Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu binsa da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.Bayan haka a watannin baya mun yi rubutu kan gwagwarmayar gano gaskiya na daya daga cikin Sahabban Manzon Allah (SAW) wato Salmanul Farisi (RA), […]

Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (1)
Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu binsa da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka a watannin baya mun yi rubutu kan gwagwarmayar gano gaskiya na daya daga cikin Sahabban Manzon Allah (SAW) wato Salmanul Farisi (RA), inda muka ga yadda ya yi ta tafiye-tafiye daga gari zuwa gari da kasa zuwa kasa har Allah Ya sa ya cimma burinsa na samun shiriya ya rungumi addinin Musulunci.
To a yau za mu dubi irin adalcin da ke cikin wannan addini na Musulunci ne ta hanyar nazarin wasu al’amura da suka faru a zamanin halifancin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (Allah Ya yarda da shi).
Mun dauko misalan da Khurram Murad, Darakta Janar na Gidauniyar Musulunci (The Islamic Foundation) da ke Ingila ya kawo ne a cikin littafinsa mai suna “Daular Adalci: Labarai daga rayuwar Umar- The Kingdom of Justice Stories from the life of Umar).” Littafin da ya yi domin amfanin yara ’yan makaranta, kamar yadda ya fada a gabatarwarsa. Sai dai kamar yadda ya fada manya ma za su iya amfana daga abin da ke cikin littafin, mu ma muna fata ba yara ba har manya na wannan al’umma tamu da take tsakiyar kogin rudu da dimaucewa da hauragiya da rashin alkibla za su amfana tare da koyi da koyarwar da ke cikin wannan littafi.

Koda Fatima ce sai na hukunta ta:
Allahu Akbar! Abu ne sanannne cewa Manzon Rahma Annabi Muhammad (Sallallahu Alai wa Alihi wa Sallam) shi ne jagoran masu adalci a tsakanin sakalaini, (wadanda Allah Ya dora musu nauyin aiki da sakonnin da Annabawa suka zo da su daga wurin Allah – aljanu da mutane). Ke nan shi ne madubi na farko ga masu adalci a bayan kasa. Wannan shi ya sa marubucin ya fara bude littafinsa da kawo kissar wata mace da aka so a yi kamun kafa don kada a hukunta ta a zamanin Annabi (SAW) saboda ita ’yar manya ce.
Ga yadda labarin ya zo:
Akwai wata mace da ke zaune a garin Makka, wadda ta fito daga gidan manya da ake girmamawa, babba ce ’yar manya, ta fito daga zuriyar Makhzum ne da ake girmamawa a garin Makka, amma sai ta yi sata, ganin tana fuskantar yanke mata hannu kamar yadda Allah Ya hukunta, sai aka shiga nemo hanyar kubutar da ita. Wannan mace sunanta Fatima – sunanta daya da na ’yar Manzon Allah (SAW) – Wannan lamari ya faru ne a bayan Fathu Makka (Bude Makka). A lokacin mutane da dama sun karbi Musulunci, amma ba su san Musuluncin sosai ba, ko a ce ba su rungumi sabuwar rayuwar Musulunci ta adalci ba, wadda ta nuna duk Musulmi mai dukiya da matalauci, mai mulki da talaka, wanda ya fito daga gidan mulki da isa da sarauta da wanda ya fito daga gidan gyartai ko dan dako ko mai turin kura ko baban bola, doka tana yin aiki a kansu ne daidai wa daida a lokacin da suka aikata laifi!     
Ba haka duniya ta kasance ba kafin bayyanar Musulunci, dokar ita ce yadda ake hukunta wadanda suka fito daga gidan manya daban ne da yadda ake hukunta ya ku bayi talakawa. Idan dan gidan manya ya aikata laifi, sai a yi maza-maza a rufe saboda kada a kunyata iyayensa ko zuriyarsa a idon jama’a. Don haka da wannan abu ya faru da Fatima bint Makhzum sai aka shiga damuwa a birnin Makka, yaya za a yi a hukunta babba ’yar babba. Yaya za a yi haka ya faru! Shin babu wata hanya da za a kubutar da ita ce? Damuwa ta rika karuwa. Sai dai abin tambaya yaya za a yi a gamsar da Annabi (SAW) ya kubutar da Fatima daga hukuncin yanke mata hannu. Sun san cewa ba za su iya tunkarar Annabi (SAW) su nema mata afuwa daga hukuncin da Allah Ya tanada ba.
