Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (3)
dan Gwamna mai alfahari: Wata rana Amirul Muminina Umar dan Khaddabi yana zaune a masallaci, sai wani mutumin Masar ya shiga ya yi masa sallama kamar yadda aka saba: ‘Assalamu alaikum’ ya ce: Umar (RA) ya amsa ‘Wa alaikumus salam.’ Sai bakon nan ya nemi wuri ya zauna kusa da Umar (RA) sannan ya ce: […]
dan Gwamna mai alfahari:
Wata rana Amirul Muminina Umar dan Khaddabi yana zaune a masallaci, sai wani mutumin Masar ya shiga ya yi masa sallama kamar yadda aka saba: ‘Assalamu alaikum’ ya ce: Umar (RA) ya amsa ‘Wa alaikumus salam.’ Sai bakon nan ya nemi wuri ya zauna kusa da Umar (RA) sannan ya ce: “Idan na gabatar da kukana gabanka, ina da tabbacin samun adalci da kuma kariya?” Umar (Allah Ya kara masa yarda) ya ce: “kwarai kuwa na yi maka alkawarin samun adalci da kuma ba ka kariya. Amma ka gaya min, me yake damunka?”
Sai mutumin Masar din nan ya ce: Gwamnanka a Masar Amru bin Al-As yana da wata dabi’ a ta shirya gasar tseren dawaki. Kuma ka san yadda muke son dawaki a Masar kamar yadda lamarin yake a kasashen Larabawa, da damanmu muna da dawaki masu kyau. Kowa yana son a ce ya shiga gasar nan, kuma akan dauki kwanaki ana shirye-shirye don wannan gasa ta musamman mai muhimmanci. To ni ma ina da wani doki mai kyau da karfi, kuma ina da kyakkyawar fata in lashe gasar nan.”
Wannan mutumin Masar ya ci gaba da bayyana wa Amirul Muminina Umar dan Khaddabi abin da ya gudana kamar haka: “Muhammad (dan Gwamnan Masar) Amru ya shiga gasar tseren dawakin. To da aka fara gasar duk lokacin da dawakan suka kewayo ta gabanmu sai mu rika lekawa mu ga wanda ke gaba. Sai na hango dokina wanda aka bari a baya a farkon gasar yana kara gudu yana kamo sauran yana kokarin wuce su musamman da aka shiga zagaye na biyu. Lokacin da aka shiga zagaye na uku lokacin da dawaki suka kusato inda Muhammad yake zaune sai na ji yana fadi da babbar murya “Dokina ne a kan gaba! Dokina ne zai lashe gasar!”
Bamisire ya ci gaba da cewa: “Jimawa kadan suka iso wurina sai na ga ba dokin Muhammad ne a gaba ba, dokina ne ke kokarin lashe gasar. Kada ka ji irin murnar da na ji. Na daka tsalle na fara murna ina zuga dokina ya kara gudu na ce: Na rantse da Ubangijin Ka’aba wannan dokina ne a kan gaba. Kwatsam sai Muhammad ba tare da wata sanarwa bay a iso gare ne da bulala ya rika zane ni iyakar karfinsa yana cewa: “Karbi wannan dan talakawa karbi wannan. Kada ka manta ni dan babban mutum ne kai kuwa ba komai ba ne wofin banza.”
Ya kara da cewa “Abin mamaki ko ka san abin da ya faru da ni a bayan haka ya Amirul Muminina? Sai aka jefa ni kurkuku… kuma ba don komai ba, sai domin Amru ya samu labarin abin da ya faru, don haka nake jin tsoro na zo gare ka domin neman kariya da mika kukana kan wannan aika-aika na dansa. A can an jefa ni a kurkuku ba domin taimakon wani daga cikin masu tsaron kurkukun ba da ya ji abin da ya faru ba zan iya zuwa nan na nemi taimakonka ba.”
Da Umar (RA) ya ji wannan labara sai ya yi kasake kamar ruwa ya ci shi. Can sai ya ce: “Zauna dan uwana. Ka zauna tare da mu.” Sannan Umar (RA) ya rubuta takarda zuwa ga Gwamnan Masar yana umartarsa ya zo Madina maza-maza tare da dansa Muhammad. Shi kuma mutumin Masar din aka ce ya zauna har sai sun zo.
