekara ta 2008 bayan an shafe shekara Takwas ba a taba yin zabe a karamar Hukumar Jos ta Arewa ba, sai dai a dora kabilun da yawansu bai kai daya bisa biyar na Musulmin yankin ba, suna mulkar su. Amma ba wata rana da Musulmi suka fito domin yin zanga-zangar nuna rashin yarda ba balle su tayar da hankali da kone-kone. An yi zabe lafiya duk duniya ta gani, amma aka wayi gari aka far wa Musulmi ta ko’ina har cikin gidajensu an shiga an harbe su, an jikkata daruruwa maza da mata, ga kadan daga cikin ta’addancin da aika-aikan da aka yi wa Musulmin Jos:
a- An sami yara a makarantu suna karatu an harbe wadansu, a yayin da wasu aka kone su kurmus, Makarantar Sakandaran Al-Bayan ta isa misali wadda har CNN da Aljazeera sun dauka. An kona makarantu sakandare na Musulmi guda 25. An kone motocin sayarwa da na hawa ba iyaka, an kone kasuwar Katako da ta ’Yan Hatsi da sauransu. Shin an kama wani?
A bana, a ranar 17/01/2010 wani Musulmi da aka kona wa gida a Dutse Uku bayan ya sami damar gyarawa aka ce ba zai gyara ba, daga nan sai aka far wa Musulmi da kisa, ba wani bincike kwatsam! Sai Kwamishinan ’Yan sanda da Gwamnatin Filato ta saya ya fito a talabijin da rediyo ya ce: “Wadansu matasan Musulmi ne suka auka wa Kiristoci a coci.” Shi kuma shugaban gidan rediyo da talabijn na jihar ya sa aka rika maimaita jawabin a kowane minti goma, ya tunzura mutanen jihar musamman ’yan kabilar Birom da suke da mummunar gaba ga Musulmin jihar suka auka wa kauyukan da ke kusa da su kamar, bukuru da Angulu-Jos da Anguldi da dorawar bukuru da Unguwar Doki da Gel da Sabon Gidan Kanar da Rafin bauna da Kwal da Zagun da Bincin da Kuru karama da Kuru Babba da Bisici da Kaduna bom da Sabon Gidan danyaya da Farom Mishan da Farom da Timtin da dorawar Gindin Dutse da dorawar Babuje da Dogo na Hauwa da Pankshin da Sura. A takaice garuruwa 41 aka kai wa farmaki, kuma kauyuka 25 yanzu ba kowa a cikinsu, an karkashe na kashewa, an sassari wadansu, wadansu sun tsallake rijiya da baya!
Abin mamaki da takaici da ban haushi duk ta’addancin da ake yi wa Musulmi shekara da shekaru ba wata kasa ko jama’a da ta fito fili ta la’anci wadanda suka aikata wadannan aika-aika ko ta yi kira a zakulo’yan ta’adda domin a hukunta su.
Kuma an karkashe Fulanin da suke daji, ba su san hawa ba ko sauka, su ba ’yan siyasa ba, sun fito sun yi bayani dalla-dalla da yawan Fulanin da aka kashe da wuraren da aka kashe su da wadanda ake zargin sun kashe su, amma ba wanda ya yi magana!
Ranar 7/03/2010 wadansu da ba a san ko su wane ne ba, sun shiga Dogo na Hauwa suka bubbuge mutanen Berom, sai ga manyan kasashen duniya sun fito ba kunya ba tsoron Allah suna cewa dole ne gwamnati ta binciko tare da hukunta wadanda suka yi kisan. Misali:
1- Ofishin Jakadancin Amurka da Sakatariyar Harkokin Wajenta Misis Clinton sun yi kira a sarari cewa dole Gwamnatin Najeriya ta kamo mutanen da suka kashe Kiristoci ta hukunta su.
2- Ingila ta yi kira tare da nuna mummunan bakin ciki.
3- Kanada ta nuna damuwa tare da neman sai an kamo masu laifin.
4- Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya nuna takaici da abin da yake faruwa a Najeriya kuma ya ce dole a yi bincike.
5- Sakataren O.I.C, ya yi kaico da nuna alhininsa ga wadanda abin ya faru da su.
6- Majalisar Dokoki kuwa cewa ta yi: “Yanzu ne za a yi bincike na hakika!” Wannan shi ne Adalci!
Amma Musulmi ko an kashe su, ba komai ai suna da yawa, domin haka ba wanda zai yi magana daga manyan kasashen duniya da na Musulmi. Allah wadaran naka ya lalace.
Abu na biyu: Bayani kan tsaro: Harkar tsaro a zamanance ta dogara ne ga bangarori daban-daban na jami’an tsaro, amma idan wata fitina ta faru aka kasa shawo kanta ba a Najeriya ba a duk duniya an yarda sojoji ne za su kwantar da ita, sai ga shi a Jihar Filato abin ba haka yake ba.
Gwamnatin jihar ta kekasa kasa ta ki yarda da su, domin ba za ta sami abin da take so ba, a kullum kira take a cire sojoji a maye gurbinsu da ’yan sanda. Mu Musulmi muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara yawan sojoji a Jos da kewaye, domin soja yana da adalci, ba ya nuna bambanci tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba, soja Musulmi yana tsare Kirista da dukiyarsa kamar yadda soja Kirista ke tsare Musulmi da dukiyarsa.
Ya ku bayin Allah! Ku ba sojojin da suka bar iyalansu domin kare rayukanku da dukiyarku goyon baya, kamar yadda muke yaba wa sabon Kwamishinan ’yan sanda domin gudunmwar da yake bayarwa ga zaman lafiya da rashin goyon bayan wata al’umma ko addini wanda hakan ya taimaka wajen tabbatar da farfadowar mutuncin ’yan sanda.
Abu na uku: Bayani kan wadanda masifa ta shafa: Dangane da abin da ke faruwa na masifa ta faru ne domin mun bar Allah kuma mun kama sharholiya da san duniya da cin amana da karyace-karyace, sai mutane suka kasu uku:
a) Wadanda masifa ta shafe su, wadansu sun mayar da lamarinsu ga Allah su hakura da abin da suka samu, wadansu kuwa sun mayar da abin hanyar neman kudi da kai karar Allah wurin mutane, kai har ma mun yi karo da ’yan damfara wani ya yi karya ya yi kusa ya cuce mu Naira dubu 270 a kan wai an harbe shi amma Allah Ya tona asirinsa. Akwai misalai da yawa da muke da su.
b) Sai wadanda suke raba kayan taimako, su ji tsoron Allah su kai kayan ga wadanda abin ya shafa, duk mutumin da ya ci kayan ba da hakki ba, sai ya biya ranar Lahira.
c) Sai masu zage-zage domin an hana su kayan saboda ana ganin ba abin da ya shafe su, ko kuma abin ya shafe su amma suna da hadama, duk wadannan abin kyama ne.
Daga karshe ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah, ku so juna ku hada kai, ku tuba ga Allah Madaukaki, ku hana masu sayar da ruwa da ’yan acaba da masu sayen kwai shiga unguwannin kafirai, saboda kullum sai mun sami rahoton an kashe wani daga cikinsu.
Muna rokon Allah Ya gafarta wa Musulmin da aka kashe, Ya ba wadanda suka sami rauni lafiya Ya mayar wa wadanda aka kone dukiyarsu da dubunta. Allah Ya wulakanta duk mai kawo fitina a jihar nan da Najeriya, su kuwa ’yan kwangilar wargaza Najeriya Allah Ya mayar musu da makircinsu a kansu.
Allah Ya yi dadin tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad da sallamewa.