Bayan doguwar tattaunawa sai suka yanke shawarar kama kafar Usama bin Zaidu. Zaidu kuma (Allah Ya kara masa yarda) in za a tuna bawa ne na Annabi (SAW) da ya zama dansa ta hanyar ’yantawa, kuma yana daya daga cikin mutum hudu na farko da suka fara Musulunta. Annabi (SAW) yana matukar son Usama dan Zaidu kamar yadda yake son Zaidu mahaifinsa. Da wannan dalili ne Bani Makhzum suke ganin idan Usama ya yi magana da Annabi (SAW) za a yafe wa Fatima bint Makhzum. Usama a lokacin yana matashi. Shi kuma matasshi galibi kan yi komai cikin kuruciya da gaggawa tare da yin abubuwa domin nuna kansa a tsakanin manya. Yana jin dadi a ce wani ba ma zuriyar manya kamar ta Makhzum ba, ya zo neman taimako wurinsa.
Sai suka ce, “Usama, hakika ka san halin da muke ciki. Dubi Fatima barrantacciyar budurwa. Shin zai yi kyau a hukunta ta kamar kowane barawo? Ta yaya za ta yi tunanin wannan dan karamin kuskure zai jawo mata matsala haka? Wadannan sababbin dokoki da suke hukunta mutane daidai, babba da karami baki ne a gare mu. Ba za mu iya bin su cikin gaggawa haka ba! Ta yaya za mu iya canja halayen rayuwarmu a cikin ’yan makonni. Wannan cin zarafin wannan zuriya tamu mai girma da mutunci ne!”
Bayan ya saurari dukkan bayanansu, Usama ya dan karkata ga ra’ayinsu. Da zafi a hukunta ta kamar sauran mutane. Sun fito daga babban gida! Sai ya yi alkawarin zai yi iyakar kokarinsa domin shawo kan Annabi (SAW) ya yi sassauci ga Fatima. Ya ce “Ba komai zan yi magana da Annabi (SAW), kuma zan yi kokarin kubutar da ku da kuma ’yarku daga tozarta!”
Usama (RA) ya bari sai da ya kasance tare da Annabi (SAW) shi kadai; sai ya fara rokonsa. “Ya Manzon Allah! Ko ka ji abin da ya faru da budurwar nan mai sunan ’yarka, Fatima? Ana zarginta da sata kuma tana fuskantar hukunci. Wannan abin tashin hankali ne ga kowace budurwa, balle macen da ta fito daga gidan manyan mutane na kabilar Makhazum! Hakika ya kamata a duba lamarinta. Domin a zuriyarta ba a taba hukunta wani kan wani laifi ba.”
Usama ya ci gaba da cewa, “Wadannan tsarin dokoki sababbi ne ga mutanen Makka, ba su gama sanin dokokin suna aiki a kan babba da talaka ba. Ashe bai fi dacewa a rika gudanar da wadannan haddodi kadan-kadan ba, ana ba mutane dama suna sabawa da su domin a kauce wa tawaye ko rashin jin dadi daga wadancan sababbin Musulunta ba?”
A lokacin da Usama ke wadannan maganganu, Manzon Tsira (SAW) sai ya fuskanto shi cikin sauri, kuma shi kansa ya ga alamar bacin rai daga Annabi (SAW) kan maganganunsa, don haka yana magana yana dada rudewa, yana dada magana yana gane kuskurensa. Don haka lokacin da Annabi (SAW) ya juyo gare shi, ya fuskance shi, har zuciyarsa ta cika da nadama kamar ya nutse a kasa saboda kunya.
A karshe sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Usama ina sonka sosai, amma ka yi tunani kan abin da kake tambayata. Kana neman in bari, ko in ki aiwatar da wani umarni da Allah Ya ba ni ne, saboda kawai wanda ake zargin ya fito ne daga gidan manya!”
Kafin ka ce me, Usama ya rusuna kasa wajen kafafun Manzon Allah (SAW) yana rokonsa ya nema masa gafara a wurin Allah a kan laifinsa.