Lokacin da Amru ya karbi wannan wasika sai ya damu. Ya kira dansa ya tambaye shi me ya aikata. “Ko ka yi wani laifi ne?” Ya tambaye shi. “A’a na rantse ban yi komai ba,” inji saurayin.
“In haka ne me zai sa Umar (RA) ya neme mu ni da kai? Babu shakka akwai abin da ka aikata,” inji Amru yana nuna dansa da yatsa yana ja masa kunne.
Sai Amru da dansa Muhammad suka kama hanyar Madina, bayan doguwar tafiya suka isa Masallacin Annabi (SAW) a Madina. Jama’a ta taru lokacin da aka ji labarin Amru yana kan hanya, kuma mutane da dama suka rika jinjina ga babban janar a lokacin da yake wucewa ta wurinsu, shi kuma yana amsa gaisuwarsu. Yana sanye da tufafinsa masu tsada kamar yadda ya saba, kuma dansa mai alfaharin nan yana biye da shi.
Yana zuwa ba tare da bata lokaci ba Umar (RA) ya ce “Ina danka?” Nan da nan Muhammad ya leko ta bayan mahaifinsa Amru. Sai ya ce: “Ina mutumin Masar din nan?” Ya ce: “Ga ni ya Amirul Muminina!”
Sai Umar ya mika masa bulala ya ce: Doki wannan saurayi dan babban mutum kamar yadda ya doke ka.”
Sai mutumin Masar ya dauki bulala ya rika tsala masa, Umar yana kada kai alamar jin dadi, yana cewa, “Ya yi kyau… doki dan babban mutum.”
Bayan wanin lokaci Bamisire ya tsaya da kansa.
Sannan Umar ya waiwaya wajen Amru ya ce: “Yaushe kuka mayar da mutane bayi, bayan Allah Ya halicce su ’ya’ya?” Ya yi masa gargadi mai tsanani, sannan ya sallame su.
Daga wadannan labarai biyu da suka gabata, za mu fahimci wani babban al’amari da ya bambanta Musulunci da sauran addinai da tsare-tsare na dan Adam wajen tabbatar da adalci da kuma barin kofar shugabannin a bude ga talakawa domin su isa gare su, su isar da kuka ko korafi game da shugabannin na kasa da su.
Misali a labarin farko, jingina kalmar munafunci Gwamna Amru ya yi ga talakansa, kuma wannan talakan ya ga an yi masa iyakar cin mutunci, sannan saboda tabbacin zai samu adalci ya garzaya har Madina daga Masar ya kai kuka kuma aka yi wa Gwamnan hukunci kamar yadda Musulunci ya tanada na ya yi wa Gwamnan nan bulala 40 da kansa na yi masa kazafi da bata suna. Kuma cin kaskanci Gwamnan nan ya rusuna a gaban wannan talaka ga dubban jama’a suna kallo ya cire rawaninsa ya mika wa wannan talaka bulala ya ce ya zartar da wannan hukunci! Shin wane addini ko tsari ne yake da irin wannan koyarwa? Sannan a labari na biyu dan wannan Gwamna ne ya yi bulala ga wani dan talakawa da dokinsa ya tsere na dan Gwamna a lokacin gasar sukuwar dawaki, nan ma wannan talaka ya garzaya har Madina don neman adalci, kuma a karshe ya samu adalcin. Musamman Amirul Muminina Umar dan Khaddabi (RA) ya kira Gwamnan da dansa har Madina sannan ya hukunta dan a gaban mahaifinsa kuma ya ja masa kunne.
Mu tsaya mu tambayi kawunanmu a matsayinmu na Musulmi da muke son shiga Aljanna tare da wadancan magabata, shugabanninmu na yanzu suna yin irin wannan adalci a tsakanin mabiyansu? Shin daga kansila zuwa Shugaban kasa daga mai unguwa zuwa sarki daga lebura zuwa heluma daga masinja zuwa kan shugaban ma’aikata, wane ne cikinsu zai fadi wata mummunar magana ga na kasa da shi a ce an iya zuwa gaba an samu adalcin da na kasa zai ji cewa shi mutum ne? Shin kofofin shugabanninmu na yanzu a bude suke ga na kasa ya isar da kukansa? Shin idan dan ‘babban mutum’ ya aikata laifi hukunta shi ake yi ko kokarin kubutar da shi? Me muka lura da shi a labarin farko na fiyayyen halitta (SAW) cewa da Fatima za ta yi sata zai sa a yanke mata hannu!